Wednesday, February 25
Shadow
Shugaban kasa, Tinubu ya gana da sarkin Musulmi

Shugaban kasa, Tinubu ya gana da sarkin Musulmi

Duk Labarai
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya gana da Sarkin Musulmi Sa'ad Abubaka III a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja yayin da barazanar Trump ta kai hari ƙasar ke ci gaba da jan hankali. Ganawar tasu na zuwa ne bayan Tinubu ya gana da Archbishop na Abuja Ignatius Kaigama. Fadar shugaban ba ta bayyana abin da suka tattauna ba, amma ana sa ran ba za ta wuce yunƙurin kwantar da hankali ba yayin da wasu ke yaɗa iƙirarin yi wa mabiya addinin Kirista kisan ƙare-dangi. Daga baya sarkin ya bi sawun shugaban ƙasar wajen yin sallar Juma'a a fadar shugaban ƙasa
Dole Trump ya fito ya janye kalamansa sannan ya baiwa Najeriya hakuri>>Inji Sanata Barau

Dole Trump ya fito ya janye kalamansa sannan ya baiwa Najeriya hakuri>>Inji Sanata Barau

Duk Labarai
Sanata Barau Jibrin ya bayyana cewa, dolene Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya janye kalaman barazanar da yawa Najeriya sannan ya bayar da hakuri. Ya bayyana hakane a wajan wani taron ganawa da matasa da yayi ranar Alhamis. Sanata Barau yace Najeriya kasa ce me cin gashin kanta dan haka ba zata bari wata kasa ta zo tana mata barazana ko katsalandan ba. Yace ko da abinda Trump yake fada gaskiyane ba sigar da ya kamata ya biyo ba kenan, kamata yayi majalisar Dinkin Duniya ce zata shiga tsakani saboda akwai dokar kasa da kasa. yace mu ba dabbobi bane akwai dokokin da suka tanadi hanyoyin da ake bi dan daukar mataki akan matsaloli irin wannan ba wai barazana ba.
Kalli Bidiyon: Najeriya ce kadai kasar Duniya da aka ce za’a kawowa Khari amma aka mayar da Abin Comedy>>Inji Malam Aminu Ibrahim Daurawa

Kalli Bidiyon: Najeriya ce kadai kasar Duniya da aka ce za’a kawowa Khari amma aka mayar da Abin Comedy>>Inji Malam Aminu Ibrahim Daurawa

Duk Labarai
Babban malamin Addinin Islama, Malam Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana cewa, Najeriya ce kadai kasar Duniyar da aka ce za'a kawowa Khari amma ta mayar da abin Comedy. Malam na maganane akan harin da kasar Amurka ta yi barazanar kawowa Najeriya. https://www.tiktok.com/@daurawabackup/video/7569761079522233607?_t=ZS-91CGEy8D0SX&_r=1
Ko Gezau: Barzanar Trump bata tsorata mu ba>>Inji Fadar Shugaban kasa

Ko Gezau: Barzanar Trump bata tsorata mu ba>>Inji Fadar Shugaban kasa

Duk Labarai
Fadar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta bayyana cewa, bata kadu da barazanar kawo Khari ta kasar Amurka zuwa Najeriya ba. Ministan yada labarai, Mohammed Idris ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai bayan zaman majalisar zartaswa. Yace shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu bai kadu ba, hakanan Ministocinsa basu kadu ba da barazanar kasar Amirka ta kawo hari ba. Yace saidai tuni suka nema suka fara tattaunawa da wakilan kasar Amurka, yace suna bin hanyar Diplomaciyya dan warware matsalar.
Trump bai isa ya Hana Aiki da shari’ar Musulunci a Jihohin Arewa ba>>Inji Kungiyar Dattawan Arewa

Trump bai isa ya Hana Aiki da shari’ar Musulunci a Jihohin Arewa ba>>Inji Kungiyar Dattawan Arewa

Duk Labarai
Kungiyar Dattawan Arewa, NEF ta mayarwa da shugaban kasar Amirka, Donald Trump da martani me zafi inda tace shugaban Amurkar, Trump bai isa ya hana aiki da Shari'ar Musulunci a Jihohin arewa ba Wasu daga cikin 'yan majalisar kasar Amurka da wasu kungiyoyin fafutuka a kasar sun nuna damuwa kan amfani da shari'ar Musulunci a jihohin Arewa. Dan haka suke kiran a daina amfani da shari'ar Musulunci a Arewa sannan a sakawa wasu jami'an gwamnatin Najeriya takunkumi. Saidai kungiyar NEF ta bakin me magana da yawunta, Prof Abubakar Jiddere tace babu wannan maganar, Trump girman kai ne ke Damunsa kuma barzanar da yake yi ta banza da wofi ce babu abinda zai iya. Sannan kungiyar tace babu maganar yiwa Kiristoci Khisan Kyiyashi a Arewa matsalar tsaro tana shafar kowa da kowane. Hakanan ...
Masu Zanga-zanga sun fito a Legas suna nuna kin amincewa da Zuwan Amurka Najeriya

Masu Zanga-zanga sun fito a Legas suna nuna kin amincewa da Zuwan Amurka Najeriya

Duk Labarai
Wasu mutane sun fito zanga-zanga a Legas inda suke nuna kin amincewa da zuwan Amurka Najeriya da sunan wai zasu tseratar da kiristoci. Bidiyon masu zanga-zangar ya karade kafafen sada zumunta inda aka jisu suna fadar cewa ku kyalemu. Wasu dai sun nuna goyon baya a garesu inda wasu suka nuna basa tare dasu. https://twitter.com/ChuksEricE/status/1986493813611766028?t=OEOR9EsXIATvAkohXeYrgA&s=19
An rushe sabon Ofishin yakin neman zaben shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da aka gina a jihar Benue

An rushe sabon Ofishin yakin neman zaben shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da aka gina a jihar Benue

Duk Labarai
Rahotanni daga jihar Benue na cewa, an rushe sabon ofishin yakin neman zaben shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da aka gina a jihar. Ranar Alhamis ne Hukumar kula da raya birane ta jihar Benue din ta rushe wannan gini wanda kuma shine Hedikwatar yakin neman zaben Tinubu a jihar. Sati daya kenan da bude wannan ofishin. Shugaban kungiyar magoya bayan Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a jihar Tarnongo Simon yayi Allah wadai da lamarin inda yace sun cika duka sharudan mallaka da ginin wannan ofishi nasu kamin a rusheshi.
Kalli Bidiyo: Wasu ‘yan arewa musulmai sun fito suma suna Bayyana irin Asarar rhayukan da akawa Musulmai

Kalli Bidiyo: Wasu ‘yan arewa musulmai sun fito suma suna Bayyana irin Asarar rhayukan da akawa Musulmai

Duk Labarai
Bayan da Kiristoci suka kai kara kasar Amurka kan asarar rayukan da aka musu, Wanda hakan yasa shugaban kasar Amurka, Donald Trump bayyana cewa zai dauki mataki akan Najeriya. Suma wasu musulmai daga Arewacin Najeriya sun fito suna bayyana irin Asarar rayukan da rikice-rikice sukawa musulmai. Bidiyon su ya watsu sosai inda mutane suka rika bayyana mabanbanta ra'ayoyi akai. https://www.tiktok.com/@daawah2nonemuslim/video/7569726697172454664?_t=ZS-91C2Gz0XSoT&_r=1
A karin Farko, Wakar Hausa ta watsu sosai a Duniya har Turawa suna Rerata

A karin Farko, Wakar Hausa ta watsu sosai a Duniya har Turawa suna Rerata

Duk Labarai
Wakar da matashin Arewa Og Abba yayi ta samu kudinka kawai ka kashe ta dauki ha kula sosai a wajan 'yan kudu da Turawa da sauran sassan Duniya. Itace ta zama wakar Hausa ta farko data watsu sosai har wadanda ba Hausawa ba suka rera ta suka yi Bidiyo da ita. Manyan Mawaka da shahararrun mutanene daga Kudu daga wasu sassa na duniya suka hau wakar. https://www.tiktok.com/@ogabbah/video/7568090188195368203?_t=ZS-91BX7tusmXJ&_r=1 https://www.tiktok.com/@angelbby053/video/7568938918427626770?_t=ZS-91BXRlrQSeG&_r=1 https://www.tiktok.com/@lanoanddana/video/7569330718673833246?_t=ZS-91BXVJ7zS0u&_r=1 https://www.tiktok.com/@dj_splash_gh/video/7567642866583883064?_t=ZS-91BXajTXUvY&_r=1 https://www.tiktok.com/@viollababy.xx/video/7565925080795008264?_t=ZS...
Kalli Bidiyo: Matashiya ‘yar Jihar Bauchi me shekaru 19 ta na neman mijin aure me Hankali, Mahaifinta me kudi ne amma tace ita matashi indai yana da sana’a da nutsuwa zasu daidaita

Kalli Bidiyo: Matashiya ‘yar Jihar Bauchi me shekaru 19 ta na neman mijin aure me Hankali, Mahaifinta me kudi ne amma tace ita matashi indai yana da sana’a da nutsuwa zasu daidaita

Duk Labarai
Malam Abdulrahman Umar Sautussunnah ya bayyana cewa wata matashiya 'yar kimanin shekaru 19 daga jihar Bauchi ta na neman mijin aure me hankali da sana'a. Malam yace mahaifin matashiyar me kudi ne amma ita tace tana neman matashin dake da sana'ar da zai iya rike ta amma dai bata masa alkawarin komai ba. https://www.tiktok.com/@abdurrahmanumarr/video/7569348426798746900?_t=ZS-91BVZe3QhFY&_r=1