Friday, April 25
Shadow
Na bauta wa Kaduna da gaskiya kuma ina alfahari da hakan – El-Rufai

Na bauta wa Kaduna da gaskiya kuma ina alfahari da hakan – El-Rufai

Kaduna, Siyasa
Kwamitin da Majalisar dokokin jihar Kaduna ta kafa kan nazari game da kuɗaɗen da aka kashe a gwamnatin da ta gabata a jihar ya miƙa sakamakon bincikensa a yau. Cikin shawarwarin da kwamitin ya bayar har da na buƙatar hukumomi su binciki tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufa'i. Lokacin da ya gabatar da rahoton a ranar Laraba, shugaban kwamitin, Henry Zacharia ya ce an gano cewa akasarin kuɗin bashin da jihar ta karɓa a zamanin mulkin El-Rufa'i, ko dai ba a yi amfani da su kan abin da aka ciyo bashin domin su ba ko kuma ba a bi ƙa'ida wajen cin bashin ba. Da yake karɓar rahoton, shugaban majalisar dokokin jihar Kaduna, Yusuf Liman ya ce kuɗi naira biliyan 423 ne suka zurare a lokacin gwamnatin El-Rufa'i tare da jefa jihar cikin ƙangin bashi. Sai dai tsohon gwamnan ya ce binciken da...
A yaune Ministan kudi zai gabatar wa da shugaba Tinubu sabon daftarin mafi karancin Albashi

A yaune Ministan kudi zai gabatar wa da shugaba Tinubu sabon daftarin mafi karancin Albashi

Siyasa
Ministan kudi, Wale Edun a yau ne ake sa ran zai gabatarwa da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da sabon daftarin mafi karancin Albashi. Ko da ita kanta kungiyar kwadago, NLC ta dage zaman ta da gwamnatin tarayya sai yau din Alhamis da ake tsammanin sake ganin nawane gwamnatin tarayyar zata kara akan Naira dubu 60 da a baya NLC din ta ki amincewa da ita a matsayin mafi karancin Albashi. Saidai a rahotanni na baya, kungiyar TUC tace ba zata amince da Kari dan kadan ba akan Naira dubu 60 din. Sannan kuma tace ba ta dage akan sai an biyata Naira Dubu 400 ba, kawai dai abinda take nema shine a biya albashi da zai wadaci ma'aikaci.
Lokacin Malam Nasiru Ahmad El-Rufai na gwamnan Kaduna an cire Naira Biliyan 423 daga asusun bankin jihar ba tare da yin wani aiki da kudin ba>>Majalisar Jihar

Lokacin Malam Nasiru Ahmad El-Rufai na gwamnan Kaduna an cire Naira Biliyan 423 daga asusun bankin jihar ba tare da yin wani aiki da kudin ba>>Majalisar Jihar

Kaduna, Siyasa
Majalisar Jihar Kaduna ta bayyana cewa a lokacin Malam Nasiru Ahmad El-Rufai yana mulkin jihar, an cire Naira Biliyan 423 ba tare an yi wani aiki da kudin ba daga asusun gwamnatin jihar. Hakanan kuma an cire wata Biliyan 30 daga ofishin Kwamishinan kudi da babban akanta na jihar. Jimulla, an cire Tiriliyan 1.4 daga asusun gwamnatin jihar Kaduna. Hakan ya bayyana ne daga bakin dan majalisar jihar ta kaduna, Henry Mara wanda shine me magana da yawun Majalisar a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Channels TV.
Domin Kawo Saukin Hauhawar farashin kayan masarufi, Gwamnati zata cire harajin VAT akan kayan abinci da ake shigowa dasu Najeriya

Domin Kawo Saukin Hauhawar farashin kayan masarufi, Gwamnati zata cire harajin VAT akan kayan abinci da ake shigowa dasu Najeriya

Siyasa
Domin kawowa al'umma saukin rayuwa, Gwammatin tarayya ta sanar da shirin cire harajin VAT daga shigo da kaya da hukumar Kwastam ke karba akan kayan abinci na tsawon watanni 6. Gwammati zata dauki wannan mataki ne dan magance matsalar hauhawar farashin kayan abinci. Yanzu haka an aikawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da rahoto kan wannan lamari dan ya duba ya saka masa hannu. Kayan da za'a cirewa harajin sun hada da kayan abinci, magunguna, abincin kaji, Fulawa da sauransu. Da yawan 'yan Najeriya dai na kukan tsadar rayuwa, abin jira a gani shine idan wannan mataki zai haifar da da me ido.
Bama tunanin hadewa da kowace jam’iyya>>PDP

Bama tunanin hadewa da kowace jam’iyya>>PDP

Siyasa
Jam'iyyar PDP ta bayyana cewa, bata tunanin hadewa dan yin maja da kowace jam'iyya. Hakan na zuwane yayin da ake tsammanin Atiku da Peter Obi zasu hade dan hada karfi su kayar da jam'iyyar APC. Hakanan a bangaren Labour party, shima kakakin kungiyar yakin neman zaben Peter Obi, Yunusa Tanko ya bayyana cewa Peter Obi baya tunanin hadewa da kowa dan samun karfi. Jam'iyyar PDP tace bata neman hadewa da kowa amma tana maraba da tsaffin membobinta wanda suke son dawowa cikinta. Kakakin PDP, Debo Ologbunagba ne ya bayyana hakan inda yace a rijistar da suke yi yanzu haka, mutane da yawa a matakin mazabu sai shiga PDP suke wanda hakan alamace ta cewa har yanzu PDP jam'iyyar Al'ummace.
An gano gwamnatin Tinubu na biyan Tallafin man fetur ta bayan fage duk da ikirarin da take na cewa ta cire tallafin

An gano gwamnatin Tinubu na biyan Tallafin man fetur ta bayan fage duk da ikirarin da take na cewa ta cire tallafin

Siyasa
Wani sabon rahoto da jaridar Punch ta yi ya bayyana cewa, Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu na biyan Tallafin man fetur. Hakanan akwai tanadin biyan tallafin ma har na Naira Biliyan 5.4 da za'a biya nan da karshen shekarar da muke ciki. Hakan na kunshene a cikin wani daftarin kokarin fitar da Najeriya daga matsin tattalin arzikin da take fama dashi. Daftarin ya kunshi baiwa mutane da yawa 'yan Najeriya kudin tallafi da kuma kawo saukin farashin kayan masarufi da sauransu. Rahoton yace gwamnati ta kasa cire tallafin man fetur din gaba daya lura da yanda a yanzu haka ake tsaka da matsin tattalin arziki me tsanani. Wannan daftari za'a yi amfani dashi ne cikin watanni 6 masu zuwa. Gwamnatin Bola Ahmad Tinubu dai ta na ta ikirarin cewa ta cire tallafin man fetur amma...
Da Duminsa: Majalisar Jihar Kaduna ta bukaci a kama da hukunta tsohon gwamnan jihar, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai saboda zargin lalata kudin jihar har Naira Biliyan 423

Da Duminsa: Majalisar Jihar Kaduna ta bukaci a kama da hukunta tsohon gwamnan jihar, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai saboda zargin lalata kudin jihar har Naira Biliyan 423

Siyasa
Majalisar jihar Kaduna ta nemi a kama da hukunta tsohon gwamnan jihar, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai da mukarrabansa saboda zargin lalata kudin jihar har Naira Biliyan 423. Kwamiti na musamman da aka nada yayi binciken mulkin tsohon gwamnan bisa jagorancin dan majalisa Henry Zacharia ya kammala binciken da mikawa majalisar sakamakon abinda ya gani. Kakakin majalisar, Yusuf Liman ya bayyana damuwa kan yanda yace ake zargin tsohon gwamnan da lalata Naira Biliyan 423. Sannan ana zargin El-Rufai da kuma bayar da kwagila ba bisa ka'ida ba da satar dukiyar jama'a da kuma aikata ba daidai ba. Rahoton kuma yace mafi yawancin kudaden da gwamnatin jihar ta ciwo bashi, ba'a yi amfani dasu yanda ya kamata ba.
Da ka zama talaka dake ta mazakuta, gara ka zama me kudin da be da mazakuta>>Sanata Shehu Sani

Da ka zama talaka dake ta mazakuta, gara ka zama me kudin da be da mazakuta>>Sanata Shehu Sani

Nishadi, Shehu Sani, Siyasa
Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa, da ka zama Talaka me mazakuta, gara ka zama me kudi wanda bashi da maza kuta. Sanata Shehu Sani dai ya bayyana hakane a kan shafinsa na sada zumunta yayin da yake mayarwa da wani martani da yace masa ya yafi mayar da hankali kan lamarin mazakuta fiye da talaka. Lamarin ya samo Asali ne tun bayan da Sanata Shehu Sani ya wallafa magana akan matarnan data yankewa mijinta mazakuta a jihar Kaduna. Sana Sani yace "Matar da ta yankewa mijinta mazakuta a jihar Kaduna ta aikata babban laifi. Yace yawan cin zarafin mazakutar maza da ake yi ya kamata a samar da dokar da zata baiwa mazakutar maza kariya ta yanda za' daina guntuleta da zaginta da lalatata. "The woman who cuts the manhood of her husband in Kaduna has commit...
Casemiro ya saka hannun jari a kungiyar Marbella FC ta kasar Sifaniya

Casemiro ya saka hannun jari a kungiyar Marbella FC ta kasar Sifaniya

Casemiro, Labaran Manchester United
A wani abin ban mamaki, dan kwallon tsakiya na Manchester United, Casemiro ya saka hannun jari a kungiyar Marbella FC ta kasar Sifaniya. Hakanan bayan zuba hannun jarin, a yanzu ya shiga cikin daraktoci masu gudanarwa na kungiyar. Akwai dai tantamar ci gaba da zaman Casemiro a Kungiyar Manchester United indaa ake alakantashi da barin kungiyar. A ranar 3 ga watan Yuni dai an ruwaito cewa, Cristiano Ronaldo ya nemi Casemiro ya koma kungiyar Al nassr su yi wasa tare. Hakanan akwai kungiyoyin Al ahli dana Alqasidiya da suma ke zawarcin Casemiro.