
Me ya sa gwamnatin Malaysia za ta hana amfani da motocin CNG?
Matakin da gwamnatin ƙasar Malaysia ta ɗauka cewa daga ranar 1 ga watan Yulin 2025 za ta daina amfani da motoci masu amfani da makamashin iskar gas na CNG ya haifar da fargaba a Najeriya.
A farkon makon nan ne ministan sufurin ƙasar, Loke Fook, ya bayyana haka a wani taron manema labarai a ƙasar.
Ya ce babban kamfanin mai na ƙasar zai hana sayar da makamashin na NGV (da ya ƙunshi CNG da LPG) a gidajen man da ake sayar da shi a faɗin Malaysia.
Mista Look ya ce an ɗauki matakin ne domin kare rayukan masu ababen hawa da sauran al'ummar ƙasar.
“Tankunan waɗannan motoci masu amfani da makamashin NGV a yanzu sun kai adadin shekarun da ya kamata a ce sun daina aiki, don haka dole mu sake su, saboda sun kai shekara 15 da aka saka wa motocin''.
An ɓullo da amfani da makamashin NGV a ...