Sunday, December 21
Shadow
Da Duminsa: Kasar Jamhuriyar Nijar tace daga yanzu duk wasu kaya da za’a shigar musu dasu daga Najeriya sai an musu daidai a ga komenene a iyaka kamin a barsu su wuce

Da Duminsa: Kasar Jamhuriyar Nijar tace daga yanzu duk wasu kaya da za’a shigar musu dasu daga Najeriya sai an musu daidai a ga komenene a iyaka kamin a barsu su wuce

Duk Labarai
Kasar Nijar ta fitar da sabuwar doka wadda tace daga yanzu duk wani abu da za'a shigar mata dashi dana Najeriya sai an masa daidai an ga komenene a ciki kamin a barshi ya wuce. Nijar din ta fitar da wannan sabuwar sanarwar ne bayan da Najeriya ta dakile yunkurin juyin mulkin a kasar Benin Republic. Hakanan sanarwar na zuwane bayan da kasar Burkina Faso ta rike jirgin saman Najeriya da sojoji 11 da suka shigar mata sararin samaniyar ta ba bisa ka'ida ba.
Duk da Allah wadan da aka yi akan Bidiyon farko, Tauraron fina-finan Hausa, Shalele ya sake yin Bidiyo Manne da Abokiyarsa

Duk da Allah wadan da aka yi akan Bidiyon farko, Tauraron fina-finan Hausa, Shalele ya sake yin Bidiyo Manne da Abokiyarsa

Duk Labarai
A jiya ne dai Bidiyon Tauraron fina-finan Hausa, Shalele ya dauki hankula bayan da aka ganshi manne jikin wata yarinya. Ba 'yan kallo kadai ba, hadda wasu daga cikin abokan kasuwancinsa sun yi Allah wadai da wannan Bidiyon. Saidai a yau ma an sake tashi da wani Bidiyonsa tare da da Budurwar da suka yi Bidiyon farko. https://www.tiktok.com/@yardaraja0/video/7581618452272663826?_t=ZS-924cfDDga1Z&_r=1
Da Duminsa: EFCC sun sake kama Tsohon Ministan shari’a, Abubakar Malami

Da Duminsa: EFCC sun sake kama Tsohon Ministan shari’a, Abubakar Malami

Duk Labarai
Rahotanni daga Abuja na cewa hukumar yaki da rashawa da cin hanci, EFCC sun sake kama tsohon Ministan shari'a, Abubakar Malami. Sahara Reporters sun ruwaito cewa EFCC sun kama Abubakar Malami ne da yammacin jiya, Latinin. Sannan yanzu haka yana ta kokarin ganin ya samu manyan sakatarorin gwamnati 2 ne da zasu tsaya masa a bayar da belinsa. Ana zargin Malami ne da aikata ba daidai ba da kudaden da aka kwato na tsohon shugaban kasa, Marigayi janar Sani Abacha. Zargin da Malami ya dade da karyatawa.
Kalli Bidiyon: Brekete Family ta wallafa Hoton Malam Nura wanda ake zargi da yiwa yara 9 Lìywàdhì a Abuja

Kalli Bidiyon: Brekete Family ta wallafa Hoton Malam Nura wanda ake zargi da yiwa yara 9 Lìywàdhì a Abuja

Duk Labarai
Kafar Brekete Family ta wallafa Hoton Malam Nura da ake zargi da yiwa yara 9 lùwàdì a Abuja. Sannan an kira mahaifinsa inda yace an kara gishiri a labarin da matan ke bayarwa. Mahaifin nasa yace da aka fara zargin dansa, da kansa ya daukoshi ya mikawa hukuma amma gashi yanzu ana masa karyar wai shi ya koyawa da nasa yin Luwadin. Sannan ba kamar yanda aka watsa a baya ba, cewa, 'yansanda sun saki Nura, Ordinary President ya ce sun samu rahoton cewa Nura na gidan yari. https://www.tiktok.com/@minuwa365/video/7581583938397719815?_t=ZS-924X1Aqw1T7&_r=1 https://www.tiktok.com/@minuwa365/video/7581736713567915271?_t=ZS-924Xt54qRl2&_r=1
Kalli Bidiyon: Bayan “wulakancin” Matar Shugaban kasa, Remi Tinubu tawa Gwamnan Jihar Osun, An kuma ga abinda tawa matar tsohon shugaban kasa, Patience Jonathan wanda wasu ke cewa yama fi abinda tawa Gwamnan Osun Muni

A jiyane aka ga yanda matar shugaban kasa, Remi Tinubu ta cewa gwamnan jihar Osun ta bashi minti 5 ya kammala jawabin da yake inda tace ya kauce ya basu guri ya ishesu da wakoki. Saidai a wajan taron dai, an kuma ji abinda matar shugaban kasar ta cewa matar tsohon shugaban kasa, Dame Patience Jonathan. Matar shugaban kasar ta kira Patience Jonathan da Mama p, Kin yi murmushi kuwa? Wasu dai sunce wannan magana bata dace ba inda wasu ke ganin hakan ba wani abu bane. https://twitter.com/warrisentinel/status/1997985889624932777?t=tlkvFjjdiXNQ6evFdNW-Sw&s=19
Bidiyon yanda wasu ke hada manja a kudu ta hanyar kara masa kala dan yayi jaa sosai ya jawo cece-kuce sosai a kafafen sadarwa

Bidiyon yanda wasu ke hada manja a kudu ta hanyar kara masa kala dan yayi jaa sosai ya jawo cece-kuce sosai a kafafen sadarwa

Duk Labarai
Wani Bidiyo da ya nuna yanda wasu ke hada manja ta hanyar kara masa kala dan yayi jaa sosai a kudancin Najeriya ya jawo cece-kuce sosai. Bidiyon ya dagawa mutane hankali sosai inda aka rika kiran gwamnati ta dauki mataki kan lamarin. An yi kira ga hukumar NAFDAC da su tsaurara bincike kan lamarin dan daukar matakan da suka dace. https://twitter.com/MobilePunch/status/1998005924200325415?t=hoDbM7E6PQ3WTPmxAzeUFQ&s=19
Kalli Bidiyon: Akwai ‘ya’yan Itatuwa irin na gidan Aljannah a gidana>>Inji Gfresh Al-amin

Kalli Bidiyon: Akwai ‘ya’yan Itatuwa irin na gidan Aljannah a gidana>>Inji Gfresh Al-amin

Duk Labarai
Tauraron Tiktok, Gfresh Al-amin ya bayyana cewa, akwai 'ya'yan Itatuwa irin na gidan Aljannah a gidansa. Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi bayan aurensa inda yake bayyana irin katan alatun dake gidansa. Ya bayyana cewa akwai kwanciyar hankali a gidansa. Gfresh ya bayyana cewa kuma ya gayawa matarsa irin sana'arsa kuma ta amince. https://www.tiktok.com/@sarkidonamanarmatch/video/7581616655982169400?_t=ZS-924TqGMqD2X&_r=1
Kalli Bidiyon yanda wani dan Najeriya ya koma Kango da zama bayan da kudadensa da ya zuba a harkar Forex suka lalace

Kalli Bidiyon yanda wani dan Najeriya ya koma Kango da zama bayan da kudadensa da ya zuba a harkar Forex suka lalace

Duk Labarai
Wannan wani dan Najeriya ne da ya koma Kango da zama bayan da kudaden da ya zuba a harkar Forex suka lalace. An ga Bidiyon yanda dakin da yake ciki ruwa ya maye shi. Da yawa sun tausayawa yanayin da yake ciki. Rahotanni sun ce kudaden da ya tafka Asara sun ka Naira Miliyan 20 a harkar Forex din. https://twitter.com/GossipMillNaija/status/1997996254102769671?t=pIYjJKBnujDppaRejHKfTQ&s=19
Har yanzu dai Jirgin sojojin Najeriya da sojoji 11 na hannun kasar Burkina Faso

Har yanzu dai Jirgin sojojin Najeriya da sojoji 11 na hannun kasar Burkina Faso

Duk Labarai
Zuwa safiyar yau babu wani karin bayani game da Jirgin sama na sojojin Najeriya C-130 da sojoji 11 da kasar Burkina Faso ta kama. A daren jiya ne dai Kasar ta Burkuna Faso ya sanar da kama jirgin da sojonin bayan da suka shiga sararin samaniyar kasar ba da izini ba. Hukumomin kasar dai sun ce suna kan bincikene. Sannan sun yi gargadin cewa duk wani Sabon Jirgin da ya kara ketawa ta sararin samaniyar su ba da izini ba kakkboshi zasu yi ba wata kakkautawa.
Zuwan wakilin kasar Amurka jihar Benue kadai ya jawo cece-kuce

Zuwan wakilin kasar Amurka jihar Benue kadai ya jawo cece-kuce

Duk Labarai
Rashin zuwa wakilin da kasar Amurka ta turo zuwa Najeriya dan ya duba abinda suke zargi na Khisan Kyiyashi da suka ce anawa Kiristoci zuwa sauran jihohin Najeriya dake fama da matsalar tsaro ya jawo cece-kuce. Riley Moore wanda dan majalisar kasar Amurka ne kuma me karfin riko da Kiristoci ne Trump ya wakilta ya masa bincike kan lamarin. Kuma ya zo ya gana da wakilan Kiristoci a jihar Benue amma ba'a ganshi yana ganawa da bangaren musulmai ba, sannan ba'a ganshi a jihohin Inyamurai ba kuma ba'a ganshi a jihar Filato ba inda nan ma ana da matsalolin tsaron. Saidai wannan bai zowa mutane da mamaki ba lura da cewa, dama can Amurkar tace Khisan Kyiyashi da akewa Kiristoci ne take son hanawa. Duk da cewa bayan kammala ziyarar tasa, Riley Moore yace akwai bukatar samarwa duka 'yan ...