Sunday, December 21
Shadow
Shugaba Tinubu ya aikawa shugaban Benin Republic da Sojoji

Shugaba Tinubu ya aikawa shugaban Benin Republic da Sojoji

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya aikawa shugaban kasar Benin Republic, Patrice Talon da wakilan sojoji. Hakan na zuwane bayan da Najeriya ta taimakawa kasar ta Benin Republic wajan dakile yunkurin juyin mulkin. Kuma wannan ziyara na matsayin nuna goyon baya ga shugaba Patrice Talon daga Najeriya. https://twitter.com/DejiAdesogan/status/1999046656650813611?t=FH0Md1K45joV7JNzynQgnA&s=19
Sabbin Bidiyo shagulgulan Bikin Auren Rahama Sadau sun bayyana

Sabbin Bidiyo shagulgulan Bikin Auren Rahama Sadau sun bayyana

Duk Labarai
Sabbin Bidiyon shagulgulan Bikin Auren Rahama Sadau sun bayyana a kafafen sada zumunta inda aka ganta tare da 'yan Uwanta suna shagali. Bidiyoyin sun dauki hankulan mutane inda kuma suka daurewa mutane kai inda wasu suka rika tambayar shin wai sai yanzu za'ayi bikinne? Dalili kuwa shine a jikin Rahamar an ga an rubuta ta kusa zama Amarya. Saidai wasu na tunanin tsaffin Bidiyon ne aka saki. https://www.tiktok.com/@sajeedourhs_couture/video/7582323782690360584?_t=ZS-928ZifmCogD&_r=1 https://www.tiktok.com/@sajeedourhs_couture/video/7582370193716841735?_t=ZS-928Zfd8ayWW&_r=1 https://www.tiktok.com/@sajeedourhs_couture/video/7582367552261704968?_t=ZS-928ZbhK1No1&_r=1 https://www.tiktok.com/@just_rukayyah/video/7582291905862569234?_t=ZS-928Ys7RcOtl&_r...
Kalli Bidiyon: Kalli Yanda cacar bakin Adam A. Zango da Tijjani Asase ta kasance

Kalli Bidiyon: Kalli Yanda cacar bakin Adam A. Zango da Tijjani Asase ta kasance

Duk Labarai
Adam A. Zango ya mayar da martani ga Abokin aikinsa, Tijjani Asase bayan da Tijjanin ya zargi Adamu da korar yaransa da kuma kin zuwa ya masa gaisuwar rasuwar mahaifansa. Adamu yace lallai da gaske ya kori yaransa saboda a wancan lokacin za'a fito a zageshi amma yaranshi babu wanda zai fito ya kareshi. Ya bayyana cewa game da rashin yiwa Tijjani Asase gaisuwar mahaifansa kuwa ya kirashi a waya kuma ya saka ta'aziyya a shafinsa na sada zumunta. Yace dalilin kasa zuwa masa gaisuwar mahaifansa shine, a lokacin ana son a kamashi a Kano. https://www.tiktok.com/@namanzaallah0/video/7581668909644811538?_t=ZS-928VxwbbsKf&_r=1
Kalli Bidiyon: Majalisa ta kammala tantance Dambazau da FFK a matsayin jakadu

Kalli Bidiyon: Majalisa ta kammala tantance Dambazau da FFK a matsayin jakadu

Duk Labarai
Majalisar Dattijai ta kammala tantance Femi Fani Kayode da Abdulrahman Dambazau a matsayin jakadu wanda shugaba Tinubu zai aika kasar waje. A baya dai dukansu sun taba zuwa majalisar inda aka tantancesu, shiyasa yanzu da suka je sai majalisar tace musu kawai su wuce. https://twitter.com/Imranmuhdz/status/1999092298504933606?t=YAkZeDxEXKAkUlSQcV3xZA&s=19 https://twitter.com/Imranmuhdz/status/1999119860899418599?t=Yb9U7kI6UM1vdlBGvKBy3w&s=19
Kalli Bidiyon: Trump ka gaggauta ka zo kamin su gama damu, yanzu haka ma sun sa an rufe min shafina na Facebook>>Rev. Ezekiel Dachomo ya bayyana

Kalli Bidiyon: Trump ka gaggauta ka zo kamin su gama damu, yanzu haka ma sun sa an rufe min shafina na Facebook>>Rev. Ezekiel Dachomo ya bayyana

Duk Labarai
Malamin Kirista, Rev. Ezekiel Dachomo ya roki shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya gaggauta ya zo Najeriya inda yace yazo kamin a gama dasu. Ya kawo misalin cewa yanzu haka shi an sa an rufe masa shafinsa na Facebook. Rev. Ezekiel Dachomo dai na daya daga cikin na gaba-gaba dake son Kasar Amurka ta kawo dauki Najeriya. https://twitter.com/ezekieldachomo0/status/1999081251916112013?t=icVkjZj14fTLkkkayG2uPg&s=19
Kalli Bidiyon yanda hàtsànìyà ta kaure a majalisa aka so a baiwa Hammata Iska saboda gayyatar gwamnan CBN saboda batan Naira Triliyan 11>>Wasu ‘yan majalisar sun yadda a gayyaceshi inda wasu suka ce basu yadda ba

Kalli Bidiyon yanda hàtsànìyà ta kaure a majalisa aka so a baiwa Hammata Iska saboda gayyatar gwamnan CBN saboda batan Naira Triliyan 11>>Wasu ‘yan majalisar sun yadda a gayyaceshi inda wasu suka ce basu yadda ba

Duk Labarai
' Yan majalisar Wakilai sun tattauna bukatar gayyatar gwamnan babban bankin Najeriya, CBN, Cordoso saboda zargin batan wasu kudade har Naira Tiriliyan 11. Saidai kan 'yan majalisar ya rabu inda wasu suka amince a gayyaci gwamnan CBN din wasu kuma sun ce basu amince ba. Muhawara ta yi zafi akan hakan inda aka rika gayawa juna magana da nuna yatsa. https://twitter.com/thecableng/status/1998841059497934985?t=CgGvcKBNth4voAhpc76kmg&s=19