Kaf masu neman takarar shugabancin Najeriya babu Gwani wanda ya cancanta kamar ni>>Inji Peter Obi
Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar Labour party a zaben shekarar 2027, Peter Obi ya bayyana cewa, babu Dimokradiyya a mulkin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
Ya bayyana cewa idan aka lura da abinda ya faru a jihar Rivers da zaben jihar Edo za'a iya gane cewa, babu Dimokradiyya a Najeriya.
Peter Obi ya bayyana hakane a wata ganawa da aka yi dashi a Arise TV.
Yace shiyasa yake ta neman ya zama shugaban kasa, saboda ya gyara wannan matsalar, yace a kaf cikin masu neman takarar shugaban kasar, babu gwani wanda ke da kwarewa kamarsa saboda yayi aiki da kamfanoni kuma ya zama gwamna.








