Saturday, February 28
Shadow
Gwamnatin Jihar Kano zata sake aurar da Zawarawa akan Naira Biliyan 1

Gwamnatin Jihar Kano zata sake aurar da Zawarawa akan Naira Biliyan 1

Duk Labarai
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya amince da kashe Naira Biliyan 1 da Miliyan 6, domin auren zawarawa karo na biyu. Kwamishin yaɗa labarai da harkokin cikin gida Kwamarad Ibrahim Abdullahi Waiya ya bayyana haka lokacin da yake ganawa da manema labarai kan sakamakon zaman majalisar zartaswar jihar Karo na 32 da ka gudanar ranar juma'ar da ta gabata. Me zaku ce?
Muna nan akan Bakanmu, kowa sai ya biya Haraji, ko ta hanyar halarar ya samu kuri ko bata ta hanyar halal ba, Qaruwai, Kwandastan Mota, dama kowace irin sana’a kake nan da 2026 sai ka fara biyan Haraji>>Inji Gwamnatin Tinubu

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, tana nan akan bakanta na cewa, kowa sai ya biya haraji. Shugaban kwamitin Gyaran fasalin kudi na shugaban kasa, Taiwo Oyedele ne ya bayyana haka a wata ganawa da manema labarai. Yace a Duniya gaba daya haka tsarin yake, ko ta wace hanya ka samu kudi sai ka biya Haraji, yace idan ance wanda suka samu kudi ta hanyar Halal ne kadai zasu biya haraji, to sai wasu su koma samun kudi ta hanyar Haram dan su kaucewa biyan Harajin. Yace hukumar karbar Haraji ta kasar Amurka nada taken cewa ko sata kayi sai ka biya Haraji.
Tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan na shirin komawa jam’iyyar ADC

Tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan na shirin komawa jam’iyyar ADC

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan na shirin komawa jam'iyyar ADC. Wasu majiyoyi ne suka fadawa kafar Punchng hakan a asirce daga jam'iyyar ADC din saboda basu da ikon yin magana da yawun jam'iyyar. An jima dai ana rade-radin cewa, tsohon shugaban kasar zai tsaya takarar shugaban kasa a 2027 amma shi bai fito ya tabbatar da hakan a hukumance ba.
Allah ya kawo mu zamanin Wawaye da Jahilai kowa sai fadin abinda yaga dama akan Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) yake>>Inji Sheikh Umar Sani Fage

Allah ya kawo mu zamanin Wawaye da Jahilai kowa sai fadin abinda yaga dama akan Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) yake>>Inji Sheikh Umar Sani Fage

Duk Labarai
Malamin Addinin Islama, Sheikh Umar Sani Fagge ya yi raddi sosai akan masu yin kalamai da basu dace ba akan Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam). Malam yace idan aka samu mutum da laifi zai iya kaiwa a dauki hukuncin khisa akansa. https://www.tiktok.com/@mai.6013/video/7557485955301625095?_t=ZS-90I9Vj3gtdp&_r=1
Maganar Gaskiya, Malam Lawal Triumph duk da namune, sai mun fadi gaskiya, Yayi Kuskure kalaman da yayi kan Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) kuma ya kamata a hukuntashi>>Sheikh Yusuf Sambo Rigachukun

Malamin Addinin Islama Sheikh Yusuf Sambo Rigachukun ya bayyana cewa duk da Malam Lawal Triumph yana bangarensu ne amma maganar gaskiya yayi kuskure. Malam ya bayyana cewa maganar Sheikh Lawal Triumph bata dace da Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ba amma kuma bata fitar dashi daga Musulunci ba. Ya kawo misalin irin hakan data faru a baya inda yace ladabtarwa ce ake wa irin wannan suka yi hakan. https://www.tiktok.com/@mai.6013/video/7557115827904990482?_t=ZS-90I63lDof5M&_r=1