Saturday, December 20
Shadow
Zamu Wallafa Bayanan sirri da muka samo daga kasar Israyla ta hanyar kutse ga duniya kowa ya gani>>Kasar Ìràn

Zamu Wallafa Bayanan sirri da muka samo daga kasar Israyla ta hanyar kutse ga duniya kowa ya gani>>Kasar Ìràn

Duk Labarai
Kasar Iran ta bayyana cewa, zata wallafawa Duniya bayanan sirrin da ta samo daga kasar Israyla ta hanyar kutsen data mata. Kasar Iran tace ta samu bayanan sirri ciki hadda na makaman kare dangi na kasar Israela bayan data biya wasu 'yan kasar makudan kudade suka samo mata bayanan. Kasar Israyla a baya itama ta yiwa kasar Iran irin wannan kutse daga baya ta kuma wallafawa kowa Duniya ta gani. Dan haka a yanzu zamu iya cewa, kasar Iran ramako ne kate yi.
Ana zargin Ministan Shari’a da cire sunan Shugabar bankin Fidelity Bank daga zargin Almundahana duk da shaida karara

Ana zargin Ministan Shari’a da cire sunan Shugabar bankin Fidelity Bank daga zargin Almundahana duk da shaida karara

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnatin tarayya ta cire sunan shugabar bankin Fidelity Dr. Nneka C. Onyeali-Ikpe daga sunayen mutanen da take bincika. Babban Lauyan Najeriya, kuma Ministan shari'a, Lateef Fagbemi (SAN) ne ya fara bincikenta a baya bisa zargin damfara da Almundahana. Wasu daga cikin zarge-zargen da ake mata shine amfani da kudin bankin wajan sayen hannun Jari na miliyoyin Naira. Saidai gashi yanzu da Alama Gwamnatin ta yafe mata.
Gòbàrà ta làlàtà dukiya a kasuwar Kara a Birnin Kebbi

Gòbàrà ta làlàtà dukiya a kasuwar Kara a Birnin Kebbi

Duk Labarai
Wata mummunar gobara da tashi a kasuwar Kara a Birnin Kebbi, ta lalata shaguna da kuma dukiyoyi da dama. Gobarar wadda ta soma a safiyar yau Lahadi, ta janyo asarar kayayyaki da kuɗinsu ya kai na miliyoyin naira. Wasu shaidu sun bayyana cewa wutar ta yaɗu da sauri kafin a samu zuwan masu kashe gobara, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito. "Mun ga hayaki na tashi ko ta ina, nan da nan wutar ta karaɗe yawancin shaguna da ke cikin wannan kasuwa," in ji wani ɗan kasuwa mai suna Musa Bello. Ba a samu rahoton asarar rai ba a gobarar, sannan zuwa yanzu ba a san abin da ya haddasa ta ba. Gwamnatin jihar Kebbi ta jajantawa waɗanda lamarin ya shafa a wata sanarwa da ta fitar. Ta nuna takaicinta kan afkuwar lamarin.
Gwamnatin jihar Kano ta nemi gwamnatin Tarayya ta biyata diyya saboda hana hawan sallah tsawon shekaru 2

Gwamnatin jihar Kano ta nemi gwamnatin Tarayya ta biyata diyya saboda hana hawan sallah tsawon shekaru 2

Duk Labarai
Gwamnatin jihar Kano ta nemi Gwamnatin tarayya ta biyata diyya saboda hana hawan Sallah na tsawon shekaru 2. Kwamishinan kananan hukumomi da sarautun gargajiya, Alhaji Tajo Uthman ya bayyana haka a yayin da me martaba, sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya kaiwa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf Ziyara a gidan Gwamnatin Jihar. Ya bayyana cewa, wannan hani yasa sun tafka babbar asara saboda mutane daga ciki da wajen Najeriya na zuwa kallon hawan Sallar. Ya bayyana cewa, Har majalisar Dinkin Duniya ta san da zaman hawan Sallar a Kano kuma rashin kudin da suke samu daga hawan Sallar ya taba kasafin kudin jihar. Ya bayyana cewa, Dan haka gwamnatin tarayya ta biya musu kudaden da suka rasa na hawan Sallah.
Kalli Bidiyo: Bahaushiya dake zaune a kasar Ingila amma Bazawara ce na neman Mijin Aure daga Najeriya

Kalli Bidiyo: Bahaushiya dake zaune a kasar Ingila amma Bazawara ce na neman Mijin Aure daga Najeriya

Duk Labarai
Wata Bahaushiya me shekaru 33 wadda bazawarace tana zaune a kasar Ingila, tace tana neman mijin aure har daga Najeriya. Ga wanda ke so zai iya yin magana a kasan wannan Bidiyon ko ya aikawa matar me jawabi da lambar wayars. https://twitter.com/Hadeezaasabo/status/1931632926082396506?t=l3O5Uf9nXitwYOW1f6nGYA&s=19 Da yawa dai sun bayyana suna da ra'ayi amma kana iya gwada sa'arka.
Matawalle ya yi wa Dauda Lawal tayin shiga APC

Matawalle ya yi wa Dauda Lawal tayin shiga APC

Duk Labarai
Karamin ministan tsaron Najeriya, Bello Matawalle ya yi wa gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal tayin shiga jam'iyyar APC mai mulki. Ministan ya yi tayin ne ranar Asabar a garin mahaifarsa ta Maradun, lokacin da ya karɓi bakuncin dubban magoya bayansa da suka kai masa gaisuwar barka da sallah. Matawalle wanda ya kasance tsohon gwamnan Zamfara, ya ce APC jam'iyya ce ta mutanen kirki da dattako, don haka ya shawarci Dauda Lawal ya shiga jam'iyyar. Ministan ya ce maimakon gwamnan ya bi ta ɓarauniya hanya, gara ya fito fili ya bi hanyar da ta dace wajen shiga APC. "Ba ni da matsala da gwamnan idan yana son shiga APC. Ya zo ya bi sahun masu yunkurin kawo ci gaba a ɓangaren tsaro da zaman lafiya da kuma ayyukan raya ƙasa," in ji Matawalle. Ya kuma ce shugaba Bola Tinubu jagora ne na...
Bazan iya zama jam’iyya daya da El-Rufai ba, saboda bashi da akida>>Inji Sanata Wadada yace ya bar jam’iyyar SDP

Bazan iya zama jam’iyya daya da El-Rufai ba, saboda bashi da akida>>Inji Sanata Wadada yace ya bar jam’iyyar SDP

Duk Labarai
Sanata Ahmed Aliyu Wadada daga Jihar Nasarawa ya bayyana cewa ya bar jam'iyyar SDP. Ya bayyana cewa dalilinsa na barin jam'iyyar shine ba zai iya ci gaba da zama da wadanda basu da akida a jam'iyya daya ba. Ya bayyana hakanne a hirarsa da 'yan jarida inda yace Musamman Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai, yace bashi da akida. Yace El-Rufai na kan gaba wajan jawo hankalin mutane da cewa ya kamata mulki ya koma kudancin Najeriya. Ya kara da cewa shine ya ce a zabi Tinubu amma saboda bai samu mukamin Minista ba amma ya bar jam'iyyar.
Fasto ya caccaki Shugaba Tinubu daboda fara yakin neman zabe shekaru 2 kamin zabe

Fasto ya caccaki Shugaba Tinubu daboda fara yakin neman zabe shekaru 2 kamin zabe

Duk Labarai
Babban Fasto a jihar Kaduna, Reverend Timothy Yahaya ya caccaki shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu inda ya bayyana cewa, yayi wuri a fara yakin neman zaben. Yace yana kiran shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da ya dakatar da yakin neman zaben inda yace sai kwanaki 90 kamin zaben ya kamata a fara yakin neman zaben. Reverend Timothy Yahaya yace gaba daya an manta da yiwa mutane aiki inda aka koma yakin neman zabe wanda a baya ba haka tsarin yake ba a kasarnan.