Namijin Goro: Namijin goro karfin maza
Namijin Goro sanannen abune da ake amfani dashi a duka fadin Duniya. Akan yi amfani dashi wajan warkar da cutar Mura ko cutar Koda.
Namijin goro in English
Sunan namijin goro da turanci shine Bitter Kola, ana kuma ce masa Bitter Cola, ko kuma Garcinia Kola.
Ana samun Namijin goro a kasashen Afrika kamar su Gambia, Democratic Republic of the Congo, Ivory Coast, Mali, Gabon, Ghana, Liberia, Nigeria, Senegal da Sierra Leone.
Kuma masana sun yi bayani sosai akan amfanin da yakewa jikin dan Adam kamar yanda zamu gani a kasa.
Amfanin namijin goro
Namijin goro na taimakawa masu son rage kiba
Yana taimakawa sarrafa abinci.
Yana taimakawa garkuwar jiki.
Yana saukar da hawan jini.
Yana maganin bacin rai da damuwa.
Yana maganin guba.
Yana maganin ciwon ido.
Yan...