Monday, December 15
Shadow
Kalli Bidiyon yanda masunta suka kama Katoton maciji a Kaduna me ban tsoro

Kalli Bidiyon yanda masunta suka kama Katoton maciji a Kaduna me ban tsoro

Duk Labarai
Bidiyon yanda wasu masunta da suka je kamun kifi amma suka kama Katon maciji a jihar Kaduna ya dauki hankula. An ce aun ajiye macijinne har kusan tsawon wata daya inda wani ya sayeshi amma ya rika yunkurin tserewa. Abin dai ya bada mamaki: https://twitter.com/Nasir1on1/status/1925204970732745095?t=hVC6JcLoXlxX71V2rZlvdQ&s=19 Da yawa aun yo mamaki da ganin girman Macijin.
Bankin Duniya yace rabin mutanen Najeriya watau mutane sama da Miliyan 100 sun fada Talauci tsamo-tsamo

Bankin Duniya yace rabin mutanen Najeriya watau mutane sama da Miliyan 100 sun fada Talauci tsamo-tsamo

Duk Labarai
Bankin Duniya yace kusan rabin 'yan Najeriya sun fada cikin talauci tsamo-tsamo saboda tsadar rayuwa dake karuwa akasar. Sanarwar da bankin ya fitar yace kaso 46 na 'yan Najeriya watau mutane Miliyan 107 sun fada cikin talauci inda suke rayuwa a kasa da Dala $2.15 a kullun. Bankin yace ma'aikata basa samun rayuwa me kyau saboda Albashinsu baya kai musu yanda ya kamata. A baya dai bankin yace akwai Talauci sosai a tsakanin kauyawan Najeriya.
Kalli Bidiyo: ‘Yar majalisar Amurka, Nancy Mace ta nunawa abokan aikinta ‘yan majalisa Bidiyonta tsirara wanda tace tsohon saurayinta ne ya dauke ta ba tare da izinin ta ba kuma tana son a hukuntashi

Kalli Bidiyo: ‘Yar majalisar Amurka, Nancy Mace ta nunawa abokan aikinta ‘yan majalisa Bidiyonta tsirara wanda tace tsohon saurayinta ne ya dauke ta ba tare da izinin ta ba kuma tana son a hukuntashi

Duk Labarai
'Yar majalisar Amurka, Nancy Mace ta nunawa abokan aikinta a zaman majalisar Bidiyon ta tsirara dan ta kafa shaida akan zargin da takewa tsohon Saurayinta cewa ya yada Bidiyon tsiraicinta ba tare da izinin ta ba. Ta ce ya yada Bidiyon ta har guda dubu 10 ba tare da izininta ba. https://twitter.com/nypost/status/1925193881437548789?t=LGLEHnJo4XBJNQ4g_OZW_g&s=19 Saidai mutane na shakkar cewa ta yaya zai samu Bidiyon ta har guda dubu 10 kuma tace ba tare da saninta ba? Ana zargin dai ya kafa kyamarori ne a gurare daban-daban inda ta hakane ya samu Bidiyon nata.
An buɗe cibiyar koya wa almajirai kwamfuta a Sokoto

An buɗe cibiyar koya wa almajirai kwamfuta a Sokoto

Duk Labarai
Gwamnan jihar Sokoto Ahmad Aliyu ya ƙaddamar da wata cibiyar bai wa almajirai da yara mata marasa zuwa makaranta ilimin kwamfuta da na sana'o'i "domin inganta rayuwarsu". Cibiyar wadda gwamnatin ta gina tare da tallafin asusun tallafa wa yara na duniya UNICEF, zai mayar da hankali wajen koya wa ɗaliban ilimin yadda za su yi sana'a ta amfani da fasahar zamani, ta hanyar amfani da wayoyin hannu da kuma kwamfuta. Manufar shirin ita ce tallafa wa tsarin bayar da ilimi ga kowa, a matakin jiha da ƙananan hukumomi. Baya ga ilimin kwamfuta, ɗaliban za su kwashe shekara ɗaya suna samun horo a sana'o'i daban-daban da kuma ilimin rubutu da karatu. Sokoto na cikin jihohin arewacin Najeriya masu fama da matsalar yawaitar yara marasa zuwa makaranta da kuma almajirai masu gararamba a kan titu...
‘Ƴan majalisar Najeriya na cusa kwangilolin son rai a kasafin kuɗi’

‘Ƴan majalisar Najeriya na cusa kwangilolin son rai a kasafin kuɗi’

Duk Labarai
Rahoton wata ƙungiya mai sanya ido kan kasafin kuɗi a Najeriya da wasu ƙasashen Afirka (BudgIT) ya gano cewa wasu ƴan majalisar dokokin Najeriya na cusa kwangiloli marasa amfani, waɗanda ba su da alfanu ga ƙasa a cikin kasafin kuɗin Najeriya. BudgIT ta ce ta gano kwagiloli har 11,122 wadanda za su lashe kuɗin da ya haura naira tiriliyan 6.93 da aka saka a cikin kasafin kuɗin 2025 da Majalisar ƙasa ta cusa ba tare da la’akari da cancanta ba. Haka nan rahoton ya bayyana cewa an cusa irin wadannan ayyuka a kasafin hukumomi da ma’aikatun gwamnati waɗanda ba su da wata alaƙa da ayyukan. Wasu daga cikin kwangilolin da aka lissafa sun haɗa da kwangilar bayar da tallafin karatu da rabon takin zamani da gina cibiyar koyar da kwamfuta ICT/CBT, da kuma samar da motoci don tsaro da sauransu d...
Kotu Ta Tasa Keyar Wasu Mutane Biyar Zuwa Gidan Yari A Kano Saboda Awakinsu Sun Ci Shukar Gwamnati

Kotu Ta Tasa Keyar Wasu Mutane Biyar Zuwa Gidan Yari A Kano Saboda Awakinsu Sun Ci Shukar Gwamnati

Duk Labarai
Kotu ta yanke wa mutane biyar hukunci bisa sakin awaki su lalata bishiyu a Kano. Wata kotun majistare da ke Kano ta yanke wa mutane biyar hukuncin daurin wata guda a gidan yari saboda barin awakinsu su yi yawo babu kulawa tare da lalata shuke-shuken ado da gwamnatin jihar ke yi a titunan Lodge Road da Race Course Road. Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi ta Jihar Kano ce ta gurfanar da wadanda aka kama, karkashin jagorancin Usman Abdullahi, bisa sashe na 7(e) na dokar lafiyar jama’a ta jihar Kano ta shekarar 2019, wadda ke haramta duk wani aiki da zai lalata kayayyakin more rayuwa na gwamnati ko ya zama barazana ga muhalli. LEADERSHIP ta rawaito cewa lamarin ya jawo hankalin jama’a makonni da suka gabata bayan jami’an ma’aikatar sun kama awaki 17 da aka samu suna kiwo a cikin ...
Ƴan siyasa da sojoji na daga cikin masu baiwa masu ikirarin Jìhàdì bayanai>>Inji Gwamna Zulum

Ƴan siyasa da sojoji na daga cikin masu baiwa masu ikirarin Jìhàdì bayanai>>Inji Gwamna Zulum

Duk Labarai
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya zargi wasu jami’an sojoji da ƴan siyasa da kasancewa masu bai wa ƴan ta’addan Bòkò Hàràm bayanai da kuma hada kai da su. Daily Trust ta rawaito cewa yayin wata hira da aka yi da shi a shirin 'Breakfast Central' na tashar News Central, Zulum ya sha alwashin daukar saka kafar wando ɗaya da duk wanda ke kokarin kawo cikas ga kokarin gwamnatinsa na yaki da ta’addanci a jihar. Gwamnan ya kara da cewa gwamnatinsa za ta karfafa aikin leken asiri domin shawo kan ’yan ta’addan da masu taimaka musu. Ya ce: “Muna da masu bayar da bayanai da masu hada kai da su a cikin Sojojin Najeriya, cikin ’yan siyasa da kuma a cikin al’umma. “Abin da za mu yi shi ne mu karfafa aikin leken asiri kuma mu dauki mataki mai tsauri a kansu. “Mu cire tsarin kwangila ...
Kalli Bidiyon yanda dansandan Najeriya ya harbe Dalibin dake kan hanyar zuwa rubuta WAEC ya mùtù

Kalli Bidiyon yanda dansandan Najeriya ya harbe Dalibin dake kan hanyar zuwa rubuta WAEC ya mùtù

Duk Labarai
Ana zargin dansandan Najeriya da harbin dalibin dake kan hanyar zuwa rubuta jarabawar WAEC inda dalibin ya mutu. Lamarin ya faru a jihar Oyo. Mahaifin yaronne yake tuka mota inda yayi aron hannu sai aka yi rashin sa'a ya hadu da hukumar kula da hadurra ta jihar me suna, OYTMA. Da aka tsayar dashi sai yaki tsayawa ashe 'yansanda na kusa inda suka kara mai mota nan ma yaki tsayawa sai suka yi zuga suka bishi. https://twitter.com/OurFavOnlineDoc/status/1925080799910490117?t=m8uYTW_Yg7509vo6kNenNw&s=19 https://twitter.com/OurFavOnlineDoc/status/1925080799910490117?t=m8uYTW_Yg7509vo6kNenNw&s=19 Anan ne daya daga cikin 'yansandan yayi kokarin harbin tayar motar inda harsashin ya kuskure ya harbi dan me motar, Kehinde Alade me shekaru 14. An garzaya dashi Asibiti ...