Mun samu nasara sosai akan tshageran Dhaji amma kalaman Shugaban Amurka, Trump ya sa suka samu karfin Gwiwar dadowa har suka dauke daliban jihar Kebbi>>Inji Gwamnatin tarayya
Gwamnatin tarayya ta bayyana rashin jin dadi kan kalaman shugaban kasar Amurka, Donald Trump na cewa zai kawowa Najeriya hari.
Gwamnatin tace wadannan kalaman ne suka karfafa 'yan ta'dda har suka dawo suka kai hari makarantar 'yan mata ta jihar Kebbi.
Sakataren Gwamnatin tarayya, George Akume ne ya bayyana hakan ranar Laraba.
Yace sun samu nasara sosai akan 'yan Bindigar amma kalaman na Trump yasa suka dawo har suke samun kara fadada ayyukansu.
Yace sojojin Najeriya na da kwarewa kuma a baya sun samu nasara sosai akan tsageran dajin dan sun kwato wasu garuruwa dake hannun tsageran dajin.
Yace abinda Najeriya ke bukata ba wai wata kasa ta shigo ta yaki 'yan ta'adda ba, tana neman hadin gwiwa ne ta hanyar bayanan sirri da makamai da sauran su musamman daga kasashe irin su Amur...








