Wednesday, March 4
Shadow
Kalli Bidiyo: Ji kalaman Soyayyar da Rarara ya gayawa uwargidansa a gaban Amarya A’ishatulhumaira da suka dauki hankula

Kalli Bidiyo: Ji kalaman Soyayyar da Rarara ya gayawa uwargidansa a gaban Amarya A’ishatulhumaira da suka dauki hankula

Duk Labarai
A wani Bidiyo da ya bayyana ya karade kafafen sada zumunta, An ga Tauraron mawakin siyasa Dauda Kahutu, Rarara tare da uwargidansa. An ji kuma ya bayyana ta da ransa. A wajan dai ta kasa sakin jiki inda yake cewa kunya take ji. https://www.tiktok.com/@fmkclothingnig_/video/7542292556172856594?_t=ZS-8zD9P6RomLR&_r=1
Kungiyar malaman jami’a ta yi barazanar shiga yajin aikin da ba’a taba ganin irinsa ba

Kungiyar malaman jami’a ta yi barazanar shiga yajin aikin da ba’a taba ganin irinsa ba

Duk Labarai
ASUU: Mun shirya shiga yajin aikin da ba a taɓa irin sa a Nijeriya ba - ASUU. Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta bayyana cewa tana shirye-shiryen shiga babban yajin aiki fiye da duk wanda aka taba yi, muddin gwamnati ta gaza aiwatar da yarjejeniyar 2009 da aka kulla tsakaninta da kungiyar. Sashen ASUU na Jami’ar Calabar (Unical) ne ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a Calabar, ranar Talata. Shugaban sashen, Dr. Peter Ubi, ya ce lokaci ya yi da gwamnatin tarayya za ta cika alkawurran da suka dade suna jinkiri, wadanda aka tsara domin inganta matsayin ilimin jami’a a kasar. Ya bayyana cewa za a fara yajin aikin da zarar babban kwamitin ASUU na kasa ya bayar da sanarwa bayan taron da za a gudanar a ranar 28 ga watan Agusta. Daga cikin bukatu...
Kalli Bidiyon da Alpha Charles Borno ta dora inda aka ganta “Ba Wqndo” ya jawo cece-kuce

Kalli Bidiyon da Alpha Charles Borno ta dora inda aka ganta “Ba Wqndo” ya jawo cece-kuce

Duk Labarai
Tauraruwar Tiktok, me sayar da kayan Mata dana maza, Alpha Charles Borno ta dauki hankula bayan Bidiyon fata dora inda aka ganta zaune a cikin mota Da yawa sun bayyana cewa bata sanye da wando wanda hakan ya jawo cece-kuce. Saidai wasu sun ce sun tana da wando. Lamarin dai ya jawo zazzafar muhawara. https://www.tiktok.com/@alphacharlesborno/video/7541963311210892552?_t=ZS-8zD6GTs339l&_r=1
Da Duminsa: Hukumar kula da jiragen kasa ta Najeriya, NRC, ta dakatar da jigilar fasinja daga Kaduna zuwa Abuja

Da Duminsa: Hukumar kula da jiragen kasa ta Najeriya, NRC, ta dakatar da jigilar fasinja daga Kaduna zuwa Abuja

Duk Labarai
Hukumar kula da sufurin jiragen kasa ta Najeriya, NRC ta sanar da dakatar da sufurin jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna, har sai abinda hali yayi. Hukumar ta sanar da hakane jim kadan bayan hadarin da aka samu bayan tashin jirgin kasan daga Abuja zuwa Kaduna bayan da ya kaucewa taragonsa. Daraktan hukumar, Kayode Opeifa ne ya sanar da haka a Abuja ga manema labarai, Ya musanta rade-radin da ake yi cewa dama jirgin kasan yana da matsala. Yace jami'an hukumar su dana hukumar bincike ta kasa, (NSIB) sun halarci wajan faruwar hadarin inda yace suna kan bincike kan lamarin. Ya kuma kara da cewa, sun fara shirin mayarwa da fasinjojin fake cikin jirgin kudaden tikiti da suka saya. Yace mutane 6 sun ji raunika ba masu muni ba kuma an basu kulawar data kamata.
Hattara, Hukumar NAFDAC ta yi gargadi ga wanda basu son daukar ciki, inda tace an shigo da Maganin hana daukar ciki na Boge Najeriya, Ji yanda zaku ganeshi

Hattara, Hukumar NAFDAC ta yi gargadi ga wanda basu son daukar ciki, inda tace an shigo da Maganin hana daukar ciki na Boge Najeriya, Ji yanda zaku ganeshi

Duk Labarai
Hukumar kula da magunguna da abinci ta kasa, NAFDAC ta yi gargadi cewa an shigo da maganin hana daukar ciki me suna Postinor na bogi Najeriya. Hukumar tace ta tabbatar da hakan ne bayan da hukumar Society for Family Health (SFH) wadda itace aka yadda ta shigo da maganin ta bayyana cewa ba itace ta shigo da maganin boge din ba. NAFDAC tace yanda za'a gane maganin na boge shine, rubutunsa kanana ne, sannan an yi kuskuren rubuta kalmar Verify inda aka rubuta Veify. Sannan kuma akwai kuskuren rubutun Distnibuted in Nigeria maimakon a rubuta, distributed in Nigeria. Hukumar tace wannan magani na jabu na nan yana yawo a Najeriya kuma akwai yiyuwar yana dauke da sinadarai masu cutarwa dan haka ta nemi a gujeshi.
Kalli Yanda a Maulidin Bana, Sheikh Qaribu Kabara Ya kawo tsarabar Reshen Itaciyar Annabi Adamu(AS)

Kalli Yanda a Maulidin Bana, Sheikh Qaribu Kabara Ya kawo tsarabar Reshen Itaciyar Annabi Adamu(AS)

Duk Labarai
Bishiyar Annabi Adamu A.S. Tsarabar Mawloudin Bana a gidan Qadiriyya ita ce, reshen Bishiyar Itaciyar Annabi Adamu A.S.Bayan an yi bukin ɗaga tuta an fara baje kolin kayan tarihi a gidan sakamakon shiga bukin maulidin a Kano. Inda aka gano Qaribu Kabara tare da rike wani Reshe da ake cewa reshen bishiyar Annabi Adamu ne da aka kawo masa daga kasar Saudiyya a matsayin kyautar bangirma saboda haɗinkan da ya bayar wajen daƙile Sheikh Abduljabbar Kabara ɗan uwansa da ake zargin zai shiga Shi'a.Rahoton: Shawus Assufy NaTa'ala Me za ku ce!
Mun kulla huldar kudi, harkar lafiya, Sufuri da kasar Brazil>>Inji Shugaba Tinubu

Mun kulla huldar kudi, harkar lafiya, Sufuri da kasar Brazil>>Inji Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, Najeriya da kasar Brazil sun kulla huldar kasuwanci data hada da Kudi, Harkar lafiya, da sufuri da kuma huldar diflomasiyya. Ya bayyana hakane a shafinsa na sada zumunta inda yace a yanzu sun kulla huldar tashin jirage daga Najeriya zuwa kasar Brazil Kai tsaye. Sannan akwai maganar kimiyya da fasaha da sauransu.
Kalli Bidiyo: Akwai wanda yace mana idan Izala Gaskiya ce kada Allah yasa ya kai shekara me zuwa, kuma baikai labari ba, kamin shekara ta zagayo ya riga mu gidan gaskiya>>Inji Sheikh Yusuf Sambo Rigachukun

Kalli Bidiyo: Akwai wanda yace mana idan Izala Gaskiya ce kada Allah yasa ya kai shekara me zuwa, kuma baikai labari ba, kamin shekara ta zagayo ya riga mu gidan gaskiya>>Inji Sheikh Yusuf Sambo Rigachukun

Duk Labarai
Malamin Addinin Islama, Sheikh Yusuf Sambo Rigachukun ya bayar da labarun irin mutanen da ya kara dasu a baya kuma basu kai labari ba. Malam yace daga cikinsu akwai wanda yace idan Izala Gaskiyace kada Allah ya kaishi shekara me zuwa kuma baikai shekarar me zuwa ba. Malam ya bayyana hakane a wajan tafsir da yake yi. https://www.tiktok.com/@saleemyusufmuhammadsambo/video/7541886797857426695?_t=ZS-8zCarB4l1tI&_r=1