Mummunar Zanga-zangar kin jinin Korar Baki da shugaba Trump yake yi a kasar Amurka ta barke
Zanga-zangar adawa da korar baki ta barke a kasar Amurka, musamman birnin Los Angeles.
Zanga-zangar ta fara ne bayan da hukumar ICE wadda itace ke kula da shige da fici ta kasar ta kama wasu mutane 'yan cirani 118 wanda cikinsu akwai 'yan daba.
Zanga-zangar ta barke sosai inda aka rika lalata motoci ana konawa hadda na jami'an tsaro ana yanka musu tayoyin mota.
Lamarin ya kazance inda aka fara shiga shagunan mutane ana musu sata.
Sannan an lalata gine-ginen Gwamnati.
https://twitter.com/nicksortor/status/1931436052415123859?t=GsqUQ-rFdENP8iuJhFIsoQ&s=19
https://twitter.com/nicksortor/status/1931960574801314219?t=UywvL5SCigykvd9TT9zFUA&s=19
Shugaba Trump ya aika da jami'an tsaro da ake kira da National Guard zuwa Birnin na Los Angeles inda ya zargin Gwamna ...








