Hukumar JAMB ta sanya 150 a matsayin mafi karancin makin shiga Jami’a
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":["local"],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false}
Hukumar shirya jarabawar JAMB ta saka makin 150 a matsayin mafi karancin maki na shiga jami'a.
Sannan ta saka maki 100 a matsayin maki mafi karanci na shiga kwalejojin kimiyya da fasaha da na Ilimi.
Sannan ta saka makin 140 a matsayin mafi karancin makin shiga makarantun koyar da aikin jinya.
An amince da wannan maki ne a zama da aka yi tsakanin wakilan shuwagabannin jami'o'in da shugaban hukumar JAMB, Prof. Is-haq Oloyede, a Abuja ranar Talata.








