Sunday, December 21
Shadow
Da Duminsa: Kalli Bidiyon yanda Jirgin sojojin Najeriya yayi sukar Dole dauke da sojoji 11 a kasar Burkina Faso

Da Duminsa: Kalli Bidiyon yanda Jirgin sojojin Najeriya yayi sukar Dole dauke da sojoji 11 a kasar Burkina Faso

Duk Labarai
Wannan Jirgin Najeriya me suna C-130 kenan da yayi saukar gaggawa a kasar Burkina Faso bayan da hukumomin kasar suka bukaci hakan. Akwai sojojin Najeriya 11 a cikin jirgin. Kasar Burkina Faso tace irin wannan abu tarwatsa jirgin kawai suke idan aka musu shi. Rahotanni sun ce jirgin na kan hanyar zuwa kasar Senegal ne shine ya ratsha ta Burkina Faso. https://twitter.com/General_Somto/status/1998151523331641803?t=PODshAmoJ5otZLE-EWcosg&s=19
Da Duminsa: Kasar Burina Faso ta fitar da sabon bayani kan Jirgin sojin Najeriya data kama da sojojin Najeriya 11 a ciki

Da Duminsa: Kasar Burina Faso ta fitar da sabon bayani kan Jirgin sojin Najeriya data kama da sojojin Najeriya 11 a ciki

Duk Labarai
Kasar Burkina Faso tace itace ta tursasawa jirgin sojojin Najeriya me suna C-130 ya yi saukar gaggawa saboda basu yadda da shawagin da yake a sararin samaniyarsu ba. Sun ce sun baiwa sojojinsu umarnin duk jirgin da aka gani irin haka ya shiga kasar ba da Izini ba a harbeshi a darkakeshi ba tare da wata-wata ba. https://twitter.com/General_Somto/status/1998153345362796811?t=0jPTQhRgMmVMk9ZtuT6oUw&s=19
Bidiyo Da Duminsa: Hukumomin Gwamnatin Soji ta kasar Burkina Faso sun ce auna rike da sojojin Najeriya 11 bayan da jirginsu yayi saukar gaggawa a kasar

Bidiyo Da Duminsa: Hukumomin Gwamnatin Soji ta kasar Burkina Faso sun ce auna rike da sojojin Najeriya 11 bayan da jirginsu yayi saukar gaggawa a kasar

Duk Labarai
Hukumar mulkin soji ta kasar Burkina Faso tace tana rike da sojojin Najeriya 11 bayan da jirginsu yayi saukar gaggawa a Bobo-Dioulasso dake Burkina Faso. Hukumar tace ta dauki wannan mataki da cewa kutsene Najeriya take shirin yiwa kasar dan jirgin ya shiga sararin samaniyar ta ba tare da izini ba. Kuma tace hukuncin wannan laifi shine Kisa. https://twitter.com/BrantPhilip_/status/1998141332758630422?t=I7qxeWcMGmYnAxZp_hai3g&s=19 Hukumar kasar Burkina Faso tace ta baiwa sojojinta umarnin duk jirgin da ya shigo mata kasa ba da izini ba kawai a bude masa wuta ba wani jiran ba'asi. Rahotanni sun ce jirgin sojin Najeriyar ya keta ta sararin samaniyar Burkina Faso ne akan hanyarsa ta zuwa kasar Senegal.
Tura sojoji kasar Benin Republic da shugaba Tinubu yayi babban laifine da ya kamata ace an tsigeshi daga shugabancin Najeriya>>Inji Lauya

Tura sojoji kasar Benin Republic da shugaba Tinubu yayi babban laifine da ya kamata ace an tsigeshi daga shugabancin Najeriya>>Inji Lauya

Duk Labarai
!Babban lauya me suna Marshal Abubakar ya bayyana cewa aika sojojin Najeriya zuwa kasar Benin Republic da shugaba Tinubu yayi babban laifine da ya kamata ace an tsigeshi daga mulki. Yace tura sojoji zuwa wata kasa doka ta tanadi cewa sai majalisa ta amince amma shugaba Tinubu yayi gaban kansa. A jiya shugaba yi ya aika da sojojin sama dana kasa dan su dakile yunkurin juyin mulkin kasar ta Benin Republic Saidai Lauyan yace wannan mataki ya sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya.
Nayi shaharar da ba zan taba yin taĺauci ba>>Inji Gfresh Al-amin

Nayi shaharar da ba zan taba yin taĺauci ba>>Inji Gfresh Al-amin

Duk Labarai
Tauraron Tiktok, Gfresh Al-amin ya bayyana cewa, Yayi Shaharar da ba zai taba yin Taĺauci ba. Ya bayyana hakane a shafinsa na Tiktok yayin da wasu ke masa dariyar wai an kulle Tiktok live dan haka ya daina samun kudi. Yace shi yayi shaharar da yana samun kamfanoni da yakewa talla dan haka ko ba Tiktok live zai ci gaba da rayuwar jin dadi. Ya kara da cewa babban abinda ya bashi mamaki shine cikin masu murnar zai daina samun kudi saboda an dakatar da Tiktok live hadda tsohuwar matarsa Maryam. Yace wallahi da yayi niyyar bata kyautar Naira Miliyan 1 dan baya so ta shiga wahala amma yanzu ya fasa https://www.tiktok.com/@gfreshfanpage/video/7581545115416546578?_t=ZS-923l2d7ad05&_r=1
Kalli Bidiyon: Magidanci ya koka da cewa, matarsa ta bayar da gidansa jingina ta karbi bashin banki, a yanzu kuma bankin sun kwace gidansa

Kalli Bidiyon: Magidanci ya koka da cewa, matarsa ta bayar da gidansa jingina ta karbi bashin banki, a yanzu kuma bankin sun kwace gidansa

Duk Labarai
Wani magidanci ya dauki hankula sosai akaita tausaya masa bayan da matarsa ta bayar da gidansa jingina ta karbi bashin baki. Kudi dai sun narke kuma bankin sun je har gidansa suna watsar masa da kaya waje. A dauki Bidiyon faruwar lamarin inda ya wallafa a yanar gizo kuma da yawa sun tausaya masa. https://twitter.com/yabaleftonline/status/1997735056547446989?t=ZAAsg-De6PCDZqC4Sm8-lA&s=19
Wannan Cin Amana har Ina: Ji Abinda Magidanci yayi bayan kama yaron dake masa aiki yana aikata Alfàshà da matarsa

Wannan Cin Amana har Ina: Ji Abinda Magidanci yayi bayan kama yaron dake masa aiki yana aikata Alfàshà da matarsa

Duk Labarai
Wani magidanci a Legas dake unguwar Victoria Garden City ya hallakà yaron aikin gidansa bayan kamashi yana aikata Alfasha da matarsa. Yaron aikin dan kimanin shekaru 20 sunansa Nengak kuma dan asalin jihar Filato ne wanda aka daukeshi aiki a gidan yana kai yara makaranta da aiken cefane da sauransu. Me gidan ya fara jin rade-radin cewa yaron na lalata da matarsa. Dalilin haka ya saka kyamarar CCTV kuma ya kamasu turmi da tabarya. Anan ya gayyato yaran layi sukawa yaron aikin gidan nasa duka har ya mutu. Abokin mamacin Bitrus Idi ne ya bayyana haka ga kafar Daily Post inda yace gawar sa na mutuware an ki basu inda 'yansanda suka ce sai sun biya kudi an yi bincike kan dalilin mutuwar tasa.
Kalli Bidiyon: Yanda aka Zargi wata Fastuwa da sayar da mai wanda tace duk wanda yayi amfani dashi yana hana Tshàgyèràn Dhàjì su sàcè mutum

Kalli Bidiyon: Yanda aka Zargi wata Fastuwa da sayar da mai wanda tace duk wanda yayi amfani dashi yana hana Tshàgyèràn Dhàjì su sàcè mutum

Duk Labarai
Wannan Fastuwar ta dauki hankula bayan da aka zargeta da sayar da wani mai Wanda tace duk wanda yayi amfani dashi, 'yan Bindiga ba zasu yi garkuwa dashi ba. An ganta tana karbar kudi tana bayar da man a cocinta. Lamarin dai ya jawo cece-kuce inda da yawa ke cewa akwai salon damfara a lamarin. https://twitter.com/ObaOfVibes/status/1997670841652334788?t=_toe3S-gGnnSVc3HL2aXzA&s=19
Kalli Bidiyon yanda wasu matasa suka Hàllàqà wani shugaban Fulani a jihar Benue, Sojoji sun kama wanda ake zargi suka damkawa ‘yansanda

Kalli Bidiyon yanda wasu matasa suka Hàllàqà wani shugaban Fulani a jihar Benue, Sojoji sun kama wanda ake zargi suka damkawa ‘yansanda

Duk Labarai
Rahotanni daga Ogbobia, dake jihar Benue na cewa, wasu matasa sun yiwa wani shugaban Fulani Kwantan Bauna suka hallaqashi. Sun bai wannan aika-aika ne yayin da yake kan hanyar zuwa garken shanunsa, hakanan sun bi garken shanun suka kashe su sannan suka sace wasu. Wani dake tare da shugaban Fulanin da ya samu kubuta daga hannun maharan ya garzaya gida ya fada, fulanin sun je suka gayawa wasu sojoji dake wajen. Ko da sojojin suka je wajan sun tarar da muharan akan gawar shugaban fulanin. Suna ganin sojojin sai suka tsere. Sojojin dai sun bisu inda suka kama guda daya suka mikashi hannun 'yansanda. Saidai Fulanin sun ce daga baya sun samu labarin 'yansandan sun sakeshi. shahararren dan fafutuka, VDM ne ya bayyana hakan inda ya wallafa hotunan yanda lamarin ya faru, yace f...
Yanzu-Yanzu: Bayan aiko da wakilanta suka ganewa idanunsu abinda ke faruwa a Najeriya, kasar Amurka tace lallai gaba dayan ‘yan Najeriya ne ya kamata a samarwa da tsaro

Yanzu-Yanzu: Bayan aiko da wakilanta suka ganewa idanunsu abinda ke faruwa a Najeriya, kasar Amurka tace lallai gaba dayan ‘yan Najeriya ne ya kamata a samarwa da tsaro

Duk Labarai
Dan majalisar kasar Amurka, Riley Moore wanda Shugaban kasar, Donald Trump ya wakilta ya zo Najeriya yaga yanda ake Mhuzghunawa Kiristoci kamar yanda suke zargi. Bayan ziyarar tasa yace a yanzu 'yan Najeriya gaba daya ne ya kamata a samarwa da tsaro. Saidai yace duk da haka sun fi damuwa da samarwa Kiristoci tsaro. Yace ya ji dadin yanda Najeriya ta amince zata yi aiki da kasar Amurka dan samarwa kasar tsaro amma ba a baki kawai abin ya kamata ya kasance ba. Kamata yayi a tabbatar da abubuwan da aka tattauna a aikace.