Wednesday, March 4
Shadow
Duk da kokarin shugaba Tinubu na rage farashin magunguna a Najeriya, Farashin Magungunan sai kara tashi suke

Duk da kokarin shugaba Tinubu na rage farashin magunguna a Najeriya, Farashin Magungunan sai kara tashi suke

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya yi yunkurin rage farashin magunguna a Najeriya dan samarwa musamman talakawa da masu karamin karfi saukin rayuwa. Saidai duk da wannan, ana ci gaba da samun hauhawar farashin magunguna. A watan Yuni na shekarar 2024 ne Ministan Lafiya,Muhammad Pate ya bayyana cewa, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya cire haraji akan magunguna da ake shigowa dasu Najeriya da kayan aikin hada magunguna, musamman dan a saukaka farashin hada magungunan a Najeriya. Saidai rahoton jaridar Punchng yace har yanzu magunguna irin na su hawan jini da zazzabin cizon Sauro da sauransu ba su yi sauki ba.
Bakin da aka ga fuska ta tayi a lokacin da BBChausa suka yi hira dani yawan aski ne yasa amma bana amfani da man kara hasken fata, ni Farine, duka jikina Farina>>Inji Gfresh Al-amin

Bakin da aka ga fuska ta tayi a lokacin da BBChausa suka yi hira dani yawan aski ne yasa amma bana amfani da man kara hasken fata, ni Farine, duka jikina Farina>>Inji Gfresh Al-amin

Duk Labarai
Tauraron fina-finan Hausa, Gfresh Al-amin ya bayyana cewa, duka jikinsa Farine. Ya bayyana hakane a wani Bidiyo daya wallafa a shafinsa na Tiktok inda yace ko hirar da aka yi dashi a BBChausa aka ga fuskarsa ta yi duhu, saboda yawan aski ne. Gfresh ya kara da cewa, baya amfani da man kara hasken fata. https://www.tiktok.com/@gfreshfanpage/video/7542643231998135560?_t=ZS-8zBwLZmWRW4&_r=1
Kalli Bidiyo: Yanda wani yawa  Sheikh Sani Yahya Jingir Ihu a masallaci yace masa nan ba wajan Kamfe bane

Kalli Bidiyo: Yanda wani yawa Sheikh Sani Yahya Jingir Ihu a masallaci yace masa nan ba wajan Kamfe bane

Duk Labarai
Bidiyo ya bayyana inda aka ga wani dalibin babban malamin Izala na Jos, Sheikh Sani Yahya Jingir yana korafi kan wani da yawa malamin Ihun bama so da cewa, nan masallaci ne ba wajan kamfe ba. Dalibin ya bayyana cewa, wannan cin fuska ne ga Malam kuma ba zasu dauka ba, sun sa a nemo musu wadanda sukawa malamin wannan abu. Ya bayyana hakane a shafinsa na Tiktok: https://www.tiktok.com/@saleemyusufmuhammadsambo/video/7542257130359753991?_t=ZS-8zAeQvh2rHU&_r=1
Ji yanda kotu ta daure wata matashiya tsawon shekaru 7 ko ta biya tarar Naira Dubu dari hudu da hamsin bayan da Wani ya aika mata Naira Dubu 150 ta sameshi a gidansa amma ta cinye kudin kuma ta ki zuwa

Wannan matashiyar me suna Jennifer ta fuskanci hukuncin daurin shekaru 7 ko biyan tarar Naira 450 bayan da kotu ta sameta da laifin zamba da bata lokaci. Wani mutum ne me suna Emmanuel ne da suka hadu a kafar sada sumunta ya aika mata da Naira dubu 150 dan ta sameshi a Abuja. Saidai ta cinye kudin kuma ta ki zuwa ta biya masa bukata. Dalilin hakane ya kaita kotu. Kotu dai ta sameta da laifin zamba da bata lokaci dan haka aka yanke mata hukuncin Daurin shekaru 7 a gidan yari ko biyan tarar Naira dubu. 450
Kalli Bidiyo: Sunana Sunday Tinubu, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu Babana ne, ina neman haduwa dashi ruwa a jallo

Kalli Bidiyo: Sunana Sunday Tinubu, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu Babana ne, ina neman haduwa dashi ruwa a jallo

Duk Labarai
Wannan mutumin ya bayyana cewa, sunansa Sunday Tinubu inda yace shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu mahaifinsa ne. Yace tun shugaban kasar bashi da komai ya haifeshi. A jawabinsa, yace mahaifiyarsa 'yar rawar Fela ce kuma a haka suka hadu da Tinubu suka haifeshi amma ita ta rasu. https://www.tiktok.com/@cyberopsng/video/7541292483121138952?_t=ZS-8z7DOE1h3ZJ&_r=1
Kalli Bidiyon Tambaya: Rashin Kulawar Mijina yasa na Afkawa Alfasha, Har Ciki ya shiga, menene Mafita?

Kalli Bidiyon Tambaya: Rashin Kulawar Mijina yasa na Afkawa Alfasha, Har Ciki ya shiga, menene Mafita?

Duk Labarai
Wata matar aure ta aikawa da malam Tambayar cewa rashin kulawar da mijinta baya bata tasa ta afka zina . Tace ta gaya masa amma sai yace ta tafi gidansu. Tace bayaj taje gidansu ta yi jini, sai yace ta koma. Tace amma bayan ta koma sai ciki ya shiga kuma ta gano cewa bayan ta yi jinine cikin ya shiga. Tace mijinta yace a zubar da cikin amma ita ta kiya. https://www.tiktok.com/@nuraabunasir/video/7540630374385241351?_t=ZS-8z79hgia69R&_r=1
Yaudarar mu ADC suke, ba zasu iya tsinana komai ba ko da sun samu mulki>>Inji Datti Baba Ahmad

Yaudarar mu ADC suke, ba zasu iya tsinana komai ba ko da sun samu mulki>>Inji Datti Baba Ahmad

Duk Labarai
Tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar ADC, Datti Baba Ahmad ya bayyana cewa, Jam'iyyar ADC yaudarar talakawa kawai suke ko sun samu mulki babu wani ci gaba da zasu iya kawowa. Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a Channels TV ranar Juma'a. Datti na wannan maganar ne duk da cewa, Peter Obi wanda suka yi takara tare a yanzu yana jam'iyyar ADC. Datti dai yace, yana fatan Peter Obi zai koma jam'iyyar Labour party yayi takara acan. Da aka tambayeshi ko zai sake yiwa Peter Obi takarar mataimakin shugaban kasa? Datti Baba Ahmad ya ce Eh.
Usman da Umar (AS) zasu iya canja hukuncin da Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) yayi kuma hakan yayi daidai>>Inji Sheikh Dr. Ahmad Gumi

Usman da Umar (AS) zasu iya canja hukuncin da Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) yayi kuma hakan yayi daidai>>Inji Sheikh Dr. Ahmad Gumi

Duk Labarai
Babba Malamin Addinin Islama, Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya bayyana cewa, Sahabban Annabi(Sallallahu Alaihi Wa Sallam) Umar da Usman (AS) zasu iya canja hukuncin sa Annabi(Sallallahu Alaihi Wa Sallam) yayi kuma hakan yayi daidai. Yace Annabi(Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya basu wannan matsayi na cewa, duk hukuncin da suka yi ya zama shari'a. Malam ya bayyana hakane a wajan karatun da yake ranar Juma'a a masallacin Sultan Bello dake Kaduna a ranar 22/8/2025. Wakilin hutudole ya halarci wajan karatun inda malam yayi wannan maganane a yayin da yake bayar da misalin ikirarin 'yan shi'a na cewa, Khalifanci Aliyu (AS) ne ya kamata a baiwa kuma Annabi(Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya bar wasiyya kan hakan. Malam yace ko da ace Annabi(Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya bar wasiyya akan hakan am...
Kalli Bidiyo: Yanzu mun gano cewa Tinubu baya kishin Addini, Baya sauraren mu, Muna fatan Allah ya saukeshi karya kara shekara daya akan Mulki>>Inji Malaman da suka tallata Tinubu a 2023

Kalli Bidiyo: Yanzu mun gano cewa Tinubu baya kishin Addini, Baya sauraren mu, Muna fatan Allah ya saukeshi karya kara shekara daya akan Mulki>>Inji Malaman da suka tallata Tinubu a 2023

Duk Labarai
Daya daga cikin malaman da suka tallata shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a zaben shekarar 2023 ya fito ya bayyana cewa a yanzu basu tare da shugaban kasar. Yace sun yiwa shugaban kasar kamfe da zuciya daya dan ci gaban Addini, amma sun gano cewa, ba ci gaban addinine a gabansa ba. Yace dan haka suna rokon Allah kamar yanda ya dorashi mulki Allah a saukeshi: https://www.tiktok.com/@yusufautalazio1/video/7539794814984850696?_t=ZS-8z6xC7WQYNc&_r=1