Thursday, March 5
Shadow
Serap ta ba wa gwamnan Neja wa’adin janye umarnin rufe rediyon Badeggi FM

Serap ta ba wa gwamnan Neja wa’adin janye umarnin rufe rediyon Badeggi FM

Duk Labarai
Ƙungiyar neman shugabanci na gari ta Serap ta bai wa gwamnan jihar Neja da ke arewacin Najeriya wa'adin awa 48 domin ya janye umarnin rufe gidan rediyon Badeggi FM ko kuma ya fuskanci matakin shari'a. Cikin wata wasiƙa da ƙungiyar ta aika wa Gwamna Umaru Bago, shugaban Serap Kolawole Oluwadare ya ce rufe gidan rediyon da ke birnin Minna "saɓa wa doka" ne, kuma ya nemi gwamnan ya mayar musu da lasisinsu. "Toshe bakin masu suka da sunan tsaron ƙasa keta rantsuwar kama aiki da ka yi ne da kuma ɓata sunan Najeriya a idon duniya game da haƙƙin ɗan'adam," a cewar wasiƙar. A ranar Juma'a ne Gwamna Bago ya bayar da umarnin rufe gidan rediyon na Badeggi FM nan take tare da ƙwace lasisinsa saboda zargin "tayar da fitina".
Kalli Bidiyo: Abin takaici ne yanda aka baiwa ‘yan mata ‘yan kwallon Najeriya kyautar Naira Miliyan 160, kudin da har soja ya gama aikinsa in za’a hada duka abinda zai samu ba zai kai hakan ba>>Soja ya koka

Kalli Bidiyo: Abin takaici ne yanda aka baiwa ‘yan mata ‘yan kwallon Najeriya kyautar Naira Miliyan 160, kudin da har soja ya gama aikinsa in za’a hada duka abinda zai samu ba zai kai hakan ba>>Soja ya koka

Duk Labarai
Sojan Najeriya ya koka bisa yanda aka baiwa 'yan mata 'yan kwallon Najeriya kyautar Miliyoyin kudade da gidaje bayan sun lashe kofij gasar kwallon mata ta Afrika. Sojan yace duka aikin da suka yi bai wuce na watanni 3 ba. Yace amma abin takaici shine kudaden da aka basu tun daga randa aka dauki soja aiki har ya gama aikinsa ba zai samu irin wadannan kudaden ba. https://twitter.com/ChuksEricE/status/1951970780218060823?t=T8tOwYdS5fcx3MI5pgmKZQ&s=19
Gwamnati za ta gyara tsarin birnin Maiduguri domin kare ambaliya

Gwamnati za ta gyara tsarin birnin Maiduguri domin kare ambaliya

Duk Labarai
Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya ce gwamnatinsa ta fara yunƙurin gyara tsarin birnin jihar domin kiyaye jihar daga ambaliya. Zulum ya bayyana haka ne jim kaɗan bayan ziyarar gani da ido da ya yi wajen gyara da ake yi a dam ɗin Alau, inda ya ce har yanzu akwai wasu da suke gini a magudanan ruwa da kuma masu zuba shara suna toshe magudunan ruwa. "Za mu duba tare da gyara tsarin birnin Maiduguri domin mu tabbatar dukkan magudanan ruwanmu a buɗe suke kuma suna aiki," in ji shi kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito. Ya yi gargaɗin cewa duk wani gini da aka yi a magudunan ruwa za a rushe su. Ya ce za su ɗauki matakin rusau ɗin ne domin kare sake aukuwar irin ambaliya da ta auku a ranar 10 ga watan Satumban 2024 a Jere da ke Maiduguri. A game da fargabar d...
Ku zabeni, na yi Alkawarin wa’adi daya kawai zan yi in sauka>>Peter Obi

Ku zabeni, na yi Alkawarin wa’adi daya kawai zan yi in sauka>>Peter Obi

Duk Labarai
Tsohon ɗan takarar shugabancin Najeriya a jam'iyyar Labour, Peter Obi ya ce idan ya samu nasarar zama shugaban ƙasar, wa'adi ɗaya na shekara huɗu kawai zai yi kamar yadda ya yi alƙawari. Obi ya bayyana haka ne a shafinsa na X, inda ya ce ko tsohon shugaban Amurka, Abraham Lincoln wa'adi ɗaya ya yi na shekara huɗu, "sannan John F. Kennedy bai ma ƙarasa wa'adi ɗaya ba, amma ana cigaba da tunawa da su a matsayin shugabanni masu adalci." Ya ce ko a Afirka, Nelson Mandela ya zama abin koyi a duniya wajen shugabanci na adalci, "amma wa'adi ɗaya kawai ya yi." "Ba daɗewa a ofis ba ne ke alamta nasara, irin ayyukan da shugaba ya yi ne za a riƙa tunawa. Saboda haka ne nake sake nanata alƙawarin da na yi cewa wa'adi ɗaya na shekara huɗu kawai zan yi idan na zama shugaban Najeriya," in ji shi...
ABIN A YABA: Ya Tara Marayu Sama Da 200 Ya Yi Bikin Zagayowar Ranar Haihuwarsa Tare Da Su, Inda Ya Yi Wa Kowannensu Dinki

ABIN A YABA: Ya Tara Marayu Sama Da 200 Ya Yi Bikin Zagayowar Ranar Haihuwarsa Tare Da Su, Inda Ya Yi Wa Kowannensu Dinki

Duk Labarai
ABIN A YABA: Ya Tara Marayu Sama Da 200 Ya Yi Bikin Zagayowar Ranar Haihuwarsa Tare Da Su, Inda Ya Yi Wa Kowannensu Dinki …samun matashi irin Hon. Muhammad Sulai Yaro abu ne mai wuya Tabbas samun matashi kamar Hon Muhammed Sulai Yaro wanda aka nada shi a matsayin Dan Gatan Girei abu ne da kamar wuya, matashi ne da ya mayar da hankalin sa kan takalawa. A jiya ne dai ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar sa, inda ya debi yara marayu sama da dari biyu ya yi musu sabon dinki, kuma ya hada musu liyafa, har saida ya zubar da hawaye a wajen. Haka kuma ya yi musu alkawari zai ci gaba da tallafa musu har karshen rayuwar su. Wace fata za ku yi masa? Daga Hon Ishaq B Aliyu
Wata Sabuwa: Akwai yiyuwar Shugaba Tinubu zai dakko Matthew Hassan Kuka ko Yakubu Dogara ya mai mataimaki a 2027

Wata Sabuwa: Akwai yiyuwar Shugaba Tinubu zai dakko Matthew Hassan Kuka ko Yakubu Dogara ya mai mataimaki a 2027

Duk Labarai
Dan Gwagwarmaya, Mahadi Shehu ya bayyana mutanen da yake tsammanin zasu yi takara a zaben shekarar 2027 da abokan takararsu. Ya rubuta hakane a shafinsa na X inda ya bayyana 'yan takarar da yake tsammanin zasu yi takara a kowacw jam'iyya. A jam'iyyar APC yace akwai yiyuwar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai yi takara da tsohon gwamnan jihar Borno, Modu Ali Sheriff, ko Yakubu Dogara, ko babban Fasto, Mathew Hassan Kuka. A jam'iyyar ADC kuwa, yace akwai yiyuwar Atiku Abubakar da Rotimi Amaechi ne zasu yi takara a 2027. A Labour Party kuwa yace Peter Obi da Ko dai tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai, Datti Baba Ahmad, ko Aminu Waziri Tambuwal. A PDP kuwa yace akwai yiyuwar, Goodluck Jonathan su yi takara tare da Gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ko ya dau...
Ku daure ku sake zaben Tinubu a 2027 ko dan ya kammala ayyukan ci gaban da ya faro a Arewa>>Femi Gbajabiamila shugaban ma’aikatan fadar Tinubu ya roki ‘yan Arewa

Ku daure ku sake zaben Tinubu a 2027 ko dan ya kammala ayyukan ci gaban da ya faro a Arewa>>Femi Gbajabiamila shugaban ma’aikatan fadar Tinubu ya roki ‘yan Arewa

Duk Labarai
Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila ya roki 'yan arewa da su sake zaben shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a zaben 2027. Yayi wannan rokone a yayin wani taro da ya shirya na tsaffin 'yan majalisar tarayya a Abuja. Ya bayyana cewa, Shugaba Tinubu Tinibu ba shugaban kudancin Najeriya bane kadai, shugaba ne na kowanne yanki. Yace ko dan Tinubu ya kammala ayyukan ci gaban da ya ke yi a Arewa, ya kamata ace 'yan Arewan su sake zabensa.