Thursday, December 18
Shadow
Ƙasar Saudiyya Za Ta Fassara Hudubar Aikin Hajjin Bana Da Yaren Hausa A Ranar 9 Ga Watan Zul-Hajj

Ƙasar Saudiyya Za Ta Fassara Hudubar Aikin Hajjin Bana Da Yaren Hausa A Ranar 9 Ga Watan Zul-Hajj

Duk Labarai
Za a fassara Hudubar Hajj ta shekarar 1446 zuwa harsuna 34 a ranar Alhamis, 9 ga Dhul Hijjah 1446, kamar yadda shafin Haramain Sharifain ya rawaito. Harsunan su ne kamar haka: Larabci Urdu Turanci Faransanci Indonesiyanci Farisanci (Farsi) Hausa Sinanci (Mandarin) Rashanci Bengalanci Turkiyanci Malayyanci (Bahasa Melayu) Sifaniyanci Fotugis Italiyanci Jamusanci Filipino (Tagalog) Amharic (Habasha) Bosniyanci Hindi Dutch Thai Malayalam Suwahili Pashto Tamil Azerbaijani Sufedish (Swedish) Uzbek Albanian Fulani (Fula) Somaliyanci Rohingya Yarabanci (Yoruba)
Gwamnan Jihar Kano Ya Ayyana Ranar Litinin A Matsayin Ranar Hutu Saboda Ràśuwar ’Yan Wasan Kwallon Kafa Na Kano Pillars

Gwamnan Jihar Kano Ya Ayyana Ranar Litinin A Matsayin Ranar Hutu Saboda Ràśuwar ’Yan Wasan Kwallon Kafa Na Kano Pillars

Duk Labarai
Gwamnan jihar Kano dake arewacin Najeriya Abba Kabir Yusuf, ya ayyana Litinin, 2 ga Yuni, a matsayin ranar hutu domin bawa al'umma su yi addu’a da jimamin ƴan wasan jihar 22 da suka rasu a hatsarin Mota ranar Asabar. Gwamnan ya kuma bayyan alhini tare da miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan mamatan. Wannan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Asabar 31 ga Mayu, 2025. Haka kuma gwamna Abba ya bukaci limamai da ɗaukacin musulmi dake gida da na ƙasa mai tsarki da suka je aikin hajji su yi addu’ar neman rahama ga mamatan da kuma juriya ga iyalansu.
Ji mugun abin da wannan dansandan yayi da ake ta murna bayan mutuwarsa

Ji mugun abin da wannan dansandan yayi da ake ta murna bayan mutuwarsa

Duk Labarai
Da yawan mutane na ta murna da mutuwar dansanda me suna CSP Ekene Nwosu dake aiki a jihar Akwa-Ibom. Kamin mutuwarsa, shine ke kula da bangaren yaki da 'yan fashi na hukumar 'Yansandan jihar. Saidai da yawa sun bayyanashi a matsayin mugu wanda ya zalunci mutane da dama a yayin gudanar da aikinsa. Wani babban lauya me suna Inibehe Effiong ya bayyana marigayin a matsayin mugu wanda 'yan siyasa ke amfani dashi suna cimma burinsh. Yace abin mamaki ne ganin yanda aka barshi ya ci gaba da aiki a matsayin dansanda duk da irin bakin halinsa. Saidai yace yana fatan mutuwarsa zata zama izina ga sauran 'yansanda masu hali irin nasa. Ba wannan lauyan ne kadai yayi korafi akan dansandan ba da yawa sun bayyana cewa bashi da kirki.
Gwamnatin Katsina ta nemi a soke jarabawar WAEC ta turanci

Gwamnatin Katsina ta nemi a soke jarabawar WAEC ta turanci

Duk Labarai
Gwamnatin Katsina ta nemi a soke jarabawar WAEC ta turanci. Gwamnatin Jihar Katsina a ranar Asabar ta nemi a soke jarabawar harshen Turanci da Hukumar Jarabawa ta Yammacin Afirka (WAEC) ta gudanar kwanan nan. Wannan kiran ya biyo bayan wani lamari da ya haifar da jinkiri mai tsawo kafin fara jarabawar a fadin kasar nan a ranar Laraba. Matsayar gwamnatin jihar ta fito ne daga bakin Kwamishinar Ilimin Firamare da Sakandare, Zainab Musa-Musawa, lokacin da ta kai ziyara ofishin WAEC da ke Katsina. Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa wannan matsaya ta samo asali ne daga wata takardar korafi da Babbar Sakatariyar ma’aikatar, Hajiya Ummukhair Ahmed ta sanya wa hannu. A baya dai, WAEC ta danganta jinkirin fara jarabawar da ƙoƙarinta na hana magudin jarab...

PSG ta lallasa Inter Milan da ci 5-0 inda ta lashe kofin Championship League, kalli Yanda magoya bayan PSG din suka daga tutar neman a daina kàshè Falasdiynawa a Gàzà

Duk Labarai
Kungiyar kwallon kafa ta PSG ta lashe kofin Championships League bayan lallasa Kungiyar Inter Milan da ci 5-0 a wasan da suka buga da yammacin yau. Mayulu, Kvaratskhelia,Doue, da Hakimi ne suka ci mata kwallayen. Sun kafa tarihin zama kungiya ta farko data taba lashe kofin da ci 5-0. Dan wasan Kungiyar, Désiré Doué ya zama na farko da ya zama taimaka aka ci kwallo sannan ya ci kwallaye 2 a wasan karshe na gasar Championships League. Wani abu da ya kara daukar hankula a wasan shine yanda magoya bayan PSG suka rika data rubutu me dauke da neman a dainawa mutanen Gàzà kisan Kare dangi.
‘Yan Bìndìga ne ke mulkar Najeriya>>Inji Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai

‘Yan Bìndìga ne ke mulkar Najeriya>>Inji Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai

Duk Labarai
Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa, 'yan Bindiga ne ke mulkar Najeriya. El-Rufai yace dan haka Najeriya na cikin tsaka mai wuya. El-Rufai yace 'yan Najeriya na ci gaba da maimaita kuskuren da suka yi a baya na zabar shuwagabannin da bana gari ba. Ya bayyana hakane a babban birnin tarayya, Abuja ranar Asabar a wajan wani taro. Yace Najeriya na cikin matsalar da bata taba shiga ba tun shekarar 1914 a yayin sa aka hade Arewa da kudu. Yace mafi yawancin shuwagabannin basu san yanda zasu gudanar da mulki ba kawai su dai su samu mulkin shine a gabansu.

Gwamnatin jihar Kano tasa a baiwa iyalan kowane daga cikin ‘yan wasan kwallon da suka ràsù Naira Miliyan daya da kayan abinci

Duk Labarai
Mai Girma Gwamnan Kano Alh. Abba Kabir Yusuf ya bayyana alhinin sa matuka bisa rasuwar Yan Wasan Kano Mutum ashirin da biyu (22). Gwamna ya bayarda umarni abawa iyalan kowanne mamaci Naira miliyan daya (1-million) hade da kayan abinchi kafin yadawo daga kasa mai tsarki (Aikin hajji) Allah ya saka maka da alkhairi Mai Girma Gwamnan Kano ya Kuma sa kayi aikin hajji karbabbiya
Kalli Bidiyon yanda Mutum 19 suka ràsì bayan tawagar ƴanwasan Kano sun yi hatsari

Kalli Bidiyon yanda Mutum 19 suka ràsì bayan tawagar ƴanwasan Kano sun yi hatsari

Duk Labarai
Motar da ke ɗauke da ƴanwasan Kano da masu horar da su a gasar wasanni ta ƙasa wato National Sport Festival ta Najeriya ta yi hatsarin a hanyar komawa gida, inda rahotanni suka ce mutum 19 daga cikinsu sun rasu, sannan wasu sun jikkata. Lamarin ya faru kimanin kilomita 50 zuwa Kano a yau Asabar bayan motar ta taso daga jihar Ogun da ke kudu maso yammacin ƙasar bayan an kammala wasannin a ranar Juma'a. https://twitter.com/SaharaReporters/status/1928797578813984970?t=-7LG2F0J5GMJapK0JxPhMg&s=19 Ibrahim Umar Fage shugaban riƙo na hukumar wasanni ta jihar Kano ya tabbatar wa BBC da aukuwar lamarin, inda ya ce, "ƴanwasanmu sun kwana a Abuja ne da safe sai suka kama hanyar komawa gida. A kusa da Dakatsalle suka yi hatsari. Motar ta faɗa wata gada da ke kusa da Ciromawa. Aƙalla mut...
Hotuna: Jaruman Kannywood Sun Kaiwa Jagoran Mabiya Shi’a Ziyara Ta Musamman A Gidansa Da Yake Abuja

Hotuna: Jaruman Kannywood Sun Kaiwa Jagoran Mabiya Shi’a Ziyara Ta Musamman A Gidansa Da Yake Abuja

Duk Labarai
Jaruman Kannywood Sun Kaiwa Jagoran Mabiya Shi'a Ziyara Ta Musamman A Gidansa Da Yake Abuja Wasu gungun jaruman finafinai Hausa na Kannywood sun ziyarci Jagoran Mabiya Shi'a Sheikh Ibraheem Zakzaky a ranar Laraba, a gidansa da ke birnin tarayya Abuja. Sheikh El-zakzaky ya hore su da su zama jakadu na gari wajen isar da saƙo, da wayar da kan al'umma, ilimi da fadakarwa. Me zaku ce?