Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya ce bai amince a kashe Shugaban Iran ba
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana cewa, bai amince da aniyar kasar Israyla ta kashe shugaban juyin Juyahlin kasar Iran Atayollah Khumaini ba.
Israyla tana son ta kashe Shugaban Iran dinne saboda a lissafinta idan ta kasheshi shine za'a kawo karshen shirin Mallakar makamin kare dangi na kasar.
Saidai shi Trump a cewarsa, bai yadda da wannan mataki ba inda yace sulhu yafi baiwa muhimmanci.








