Sunday, December 21
Shadow
EFCC ta tsare tsohon ministan ƙwadago, Chris Ngige

EFCC ta tsare tsohon ministan ƙwadago, Chris Ngige

Duk Labarai
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC, ta tsare tsohon ministan ƙwadago kuma tsohon gwamnan jihar Anambra, Chris Ngige. Mai magana da yawun Ngige, Fred Chukwuelobe, ya tabbatar da tsare shi da safiyar ranar Alhamis, bayan wasu rahotanni da aka yaɗa cewa an sace shi. Chukwuelobe ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa, “Ngige yana tare da EFCC. Ba a sace shi ba.” Har zuwa yanzu, EFCC ba ta bayyana dalilin tsare Ngige ba amma kuma ana sa ran hukumar za ta fitar da cikakken sanarwa kan tsare shi da binciken da take yi a kansa. Ngige ya zama mutum na biyu daga cikin tsoffin ministocin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da aka tsare a kwanan nan. Kafin shi, an fara tsare tsohon ministan shari’a, Abubakar Malami, wanda shima yake hannun EFCC.
Ba zamu yafe abinda aka mana a Zaria ba>>Inji Sheikh Ibrahim Zakzaky

Ba zamu yafe abinda aka mana a Zaria ba>>Inji Sheikh Ibrahim Zakzaky

Duk Labarai
Shekara goma kenan tun bayan kisan da jami’an sojin Najeriya suka yi wa mabiya mazhabar Shi’a a garin Zaria na jihar Kaduna. A wancan lokaci an yi amanna ɗaruruwan mutane ne suka mutu, da dama kuma suka jikkata, bayan zargin rundunar soji cewa mabiya Sheikh Ibrahim Zakzaky sun tare musu hanya. Lamarin ya haddasa suka daga kungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam na duniya, waɗanda suka zargi sojoji da amfani da ƙarfi fiye da kima. Shugaban dandalin tattauna al’amura naƙkungiyar mabiya Shi’a ta IMN a Najeriya, Farfesa Abdullahi Danladi, ya ce duk da wucewar shekaru goma tun bayan faruwar wannan mummunan lamari, har yanzu ba za su taɓa yafe wa waɗanda suka aikata wannan mummunan aikin ba. A tattaunawarsa da BBC, Farfesan ya ce raɗadin abin da ya faru na ci gaba da sosa zuƙatan al’ummar Sh...
Venezuela ta zargi Amurka da sata da kuma fashin teku

Venezuela ta zargi Amurka da sata da kuma fashin teku

Duk Labarai
Venezuela ta zargi Amurka da sata karara da kuma fashin teku bayan da dakarun Amurkan suka kwace wani jirgin ruwa na dakon mai a gabar tekun Venezuela din. Ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ta ce matakin wani shiri ne na lalata arzikin makamashi na Venezuela da gangan. Sai dai jami'an Amurka sun ce jirgin ruwan yana safarar man da aka sanya takunkumin sayar da shi ne zuwa Iran kuma kudin da ake samu daga cinkin ana taimaka wa kungiyoyin ta'addanci ne. https://twitter.com/AGPamBondi/status/1998875795151024337?t=ucDi6xifDOsVYsbJydJHJQ&s=19 Lamarin ya kasance ƙarin wata sabuwar dambarwa ta matsin lambar da Amurka ke yi wa shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro - mai ra'ayin gurguzu. Mai dai shi ne babbar hanyar samun kudade na kasar ta Venezuela
Har yanzu fa Jirgin saman C-130 da sojojin mu 11 na hannun kasar Burkina Faso bata sakosu ba>>Inji Gwamnatin Tarayya

Har yanzu fa Jirgin saman C-130 da sojojin mu 11 na hannun kasar Burkina Faso bata sakosu ba>>Inji Gwamnatin Tarayya

Duk Labarai
Gwamnatin Tarayya ta hayyana cewa, har yanzu kasar Burkina Faso bata sako sojoji 11 da jirgin samansu da suka kama ba. Ministan Harkokin kasashen waje, Yusuf Tuggar ne ya bayyana hakan a wajan taron Kungiyar ECOWAS. A baya dai wasu Rahotanni sun ce an sakosu amma kuma yanzu Gwamnati ta musanta wadancan rahotannin. Tuggar yace suna tattaunawa kan yanda za'a shawo kan lamatin ta hanyar lalama.
Da Duminsa: Mataimakin Gwamnan jihar Bayelsa, Lawrence Ewhrudjakpo ya yanke jiki ya fàdì a ofishinsa ya kuma rigamu gidan gaskiya

Da Duminsa: Mataimakin Gwamnan jihar Bayelsa, Lawrence Ewhrudjakpo ya yanke jiki ya fàdì a ofishinsa ya kuma rigamu gidan gaskiya

Duk Labarai
Rahotanni daga jihar Bayelsa na cewa, Mataimakin Gwamnan jihar, Lawrence Ewhrudjakpo ya yanke jiki ya fadi a ofishinsa. An garzaya dashi FMC dake Yenagoa inda likitoci suka tabbatar da cewa ya rigamu gidan gaskiya. Ya fadi ne da misalin karfe 1:30 na rana inda na kusa dashi suka ce hakan na da alaka da yawan aikin da yake yi.
Shugaba Tinubu ya aikawa shugaban Benin Republic da Sojoji

Shugaba Tinubu ya aikawa shugaban Benin Republic da Sojoji

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya aikawa shugaban kasar Benin Republic, Patrice Talon da wakilan sojoji. Hakan na zuwane bayan da Najeriya ta taimakawa kasar ta Benin Republic wajan dakile yunkurin juyin mulkin. Kuma wannan ziyara na matsayin nuna goyon baya ga shugaba Patrice Talon daga Najeriya. https://twitter.com/DejiAdesogan/status/1999046656650813611?t=FH0Md1K45joV7JNzynQgnA&s=19
Sabbin Bidiyo shagulgulan Bikin Auren Rahama Sadau sun bayyana

Sabbin Bidiyo shagulgulan Bikin Auren Rahama Sadau sun bayyana

Duk Labarai
Sabbin Bidiyon shagulgulan Bikin Auren Rahama Sadau sun bayyana a kafafen sada zumunta inda aka ganta tare da 'yan Uwanta suna shagali. Bidiyoyin sun dauki hankulan mutane inda kuma suka daurewa mutane kai inda wasu suka rika tambayar shin wai sai yanzu za'ayi bikinne? Dalili kuwa shine a jikin Rahamar an ga an rubuta ta kusa zama Amarya. Saidai wasu na tunanin tsaffin Bidiyon ne aka saki. https://www.tiktok.com/@sajeedourhs_couture/video/7582323782690360584?_t=ZS-928ZifmCogD&_r=1 https://www.tiktok.com/@sajeedourhs_couture/video/7582370193716841735?_t=ZS-928Zfd8ayWW&_r=1 https://www.tiktok.com/@sajeedourhs_couture/video/7582367552261704968?_t=ZS-928ZbhK1No1&_r=1 https://www.tiktok.com/@just_rukayyah/video/7582291905862569234?_t=ZS-928Ys7RcOtl&_r...