Saturday, April 25
Shadow
Peter Obi ya buƙaci magoya bayansa da su zabi ADC a zaɓukan cike-gurbi

Peter Obi ya buƙaci magoya bayansa da su zabi ADC a zaɓukan cike-gurbi

Duk Labarai
Tsohon ɗantakarar shugaban Najeriya a Jam'iyyar Labour, Peter Obi ya yi kira ga masu kaɗa ƙuri'a a Najeriya, musamman masoyansa na ƙungiyar Obidient da su zaɓi jam'iyyar ADC ne a zaɓukan cike gurbi da za a yi a gobe Asabar. Obi ya bayyana haka ne a shafinsa na Facebook, inda ya ce, "a game da zaɓukan da za a yi a gobe Asabar, 16 ga watan 2025 domin cike gurbin wasu kujeru a jihohi 16 na Najeriya, tunda jam'iyyar LP ba ta da ƴantakara saboda kotu ta hana sanadiyyar rikice-rikicen da ke cikin jam'iyyar, ina kira ga masoyana da su su zaɓi jam'iyyar haɗaka ta ADC a jihohinsu." Wannan jawabin na Obi na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta muhawara game da yunƙurin haɗakar siyasa, inda ake tunanin manyan jam'iyyun hamayya za su iya haɗuwa a guri ɗaya domin fuskantar Tinubu a zaɓe mai zuwa. ...
Hukumomin Shari’a Sun Amince Da Naira Dubu 20 A Matsayin Mafi Karancin Sadaki

Hukumomin Shari’a Sun Amince Da Naira Dubu 20 A Matsayin Mafi Karancin Sadaki

Duk Labarai
Hukumomin Shari'a Sun Amince Da Naira Dubu 20 A Matsayin Mafi Karancin Sadaki. Hukumar Zakka da Hubusi ta Jihar Kano tare da Hukumar Shari’a, Majalisar Malamai, Kungiyar Limaman Masallatan Juma’a da Kungiyar Ma’aikatan Zakka da Wakafi ta Kasa sun amince da sabbin ka’idoji kan Nisabin Zakka, Diyyar Rai da Sadakin Aure a jihar. A taron da aka gudanar a Kano ranar Alhamis, an yanke shawarar amincewa da naira dubu 20 a matsayin mafi ƙarancin sadakin aure, naira miliyan 150 a matsayin diyya ga wanda aka kashe bisa kuskure, da kuma naira dubu 985 a matsayin nisabin zakka, bisa lissafin farashin Durham. Babban Sakataren Kungiyar Ma’aikatan Zakka da Wakafi ta Kasa, Farfesa Aliyu Tahiru Muhammad na Jami’ar Bayero Kano ne ya bayyana cewa taron ya kuma amince a ci gaba da gudanar da irin...
Da Duminsa: A karin farko, Musulma me sanye da Hijabi, Ameera Hashwi, ta zama Sarauniyar kyau a kasar Amurka

Da Duminsa: A karin farko, Musulma me sanye da Hijabi, Ameera Hashwi, ta zama Sarauniyar kyau a kasar Amurka

Duk Labarai
Matashiya, Ameera Hashwi me shekaru 25 ta zama Sarauniyar kyau ta garin Wayne County, Michigan kasar Amurka. Ta kafa tarihi inda ta zama ta farko, Musulma kuma me sanye da hijabi da ta kafa wannan Tarihi. Ta kammala karatu daga jami'ar Dearborn Heights inda ta karanci Lauya. Saidai hakan ya tayarwa Amurkawa fararen fata hankali sosai inda suke tambayar ya akai aka bari haka ya faru?
Shugaba Tinubu ya bar Abuja dan ziyara zuwa kasashen Japan da Brazil

Shugaba Tinubu ya bar Abuja dan ziyara zuwa kasashen Japan da Brazil

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bar Abuja a yau, Juma'a dan zuwa kasashen Japan da Brazil ziyara. Shugaban zai tsaya a Dubai, UAE kamin ya ci gaba da tafiyar tasa. Shugaba Tinubu ya tashi daga filin jirgin Nnamdi Azikiwe da misalin karfe 11:15 na safiyar yau. Manyan jami'an gwamnati da suka hada da shugaban ma'aikatan fadar Gwamnati, Femi Gbajabiamila, da babban me baiwa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro, Malam Nuhu Ribadu, da Ministan kudi, Wale Edun sun halarci filin jirgin.
Kungiyar malaman kwalejojin Kimiyya da fasaha, ASUP sun baiwa Gwamnatin Tarayya wa’adin akwanaki 21 a biya musu bukatunsu ko su tafi yajin aiki

Kungiyar malaman kwalejojin Kimiyya da fasaha, ASUP sun baiwa Gwamnatin Tarayya wa’adin akwanaki 21 a biya musu bukatunsu ko su tafi yajin aiki

Duk Labarai
Kungiyar malaman Kwalejojin Ilimin Kimiyya da Fasaha ASUP ta baiwa gwamnatin tarayya wa'adin kwanaki 21 a biya musu bukatunsu ko su tafi yajin aiki. Shugaban kungiyar, Comrade Shammah Kpanja ya bayyana hakan ga manema labarai a Abuja ranar Juma'a. Yace daya daga cikin abubuwan da suke bukata shine a kafa hukuma me kula da ayyukan kwalejojin Ilimin kimiyya da fasaha. Sannan kuma ya kara da cewa auna neman a daidaita sakamakon kammaga kwalejojin ilimin kimiyya na HND da Kwalin Digiri da ake bayarwa bayan kammala Jami'o'i.
Kalli Bidiyo: Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya ce ba ya son a yafe masa zunubansa dan haka ba zai koma jam’iyyar APC ba

Kalli Bidiyo: Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya ce ba ya son a yafe masa zunubansa dan haka ba zai koma jam’iyyar APC ba

Duk Labarai
Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana cewa ba zai koma jam'iyyar APC ba kawai dan a yafe masa zunibansa. Tambuwal ya bayyana hakane a bayan da ya fito daga ofishin EFCC bayan kamun da suka masa. An kama Tambuwal bisa zargin cewa, ya cire Naira Biliyan 189 daga asusun bankin ajiyar jihar. https://twitter.com/jrnaib2/status/1956262313893253412?t=gWOOELY_ZAWEIw9kGNJYdA&s=19
Gwamna Dikko Raɗɗa zai fara biyan Limaman Coci alawus-alawus, zai ɗauki Malaman da za su karantar da addinin kiristanci a Katsina

Gwamna Dikko Raɗɗa zai fara biyan Limaman Coci alawus-alawus, zai ɗauki Malaman da za su karantar da addinin kiristanci a Katsina

Duk Labarai
Gwamna Dikko Raɗɗa zai fara biyan Limaman Coci alawus-alawus, zai ɗauki Malaman da za su karantar da addinin kiristanci a Katsina. Gwamnatin Jihar Katsina ta amince da bayar da alawus-alawus ga Limaman Coci a matsayin wani ƙoƙari na haɗin kai a addinai da kuma bayar da gudummawa ga Malaman addinai. Ƙungiyar Kiristoci ta kasa reshen jihar Katsina ta sanar da hakan a cikin wata sanarwa da sakataren Kungiyar Dakta Musa Daniel Danladi ya fitar a madadin Shugaban Ƙungiyar Very Rev. Fr. Richard Shuaibu Liti. Haka zalika, yace Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa ya amince da ɗaukar Malaman da suka karanci addinin kiristanci domin karantarwa a makarantun gwamnati, inda Kungiyar CAN ta bayyana cewa hakan zai tabbatar da daidaito da ci gaba, tana mai cewa ƙungiyar ta daɗe tana neman haka. Usman...
Kalli Bidiyo: Yanda mutane suka rikawa motocin ‘yan siyasa rotse da duwatsu a Zaria, Kaduna

Kalli Bidiyo: Yanda mutane suka rikawa motocin ‘yan siyasa rotse da duwatsu a Zaria, Kaduna

Duk Labarai
An ga Bidiyon yanda aka rikawa motocin 'yan siyasa rotse a Zaria jihar Kaduna. An ji matasa na fadin bama so, bamayi. Saidai kowane bangare tsakanin APC da ADC na ikirarin cewa abokan hamayarsa ne akawa hakan, wasu na cewa 'yan APC ne akawa haka yayin da wasu ke cewa 'yan ADC ne akewa hakan. A ranar Asabar ne dai za'a gudanar da zabe a wasu bangarori na jihar. https://twitter.com/Abdullahigoslow/status/1956099059267027228?t=SWVNuTEqjxCd79sLJH6lng&s=19 Akwai adawa me zafi tsakanin Tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad da Gwamna me ci, Malam Uba Sani.
Kalli Bidiyo: Inda Gwamna Abba Kabir Yusuf yace yana bayar da Naira Dubu 50 a rika baiwa matasa duk wata a wajan wani taro da ya halarta, saidai matasan sun ce ba’a basu ko sisi

Kalli Bidiyo: Inda Gwamna Abba Kabir Yusuf yace yana bayar da Naira Dubu 50 a rika baiwa matasa duk wata a wajan wani taro da ya halarta, saidai matasan sun ce ba’a basu ko sisi

Duk Labarai
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa daya daga cikin ayyukan da yakewa jihar Kano Shine baiwa matasa tallafin Naira dubu 50 a wata. Ya bayyana hakane a wajan wani taron siyasa. Saidai matasan sun musanta wannan ikirari na gwamnan inda suka ce ba'a basu ko sisi. Gwamnan dai yace zai yi bincike kan lamarin.