Monday, December 15
Shadow
Zulum ya bai wa iyalan sojojin da aka kàshè tallafin miliyan 100

Zulum ya bai wa iyalan sojojin da aka kàshè tallafin miliyan 100

Duk Labarai
Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai wa iyalan sojijin da aka kashe da kuma waɗanda aka jikkata a fagen daga a yaƙi da ƴan ta da ƙayar-baya a arewa maso gabas, tallafin naira miliyan 100. Gwamnan ya bayar da tallafin ne ranar Asabar yayin liyafar cin abinci a daidai lokacin da ake ci gaba da bukukuwan sallah, inda babban hafsan sojin ƙasa Laftanar-Janar Olufemi Oluyede da babban hafsan sojin sama, Air Marshal Hassan Abubakar suka halarci liyafar a barikin sojoji na Maimalari a Maiduguri. Zulum ya gabatar da chekin kuɗin na naira miliyan 100 ga hannun kwamandan dakarun Haɗin-Kai, Manjo-janar Abdussalam Abubakar. Ya bayyana cewa kowane soja da aka raunata a fagen daga zai samu naira 500,000, yayin da za a raba sauran kuɗin ga iyalan sojojin da aka kashe. Gwamna Zulu...
Gwamnan Benue ya tona Asirin masu daukar nauyin hàrè-hàrèn ‘yan tà’àddà

Gwamnan Benue ya tona Asirin masu daukar nauyin hàrè-hàrèn ‘yan tà’àddà

Duk Labarai
Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, ya zargi wasu ƴan siyasa da ke ci a majalisar tarayya da ɗaukar nauyin hare-hare da ake kai wa jihar, inda ya ce ba za su lamunci hakan ba. Gwamnan ya yi wannan zargi ne yayin tattaunawa a shirin 'Politics Today' na gidan talabijin na Channels. Duk da cewa bai bayyana sunayen ƴan siyasar ba, gwamnan ya ce kwamitin da ya naɗa domin yin binciken kan batun kai hare-haren ya gano akwai sunayen manyan ƴan siyasa, inda ya sha alwashin ɗaukar mataki nan take idan ya karɓi rahoton kwamitin a mako mai zuwa. "Abin takaici yadda wasu manyan ƴan siyasa ke ci gaba da bai wa ƴan bindigar da ke kai hare-haren mafaka da kuma saya musu makamai. Za mu ɗauki mataki tun da ba su damu da irin rayuka da suke salwantar wa ba," in ji gwamna Alia. Jihar ta Benue...
Mun kaiwa masu ikirarin Jìhàdì mummunan hàrì>>Sojojin Najeriya

Mun kaiwa masu ikirarin Jìhàdì mummunan hàrì>>Sojojin Najeriya

Duk Labarai
Sojojin Najeriya sun bayyana cewa, Sun kaiwa Masu ikirarin Jìhàdì mummunan hari ta jirgin sama a kauyen Talala da kauyen Ajigin dake yankin Timbuktu a jihar Borno. Hukumar sojojin tace ta lalata kayan amfanin maharan da yawa. An kai harinne ranar Asabar, 7 ga watan Mayu da misalin karfe 5:30 p.m. Hukumar tace ta kai harinne bayan samun bayanai cewa mayakan masu ikirarin Jihadi na taruwa dan kaiwa sojoji hari. Hukumar tace harin ya tarwatsa maharan inda da yawa suka jikkata kuma shirinsu ya lalace. Hukumar ta yi gargadin cewa, wannan gargadi ne cewa ko a inane makiyansu suke zasu kai musu hari su tarwatsa su.
‘Yan Bìndìgà sun sake kai mummunan hàrì a jihar Arewa

‘Yan Bìndìgà sun sake kai mummunan hàrì a jihar Arewa

Duk Labarai
'Yan Bindiga akalla 10 sun kai mummunan hari wani kauye me suna Chito dake karamar hukumar Ukum ta jihar Benue ranar Asabar. Maharan sun kai harinne da misalin karfe 2:26 am inda suka shafe awanni 2 da mintuna 30 suna aikata masha'a. Ance sun daki mutane da dama sannan suka saci kayan sawa da abinci da sauransu. Daya daga cikin wadanda abin ya shafa, Dr. Isaac H. Mamkaa wanda malamine a kwalejin ilimi ta Katsina Ala ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace 'yan Bindigar sun ce zasu sake komawa su kai musu hari garin.
Ba dan kìyàyyà ga wasu mutanene yasa aka yi yàkìn basasa ba>>Inji Tsohon Shugaban kasa, Yakubu Gowon

Ba dan kìyàyyà ga wasu mutanene yasa aka yi yàkìn basasa ba>>Inji Tsohon Shugaban kasa, Yakubu Gowon

Duk Labarai
Tsohon shugaban kasa na mulkin Soja, Janar Yakubu Gowon ya bayyana cewa, ba dan kiyayya ga wasu mutanene yasa aka yi yakin basasa ba a Najeriya. Ya bayyana hakane ranar Asabar a Abuja inda yace dalilai na neman hadin kan kasa ne suka sa dole suka fito aka yi yakin basasa dasu. Yakubu Gowon ya bayyana muhimmancin yafiya, da sasanci da hadin kai. Ya bayyana cewa, ya tuna da lokaci mafi wahala a rayuwarsa, watau lokacin yakin basasa, inda yace abu ne da bashi da zabi akansa, kuma yayi abinda ya kamata dan ganin an hada kan kasarnan. Janar Yakubu Gowon dan shekaru 91 yace shima yayi asara a yakin basasa dan kuwa a yakin basasa ne ya rasa babban abokinsa, Major Arthur Unegbe.
A yayin da Kungiyar Dattawan Yarbawa ta Afenifere take kiran a tsige Shugaba Tinubu saboda bai tsinanawa ‘yan Najeriya komai ba, Kungiyar Matasan Yarbawan sun ce basu yadda a tsige shugaban ba

A yayin da Kungiyar Dattawan Yarbawa ta Afenifere take kiran a tsige Shugaba Tinubu saboda bai tsinanawa ‘yan Najeriya komai ba, Kungiyar Matasan Yarbawan sun ce basu yadda a tsige shugaban ba

Duk Labarai
Kungiyar Matasan Yarbawa, (YYSA) tace bata amince da kiran da kungiyar dattawan Yarbawan ta yi ba na cewa a tsige shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu saboda yaudarar 'yan Najeriya. Shugaban kungiyar, Olalekan Hammed ne ya fitar da sanarwar ranar Lahadi inda yace zargin da akewa shugaba Tinubu na baiwa kamfanin Mr. Gilbert Chagoury aikin gina titin Legas zuwa Calabar wanda ke da alaka dashi ba gaskiya bane. Yace kamfanin na da tarihin yin ayyuka masu kyau. Yace kiran a tsige shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu cike yake da siyasa sannan zargin da ake masa bashi da tushe ballantana makama. Sannan yacw shi Tinubu yana duba cancanta ne kamin ya bayar da aiki.
Mutane 9 sun rasu sanadiyyar hadarin mota a jihar Jigawa

Mutane 9 sun rasu sanadiyyar hadarin mota a jihar Jigawa

Duk Labarai
A kalla Mutane 9 ne suka rasu a hadarin mota da ya faru a kauyen Kyaramma dake karamar hukumar Ringim ta jihar Jigawa. Hukumar 'yansandan jihar ta tabbatar da faruwar hadarin inda tace ya farune da misalin karfe 2 na yamma tsakanin wasu motocin Golf 3 guda biyu wanda kuma ya bar mutane da yawa sun jikkata. Kakakin 'yansandan jihar, Shiisu Adam ne ya bayyana hakan inda yace motocin sun yi taho mu gama, yace bayan hadarin 'yansandan sun kai dauki wajan inda suka kai wadanda suka jikkata Asibiti. Kwamishinan 'yansandan jihar, CP A.T. Abdullahi, ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan mamatan inda yace direbobi su rika kiyaye dokokin hanya dan gujewa hadarin.
Kalli yanda Wani Bayerabe yayi tsalle ya fada Rijiya bayan da ya sha kwaya ranar Sallah Saboda murna

Kalli yanda Wani Bayerabe yayi tsalle ya fada Rijiya bayan da ya sha kwaya ranar Sallah Saboda murna

Duk Labarai
Wani bayerabe ya fada rijiya a garin Ilorin West na jihar Kwara bayan da ya sha kwaya da ake cewa Colorado. Ya sha kwayar ne ranar Sallar, watau Juma'ar data gabata inda tasashi ya haukashe ya tuma ya fada Rijiyar. Sunan mutumin Kareem dan shekaru 43. Hukumar kwana-kwana ta jihar ta bayyana cewa, an kirata aka sanar da ita lamarin da misalin karfe 10:29 na safe, kamar yanda kakakin hukumar, Hassan Adekunle ya bayyana. Yace da suka je sun fitar da gawar mutumin inda suka mikata hannun 'yansanda.
Allah ya gayamin idan na bar cocin RCCG dana na farko zai mùtù>>Inji Fasto Enoch Adeboye

Allah ya gayamin idan na bar cocin RCCG dana na farko zai mùtù>>Inji Fasto Enoch Adeboye

Duk Labarai
Babban Faston cocin RCCG, fasto Enoch Adeboye ya bayyana cewa, Allah ya taba gargadinsa cewa idan ya bar cocin RCCG din dansa na farko zai mutu. Faston ya bayyana hakane a wajan wani taron addu'a da aka yi a cocinsa ta RCCG din dake Ogun ranar 7 ga watan Yuni. Faston ya bayyana damuwa sosai kan yanda wasu kiristoci ke tsalle daga wannan coci zuwa wancan coci. Inda yace shi kam Allah ne ya hanashi canja coci dan ya gargadeshi idan ya canja, dansa na fari zai mutum.