Sarki Sanusi ya umarci hakimai da su shigo cikin Kano domin hawan Babbar Sallah
Sarki Sanusi ya umarci hakimai da su shigo cikin Kano domin hawan Babbar Sallah.
Majalisar Masarautar Kano ta fitar da wata takarda mai dauke da umarni ga dukkan Hakimai da 'Yan Majalisa na masarautar da su hallara a Birnin Kano domin halartar bikin hawan Babbar Sallah da za a gudanar cikin makon gobe.
A wata takardar sanarwa da Sakataren Majalisar Masarautar Kano, Alhaji Abba Yusuf Danmakwayon Kano ya rattabawa hannu, an bukaci Hakimai da sauran shugabannin gargajiya da su iso Kano tare da dawakan su da mahayan su a ranar Laraba, 8 ga Dhul Hijjah, 1446 Hijira, wanda ya yi daidai da 4 ga Yuni, 2025.
Bayan haka, ana sa ran za su halarci Fadar Mai Martaba Sarkin Kano a ranar Alhamis, 9 ga Dhul Hijjah, wato 5 ga Yuni, 2025 da misalin karfe 11:00 na safe, domin karbar umarni da ba...








