Thursday, December 18
Shadow
Wani me laifi da aka yankewa hukuncin daurin rai da rai ya mùtù ya dawo yace a sakeshi ya gama zaman gidan yarin da yake tunda ya mùtù ya dawo

Wani me laifi da aka yankewa hukuncin daurin rai da rai ya mùtù ya dawo yace a sakeshi ya gama zaman gidan yarin da yake tunda ya mùtù ya dawo

Duk Labarai
Wani me laifi me suna Benjamin Schreiber da ake tsare dashi a gidan yari na jihar Iowa dake kasar Amurka saboda aikata kisa aka kuma mai hukuncin daurin rai da rai yace a sakeshi yanzu ya gama zaman gidan yarinsa tunda ya mutu ya dawo. Wata Kwaya ce ya sha ta sa yayi Doguwar suma shine da ya farfado ya shigar da kara yace wai a sakeshi tunda ya mutu ya dawo. Alkali dai yayi watsi da wannan bukatar tashi inda yace har yanzu yana nan da ranshi be mutu ba.
Kamar Dai BUA Shima Dangote ya sha Alwashin karya farashin Shinkafa

Kamar Dai BUA Shima Dangote ya sha Alwashin karya farashin Shinkafa

Duk Labarai
Attajirin dan kasuwa, Aliko Dangote ya sha Alwashin karya farashin Shinkafa inda yace zai kafa kamfanin shinkafar a jihar Naija. Hakan na zuwane kwanaki bayan da BUA ya sha Alwashin karya farashin shinkafar. Babbar me baiwa shugaban kamfanin na Dangote shawara Fatima Abdurrahman ce ta bayyana haka inda tace aina gina kamfanin shinkafar ne a Wushishi. Tace shirin gina kamfanin yana karkashin hadaka ne da Gwamnatin jihar Naija ke yi da kamfanoni masu zaman kansu.
Neman Shawara: Ni matar Aure ce, An samu matsala, Tsautsai yasa abokin aiki na a ofis ya dirkamin ciki, mijina kuma ya zata cikinsa ne amma abin ya dameni, me ya kamata na yi?

Neman Shawara: Ni matar Aure ce, An samu matsala, Tsautsai yasa abokin aiki na a ofis ya dirkamin ciki, mijina kuma ya zata cikinsa ne amma abin ya dameni, me ya kamata na yi?

Duk Labarai
Wata matar aure dake aiki ta shiga tsaka mai wuya. Tace a boye sunanta inda tace ta fara lalata da abokin aikinta a Ofis inda ya dirka mata ciki a karin farko. Tace a lokacin dansu bai cika shekara guda ba, mijinta kuma yasha cikinsa ne dan haka yace ta zubar da cikin dan su samu su baiwa karamin dansu kulawa. Tace saidai a karo na biyu, abokin aikin nata ya sake dirka mata ciki inda tace amma a wannan karin mijin nata yace kada ta zubar da cikin. Musamman lura da cewa a baya ya sata ta zubar da cikin. Tace abinda ke damunta shine mijin nata bai san cewa, cikin ba nasa bane gashi yana ta nan nan da ita. shine take
Ji yanda matasa suka kàshè DPO bayan da aka zargi DPOn da Kàshè wani matashi da duka a Kano

Ji yanda matasa suka kàshè DPO bayan da aka zargi DPOn da Kàshè wani matashi da duka a Kano

Duk Labarai
Mafusata Sun Yi Silàr Mùtùwaŕ DPO'n 'Yañ Sanďà Na Garin Rano Bayan Sun Far Masa Sakamakon Zargiñsa Da Kàshè Wani Matashi Biyo Bayan Dukan Da Ya Yi Masa Lamarin dai ya jawo konè-konè da fashè-fashen motocin 'yan sandan na garin Rano dake Kano, biyo bayan mutuwar matashin. Majiyar Rariya ta tabbatar da cewa DPO'n ya rasa ne bayan gajeruwar jinya a asibiti.
YANZU-YANZU: Kakakin Majalisa Tajudeen Abbas Ya Janye Kudirin Tilasta Zaɓe wanda za’a rika cin mutum tarar Naira dubu dari bayan da ya sha suka

YANZU-YANZU: Kakakin Majalisa Tajudeen Abbas Ya Janye Kudirin Tilasta Zaɓe wanda za’a rika cin mutum tarar Naira dubu dari bayan da ya sha suka

Duk Labarai
Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas, ya janye kudirin dokar da ke neman tilasta wa 'yan Najeriya kada kuri'a a kowane zaɓe. Kudirin dai na neman gyara Dokar Zaɓe ta 2022, inda aka tanadi cewa duk masu cancantar kada kuri’a dole ne su fito su zaɓa a kowanne zabe, kuma wanda ya ki, zai iya fuskantar hukunci na daurin watanni shida zuwa tara, ko tara har Naira 100,000. Sai dai, wannan kudiri ya jawo ce-ce-ku-ce daga jama’a da kungiyoyin kare hakkin dan adam. Kungiyar SERAP ta bayyana cewa wannan yunkuri ya sabawa yancin dan adam, kundin tsarin mulki da kuma dokokin kasa da kasa. Sun jaddada cewa 'yancin kada kuri’a yana nufin mutum na da damar yanke shawara – ya kada kuri’a ko kuma ya ki. Haka kuma, sun yi barazanar daukar matakin shari’a idan aka amince da kudirin. Fi...
Iyalina sunce matsin Yayi Yawa in Aje Mukamina Kada A Kàshè ni, Kamar Yanda Aka Kèshè Thomas Sankara: Nace Masu A A Koda na Mùtù To Tabbas Na Mùtù ne Wurin ceto Al’ummar mu>>Inji Matashin Shugaban kasar Burkina

Iyalina sunce matsin Yayi Yawa in Aje Mukamina Kada A Kashe ni, Kamar Yanda Aka Kashe Thomas Sankara: Nace Masu A A Koda na Mutu To Tabbas Na Mutu ne Wurin ceto Al'ummar mu. Shugaban kasar Burkina Faso Ibrahim Traore Tabbas Kowa Yasan Akwai Kalubale Mai Yawa A Gaban Sa, A Halin Yanzu Kawai Muna Yimasa Addua Allah Ya kara Bashi Kariya.
Hukumar babban birnin tarayya Abuja ta kulle ofishin hukumar karbar Haraji ta kasa, FIRS, da bankin Access Bank, da gidan Man Total da sauransu saboda rashin biyan Haraji

Hukumar babban birnin tarayya Abuja ta kulle ofishin hukumar karbar Haraji ta kasa, FIRS, da bankin Access Bank, da gidan Man Total da sauransu saboda rashin biyan Haraji

Duk Labarai
Hukumar kula da babban birnin tarayya Abuja, FCTA ta kulle matan gine-gine a birnin saboda rashin biyan kudaden haraji da ake binsu. Wasu daga cikin manyan gine-ginen da aka kulle sun hada da: Babban Ofishin Jam'iyyar PDP na kasa. Ofishin hukumar tattara Haraji na kasa, FIRS dake Zone 5. Ofishin Access Bank dake Wuse. Da ofishin al'adun kasar China dake Zone 5. Da gidan man Total dake Zone 5. Da dai sauransu.