Monday, December 15
Shadow

Da gaske Ronaldo ya musulunta?

Duk Labarai
Masoyan dan kwallon kafa, Cristiano Ronaldo musamman Musulmai sai doki suke dan sanin cewa wai da gaske ya musulunta? Hakan bai rasa nasaba da kasancewarsa yana buga kwallo a kasar Saudiyya wadda kasa ce me tsarki ga Musulunci. Musuluntar Cristiano Ronaldo zata dauki hankula sosai a tsakanin masoyansa da wadanda ma ba masoyansa ba. A bayanan da muke dasu a yayin wannan rubutu, babu wata sahihiyar kafa data tabbatar da cewa, Cristiano Ronaldo ya musulunta. Saidai muna fatan Allah yasa nan gaba ya musulunta.

Ta yaya ake tantance labari

Duk Labarai
Ana Tantance labarine ta hanyar bincike dan gane sahihancin kafar data wallafashi. Ma'ana, kafar data wallafa labarin sahihiya ce, ta saba wallafa labaran gaskiya, sannan sabuwa ce ko tsohuwar kafar yada labarai wadda mutane da yawa suka sani? Sannan ana gane sahihancin labari idan ya zamana kafafen yada labarai da yawa manya da kanana duk sun wallafashi. Ana kuma gane sahihancin labari idan ya zamana an yi hira da wadanda abin ya faru dasu ko ya faru a gaban idanunsu watau shaidu. Ana kuma gane sahihancin labari idan ya zama cewa, an ga Bidiyon faruwar lamarin daga farko zuwa karshe.
Kalli Bidiyo Da Duminsa: A karshe dai, Tankokin Dakon Man fetur na Dangote guda 4000 sun iso Najeriya

Kalli Bidiyo Da Duminsa: A karshe dai, Tankokin Dakon Man fetur na Dangote guda 4000 sun iso Najeriya

Duk Labarai
Rahotanni daga Legas na cewa, Tankokin dakon man fetur na Attajirin Najeriya, Aliko Dangote sun iso Najeriya. An ga Bidiyon yanda ake sauke tankokin daga jirgin ruwa inda tuni aka fara hadasu. Matatar man fetur ta Dangote ta bayyana cewa, nan da ranar 15 ga watan Augusta zata fara jigilar man fetur dinta zuwa sassa daban-daban na Najeriya da sabbin tankokin man. https://twitter.com/thecableng/status/1934887582204084562?t=DQe2Yp2SBeo2bAOBA04pYw&s=19 Saidai kungiyar direbobin tankar man Najeriya sun koka da cewa, hakan zai talautasu
Kalli Bidiyo: Soja me mukamin Kyaftin yayi bayani dalla-dalla dalilin da yasa mahara ke musu wayau suna galaba akansu

Kalli Bidiyo: Soja me mukamin Kyaftin yayi bayani dalla-dalla dalilin da yasa mahara ke musu wayau suna galaba akansu

Duk Labarai
Wani soja me mukamin kyaftin yayi bayani dalla-dalla dalilin da yasa 'yan Bindiga ke nasara akansu. Sojan ya bayyana cewa, Ana kama 'yan Bindigar da suka mika kansu ace an canja musu hali sai a daukesu aikin soja. Yace wannan yana sa su rika samun horaswa da sirrin sojoji wanda ke taimakawa wajan yin nasara akansu. Kalli Bidiyon sa: Kotu ta bayar da belin Tsohon Gwamnan CBN, Emefiele akan Naira Biliyan 2
Kotu ta bayar da belin Tsohon Gwamnan CBN, Emefiele akan Naira Biliyan 2

Kotu ta bayar da belin Tsohon Gwamnan CBN, Emefiele akan Naira Biliyan 2

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":["local"],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{"square_fit":1},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":true,"containsFTESticker":false} Babbar kotun tarayya dake Maitama Abuja ta sanar da bayar da Belin Tsohon Gwamnan babban bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele akan Naira Biliyan 2. Ranar Litinin ne kotun ta bayar da belin Emefiele bayan da aka gurfanar dashi bisa zarge-zargen cin hanci da rashawa guda 8 ciki hadda gina rukunin gidaje 753 a Abuja. An kuma zargeshi da amfani da wasu mutane 'yan uwa da abokai wajan satar kudaden Gwamnati.
Najeriya ce kan gaba a yawan fitar da man fetur a Afirka cikin watan Mayu – OPEC

Najeriya ce kan gaba a yawan fitar da man fetur a Afirka cikin watan Mayu – OPEC

Duk Labarai
Ƙungiyar ƙasashe masu arzikin man fetur ta OPEC ta ce duk da raguwar fitar da mai da aka samu a Najeriya, har yanzu ƙasar ce ta fi kowace ƙasa yawa fitar da mai a Afirka. A cikin rahotonta na wata-wata da ta fitar a ranar Litinin, ƙungiyar ta OPEC ta ce fitar da ɗanyen mai daga Najeriya ya ragu zuwa ganga miliyan 1.45 a kullum a watan Mayu — daga ganga miliyan 1.48 da aka samu a watan da ya gabata. Rahoton ya bayyana cewa duk da wannan raguwar, Najeriya ta ci gaba da zama ƙasa kan gaba a yawan fitar da danyen mai a nahiyar Afirka, inda ta zarce ƙasashen Libya da Aljeriya da Kongo. OPEC ta ce ta samo wannan alƙaluma ne daga bayanan da ƙasashe suka bayar kai tsaye. OPEC ta ƙara da cewa alƙaluman da aka samu ya nuna cewa Najeriya ta fitar da ganga miliyan 1.54 a kullum a watan May...
Za a fara sauya tunanin tubabbun ƴanbindigar da suka miƙa makamai a Katsina

Za a fara sauya tunanin tubabbun ƴanbindigar da suka miƙa makamai a Katsina

Duk Labarai
Gwamnatin jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ce za ta soma shirin sauya tunanin tubabbun ƴanbindigar da suka miƙa makamai nan bada jimawa ba. Gwamnatin ta ce za a buɗe azuzuwan koyar da karatu da dubarun koyar da sana'o'i domin sauya tunanin ƴanbindigar, inda daga bisani za su koma cikin al'umma. Hukumar da ke kula da ilimin manya ta jihar ce ke da alhakin tsara yadda shirin sauya tunanin tubabbun ƴanbindigar zai kasance. Ƙarƙashin shirin za a bai wa waɗanda suka miƙa makamansu damar koyon karatun zamani da na addinin musulunci tare da fahimtar da su illar kisan mutane da kuma neman fansa. Daraktar hukumar ilimin manya ta jihar Katsinan Bilkisu Muhammad Kakai, ta tabbatarwa da BBC wannan shiri da gwamnatin jihar zata fara. Daraktar ta sanar da manema labarai...
Kannywood na ta dokin Auren Malika da Abdul M. Shareef

Kannywood na ta dokin Auren Malika da Abdul M. Shareef

Duk Labarai
A yayin da ranar auren taurarin fina-finan Hausa, Abdul M. Shareef da amaryarsa, Maryam Malika ke kara matsowa, Masana'antar Kannywood sai nuna doki take. Da farko dai ganin katin gayyatar auren ne ya fara daukar hankulan mutane inda aka ga cewa ranar 27 ga watan Yuni ne za'a daura auren. Bayan nan kuma sai Hotunan kamin boki ke ta fitowa daga manyan jaruman masana'antar. Ali Nuhu na daga wadanda suka watsa hotunan bikin: MC Ibrahim Sharukhan ma ya wallafa hotunan bikin inda yake ma sabbin ma'auratan fatan Alheri: Shima Alhaji Shehe ya wallafa hotunan auren: Muna fatan Allah ya sanya Alheri ya kaimu Lafiya.
Atiku zamu zaba idan Tinubu yaki tafiya da Shettima a 2027>>Inji Mutane daga Arewa maso gabas

Atiku zamu zaba idan Tinubu yaki tafiya da Shettima a 2027>>Inji Mutane daga Arewa maso gabas

Duk Labarai
Fargaba ta kunno kai a cikin jam'iyyar APC bayan rikicin da ya faru a jihar Gombe wajan taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar daga Arewa maso gabas. Hatsaniya ta kaure a wajan taron bayan da aka bayyana shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a matsayin dan takarar APC da yankin zai goyi baya amma ba'a ambaci sunan mataimakin shugaban kasar, Kashim Shettima ba. Rahotanni sun ce bayan rikicin, wasu wakilai daga jihar sun bayyana cewa, Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar zasu zaba a 2027 idan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu bai tafi da Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa ba a zaben shekarar 2027. Wani daga jihar Adamawa a wajan taron ya bayyana cewa zai koma jam'iyyar PDP muddin aka cire Shettima a matsayin mataimakin shugaban kasa.
Idan baka hada kai da shugaban kasa Tinubu ba, Jihar Zamfara zata tafka Asara>>Sanata Orji Kalu ya gayawa Gwamna Lawal Dare

Idan baka hada kai da shugaban kasa Tinubu ba, Jihar Zamfara zata tafka Asara>>Sanata Orji Kalu ya gayawa Gwamna Lawal Dare

Duk Labarai
Sanata Orji Kalu ya baiwa gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare shawarar ya gyara alakarsa da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. Ya bayyana hakane a ziyarar da ya kai jihar ta Zamfara ya kaddamar da Makarantar Kimiyya da fasaha da kuma sabuwar ma'aikatar mata ta jihar Zamfara da aka gina. Sanata Kalu yace alaka me kyau da shugaban kasa, zata sa jihar Zamfara ta kara samun ayyukan ci gaba. Ya bayyana cewa, ba wai sai Gwamna Dare ya bar jam'iyyar PDP ya koma APC amma alaka me kyau tsakaninsa da shugaban kasa, zata taimaka sosai wajan ci gaban jihar ta Zamfara.