Thursday, December 18
Shadow
Tinubu ya miƙa ta’aziyya kan rasuwar ƴan wasan Kano da su ka yi haɗari

Tinubu ya miƙa ta’aziyya kan rasuwar ƴan wasan Kano da su ka yi haɗari

Duk Labarai
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna alhini da jimami da alhini bisa rashe-rashen da suka faru a jihohin Kano da Neja, yana mai bayyana lamarin a matsayin babban rashi ga ƙasa baki ɗaya. A wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Juma’a, Shugaba Tinubu ya nuna matuƙar kaɗuwa kan hatsarin mota da ya rutsa da ‘yan wasan Jihar Kano a hanyarsu ta dawowa daga gasar wasanni ta ƙasa da aka kammala a Jihar Ogun. Shugaban Ƙasa ya yi addu’ar Allah ya jikan waɗanda suka rasa rayukansu a cikin hatsarin, ya kuma roƙi Allah ya bai wa iyalansu da daukacin al’ummar Kano haƙuri da juriya. Ya ce hanya mafi inganci ta girmama su ita ce ɗaukar matakan kariya domin rage aukuwar irin wannan ibtila’i a gaba. Baya ga haka, Tinubu ya bayyana alhini...
Gwamnatin Kano ta sanar da ranar hutun Babbar Sallah ga makarantun Firamare da Sakandare

Gwamnatin Kano ta sanar da ranar hutun Babbar Sallah ga makarantun Firamare da Sakandare

Duk Labarai
Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da umarni ga dukkan makarantun Firamare da na Sakandare a fadin jihar da su tafi hutun Babbar Sallah daga ranar Laraba, 4 ga Yuni, 2025 zuwa Lahadi, 15 ga Yuni, 2025 ga ɗaliban makarantu kwana, sannan daga ranar Laraba 4 ga Yuni, 2025 zuwa Litinin 16 ga Yuni, 2025 ga ɗaliban da ke zuwa gida bayan makaranta. Wani jawabi da Daraktan Wayar da Kan Jama’a na Ma’aikatar Ilimi, Balarabe Abdullahi Kiru ya sanya wa hannu ya bayyana cewa iyaye da masu kula da ɗaliban makarantun kwana su je su ɗauki ‘ya’yansu da sassafe a ranar Laraba, 4 ga Yuni, 2025. Sanarwar ta nakalto Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Dr. Ali Haruna Makoda yana kira ga iyaye da masu kula da su tabbatar da cewa ‘ya’yansu sun dawo makaranta a ranar da aka tsara, tare da gode musu bisa goyon baya d...
Ku kara hakuri dani, ku bani Lokaci>>Shugaba Tinubu ya roki ‘yan Najeriya

Ku kara hakuri dani, ku bani Lokaci>>Shugaba Tinubu ya roki ‘yan Najeriya

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya roki 'yan Najeriya da su kara hakuri dashi inda yace su bashi lokaci. Ya bayyana hakanne a yayin kaddamar da sashin farko na titin Calabar zuwa Legas ranar Asabar. Yace yasan cewa har yanzu mutane suna cikin tsammanin samun sauki kuma yasan cewa ana cikin matsi amma yana kiran a kara hakuri, sauki yana zuwa. Shugaba Tinubu yace za'a samu ci gaba sosai kuma farashin kaya zai sauka, suna kokarin kawar da rashawa da cin hanci a bangaren canjin kudi da bangaren sayar da man fetur.
Maza sama da 50 na taimakawa na koyama Jima’i wanda basu taba sanin mace ba>>Inji Wannan matar

Maza sama da 50 na taimakawa na koyama Jima’i wanda basu taba sanin mace ba>>Inji Wannan matar

Duk Labarai
Wata mata me suna Gigi Patsy 'yar Komanin shekaru 29 ta bayyana cewa, maza sama da 50 ne ya lalata ta hanyar koya musu yanda ake Jima'i. Ta bayyana cewa ta hadu da maza sama sa 2000. Saidai tace abin mamaki a cikinsu akwai sama da 50 wanda basu taba sanin mace ba. Tace kuma ba wai matasa bane kadai hadda wadanda suka haura shekari 30 zuwa 50. Tace wasu zasu je su ce mata ko kiss basu taba yiwa mace ba kuma haka zata hakura ta fara koyar dasu. Tace wasu addini, da al'ada da kunya na taimakawa wajan rashin iya jima'insu. Tace amma duk tana koyar dasu.
Gwamnatin Kano na da kudin da ta fi Karfin Haka: Shehu Sani yace Naira Miliyan daya da Gwamna Abba yace a baiwa kowane iyalan ‘yan kwallon Kano da suka ràsù a hadarin mota ta yi kadan

Gwamnatin Kano na da kudin da ta fi Karfin Haka: Shehu Sani yace Naira Miliyan daya da Gwamna Abba yace a baiwa kowane iyalan ‘yan kwallon Kano da suka ràsù a hadarin mota ta yi kadan

Duk Labarai
Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa, Naira Miliyan 1 da Gwamnatin Kano tace a baiwa kowane daga cikin iyala 'yan Kwallon jihar da suka yi hadari ta yi kadan. Sanata Sani ya bayyana hakane a shafinsa na sada zumunta inda yace Gwamnatin jihar Kano na da kudin da ya kamata ace abinda zata bayar yafi haka. Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da yake aikin hajji, ya ce a baiwa kowane daga cikin iyalan 'yan kwallon Naira Miliyan 1 sannan a basu kayan abinci kamin ya dawo.
Bidiyon wani mahajjacin Najeriya na kiran Shehu a Kasar Saudiyya ya jawo cece-kuce

Bidiyon wani mahajjacin Najeriya na kiran Shehu a Kasar Saudiyya ya jawo cece-kuce

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{"square_fit":1},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":true,"containsFTESticker":false} Bidiyon wani Mahajjaci a kasar Saudiyya dake cikin mahajjatan Bana yana kiran Shehu ya dauki hankula. https://twitter.com/_mai_daraja/status/1928928524502487253?t=mGvwrKfhfp7oqNc1-89GmA&s=19 Lamarin yasa mutane na bayyana cewa yayi asarar Naira Miliyan 8 da wani abu da ya biya ya je aikin Hajjin. Menene ra'ayinku?
Gwamnan jihar Akwa-Ibom ya magantu bayan da diyarsa ta zargeshi da yunkurin kàshè ta da yin tsafi da ita da diyarta

Gwamnan jihar Akwa-Ibom ya magantu bayan da diyarsa ta zargeshi da yunkurin kàshè ta da yin tsafi da ita da diyarta

Duk Labarai
Gwamnan jihar Akwa-Ibom, Umo Eno ya bayyana cewa, babu wata matsala a cikin iyalinsa, bayan da diyarsa ta zargi cewa yana yunkurin kashe ta da diyarta dan yin tsafi dasu. Diyar Gwamnan me suna Jane, ta zargi cewa, haka mahaifiyarta da 'yan uwanta biyu suka mutu inda ake zargin baban nasu da kashesu ta hanyar tsafi. Saidai a martaninsa, Gwamnan yace ana kokarin kawar masa da hankali ne a aikin da yake yi a matsayinsa na Gwamna. Yace wannan tsohon bidiyone kuma a yanzu da yake kokarin bayyana irin ayyukan da gwamnatin sa ta yi a cikin shekaru 2 da yayo yana Gwamna, shine aka dauko tsohon bidiyon ana yadawa.
A yau Lahadi, Masana Kimiyya sun ce wani Mulmule daga Rana zai fado Duniyarmu inda zai iya lalata wutar Lantarki, da Intanet

A yau Lahadi, Masana Kimiyya sun ce wani Mulmule daga Rana zai fado Duniyarmu inda zai iya lalata wutar Lantarki, da Intanet

Duk Labarai
Masana sararin samaniya na kasar Amurka, NOAA sun bayyana cewa, akwai yiyuwar wani mulmule daga rana zai fado Duniyarmu a yau Lahadi. Sun bayyana cewa, mulmulen na da sauri sosai inda yake gudun kisan Kilometres 1000 a duk sakan ko dakika. Sun ce zuwansa Duniyar mu ka iya shafar wutar lantarki da yadda Intanet ke aiki. Saidai basu bayyana a wane yanki ne zai fado ba.
Mu Dai Mun bi: Tinubu zamu zaba a shekarar 2027, Inji Gwamnan Legas inda yace farashin kayan abinci yayi kasa

Mu Dai Mun bi: Tinubu zamu zaba a shekarar 2027, Inji Gwamnan Legas inda yace farashin kayan abinci yayi kasa

Duk Labarai
Gwamnan jihar Legas, Sonwo Olu ya bayyana goyon bayansa ga zarcewar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a shekarar 2027. Ya bayyana hakane a yayin da yake jawabi ga ma'aikatan jihar Legas din inda yace yana aiki ne tukuru wajan inganta rayuwar su. Yace ana ganin alfanun tsare-tsaren gwamnatin Tinubu inda yace misali an samu ci gaba ta fannin noma, farashin kayan abinci ya sauka.