PDP na shirin baiwa Tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan takarar shugaban kasa a shekarar 2027, ji bayani
Wani batu da ke jan hankali a siyasar Najeriya shi ne yadda bayanai ke cewa babbar Jam'iyyar adawa ta PDP ta na lallaɓa tsohon shugaban ƙasar GoodLuck Jonathan domin ba shi tikitin takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027
Mista Jonathan ya ja baya a harkokin siyasa tun da ya fadi zabe a 2015, kuma jam'iyyar PDP ta tabbatar da cewa tana tattaunawa da shi domin ya yi mata takarar shugaban ƙasa don kalubalanar shugaba Bola Tinubu a zaɓe mai zuwa.
Wasu masana na ganin cewa wannan mataki ne na gurgunta tafiyar haɗakar wasu manyan yan'awar ƙasar.
Majiyoyin sun shaida wa BBC cewa jam'iyyar ta PDP a hukumance, da kuma a matakin wasu jiga jigan ta, ciki har da gwamnoni ne ke wannan yunkuri na zawarto tsohon shugaban Najeriyar Good Luck Ebele Jonathan dominn ba shi takara a jama'iyyar a zaben 202...








