Thursday, March 26
Shadow
Albashin da nake biyan Direbobin Tankana ya fi na wanda ya kammala jami’a>>Inji Dangote

Albashin da nake biyan Direbobin Tankana ya fi na wanda ya kammala jami’a>>Inji Dangote

Duk Labarai
Attajirin Najeriya, Aliko Dangote ya bayyana cewa, Albashin da yake biyan direbobin Tankarsa ya fi na wanda ya kammala jami'a. Dangote ya bayyana hakane a wata ganawa da yayi da manema labarai inda yayi karin haske kan rikicinsa da Kungiyar NUPENG. Ya kuma gayyaci direbobin NUPENG duk wanda bai da aiki ya je zai bashi aikin tukin. Dangote yace Albashin Direban tankarsa ya nunka mafi karancin Albashin sau 4 wanda akalla zai kai sama da Naira dubu dari uku kenan.

DSS ta maka Sowore da X da Facebook a kotu saboda ya kira shugaba Tinubu me laifi kuma ya zargi shugaban kasar da fadar ba daidai ba game da magance matsalar rashawa da cin hanci a Najeriya

Duk Labarai
Hukumar 'yansandan farin kaya ta DSS ta maka mawallafin jaridar Sahara reporters, Omoyele Sowore a kotu bisa zarginsa da kiran shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu me laifi. Sannan an zargi Sowore da kuma bayyana shugaban kasar a matsayin makaryaci saboda yace yayi ikirarin magance matsalar rashawa da cin hanci a kasar Brazil amma Sowore yace maganar ba gaskiya bace. Sowore ya wallafa cewa DSS na shirin kaishi kotu kuma a shirye yake idan an kaishi Kotun ya ansa gayyata.
Babu Yunwa a Najeriya>>Inji Me magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga

Babu Yunwa a Najeriya>>Inji Me magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga

Duk Labarai
Me magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya musanta ikirarin tsohon Mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar cewa akwai yunwa a Najeriya. Atiku yace yunwar dake Najeriya da Talauci ka iya tunzura mutane su fita zanga-zanga irin wadda ake yi a kasashen Duniya. Saidai me magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya musanta maganar ta Atiku inda yace Atiku be san halin da Najeriya take ciki ba a yanzu dan an kama hanyar ci gaba. Yace Hukumar kididdiga ta kasa, NBS ta fitar da bayanai cewa farashin kayan masarufi sun yi kasa, sannan a baya tace kudaden shigar Najeriya sun karu ta bangaren da ba na man fetur ba. Sannan yace Tinubu ya biya basuka da yawa da ake bin Najeriya. Yace kuma Tinubu ya dauki matakai na gyara kasa ba tare da tsoro ba.
Shugaba Tinubu ya yanke tudun da yake ba tare da ya kammala dan ya dawo gida Najeriya ya ci gaba da aiki>>Fadar Shugaban kasa

Shugaba Tinubu ya yanke tudun da yake ba tare da ya kammala dan ya dawo gida Najeriya ya ci gaba da aiki>>Fadar Shugaban kasa

Duk Labarai
Fadar Shugaban kasa ta sanar da cewa, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya yanke hutun da yake ba tare da kammalawa ba ya dan dawowa gida Najeriya. Me magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin. Yace shugaba Tinubu zai dawo gida Najeriya ranar Talata dan ci gaba da ayyukan raya kasa.
Gwamnati ta bayyana jihohi 11 da zasu fuskanci ambaliyar ruwa tsakanin nan da ranar Alhamis, Karanta ka ji ko jiharka na ciki

Gwamnati ta bayyana jihohi 11 da zasu fuskanci ambaliyar ruwa tsakanin nan da ranar Alhamis, Karanta ka ji ko jiharka na ciki

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta fitar da hasashe na jihohi 11 da ka iya fuskantar ambaliyar ruwa tsakanin ranar Lahadi da ranar Alhamis. Ma'aikatar Muhalli ta tarayya ce ta fitar da wannan sanarwar inda tace jihohin da lamarin zai shafa sun hada da: Adamawa State (Ganye, Natubi); Benue State (Abinsi, Agyo, Gogo, Ito, Makurdi, Udoma, Ukpiam); Nasarawa State (Agima, Rukubi, Odogbo); Taraba State (Beli, Serti, Donga); Delta State (Umugboma, Umukwata, Abraka, Aboh, Okpo-Krika); da Niger State (Rijau). Sauran Jihohin sune Kebbi State (Ribah); Kano State (Gwarzo, Karaye); Katsina State (Jibia); Sokoto State (Makira); da Zamfara State (Kaura Namoda, Shinkafi, Maradun, Gusau, Anka, Bungudu). Saidai mu yi fatan Allah ya tsare.
Ina goyon bayan ciren tallafin man fetur da shugaba Tinubu yayi>>Inji Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II

Ina goyon bayan ciren tallafin man fetur da shugaba Tinubu yayi>>Inji Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II

Duk Labarai
Me martaba sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya bayyana cewa, yana goyon bayan cire tallafin man fetur da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya yi. Ya bayyana hakane a wajan wani taron marubuta da aka gayyaceshi. Sarkin Yace Da ba'a cire tallafin Man fetur din ba da Najeriya ta durkushe. Sarki Sanusi na daga cikin na gaba-gaba wajan bayar da shawarar daina biyan tallafin man fetur shekaru da dama da suka gabata.
AbinYa Tabbata: Dangote Ya Tura Motoci 1,000 Masu Amfani Da Gas Don Fara Dakon Man Fetur Kyauta

AbinYa Tabbata: Dangote Ya Tura Motoci 1,000 Masu Amfani Da Gas Don Fara Dakon Man Fetur Kyauta

Duk Labarai
Yau Litinin, manyan motocin dakon man fetur guda 1,000 mallakin kamfanin Dangote, masu amfani da iskar gas (CNG), sun fara aikin dakon man fetur daga matatar man Dangote zuwa gidajen mai a sassan Najeriya kyauta ba tare da caji ba. Wannan mataki na daga cikin kokarin rage tsadar man fetur da kuma karancin da ake fuskanta a wasu yankuna. Ana sa ran hakan zai taimaka wajen kara wadatar man fetur da saukaka farashinsa ga 'yan kasa. Sai dai, a baya irin wannan yunkuri ya fuskanci turjiya daga wasu bangarori, musamman kungiyar direbobi da kuma dillalan man fetur, wadanda ke ganin hakan na iya shafar sana’arsu. Yaya kuke kallon wannan mataki na Dangote ko hakan zai taimaka wajen rage wahalar man fetur a kasar nan, ko kuwa akwai wata barazana da ke tattare da hakan ga masu zaman kansu? ...
Kalli Bidiyo: Maza basu kare ba da mace zata rika neman mace ‘yar Uwarta, idan kika samu maza 10 kika basu Naira Dubu-Dubu da gudu zasu rika zuwa har gida>>Inji Tauraruwar Kannywood

Kalli Bidiyo: Maza basu kare ba da mace zata rika neman mace ‘yar Uwarta, idan kika samu maza 10 kika basu Naira Dubu-Dubu da gudu zasu rika zuwa har gida>>Inji Tauraruwar Kannywood

Duk Labarai
Tauraruwar Kannywood ta bayyana cewa, maza basu kare ba da mace zata rika nema mace 'yar uwarta. Ta bayyana hakane a wata hira da aka yi da ita. Tace idan mace ta samu maza 10 ta basu dubu-dubu har gida zasu rika zuwa. Ta bayyana hakane a wata hira da aka yi da ita. https://www.tiktok.com/@mustaphayalo/video/7549847883604954376?_t=ZS-8zkDdUh9hdB&_r=1
Kalli Bidiyon: Kwanaki 2 bayan kammala dafa shinkafa a Tukunya mafi girma a Duniya, Har yanzu akwai sauran shinkafar bata kare ba

Kalli Bidiyon: Kwanaki 2 bayan kammala dafa shinkafa a Tukunya mafi girma a Duniya, Har yanzu akwai sauran shinkafar bata kare ba

Duk Labarai
Rahotanni sun ce kawanaki 2 bayan kammala dafa shinkafar Hilda Baci wadda ta dafa a Tukunya mafi girma a Duniya, har yanzu akwai sauran shinkafar bata kare ba. Hilda Baci dai ta dafa shinkafa buhu 200 wanda kuma mutane 20,000 suka bayyana son zuwa wajan dan su ci. Saidai duk da haka shinkafar bata kare ba inda a wasu lokutan aka ga Hilda na rokon Mutane su zo su ci shinkafar dan bata san yanda zata yi da ita ba. https://twitter.com/ChuksEricE/status/1967215847782670520?t=x--2fHoNqww6bmdclpS0VQ&s=19