Hajji 2025: Rukunin Farko Na Maniyyatan Jihar Borno Sun Tashi Zuwa Ƙasa Mai Tsarki
Mataimakin gwamnan Jihar Borno, Dakta Umar Kadafur, tare da shugaban kwamitin aikin Hajji na Jihar Borno, Sanata Kaka Shehu Lawan, SAN, sun gabatar da jawabin bankwana ga rukunin farko na alhazan Jihar Borno da suka tashi zuwa ƙasa mai tsarki domin gudanar da Hajjin 2025, jiya, a filin sauka da tashin jiragen sama na ƙasa da ƙasa da ke birnin Maiduguri.
Cikin jawabin da suka gabatar, Sanata Kaka da Dakta Kadafur da sauran membobin kwamitin sun yi wa maniyyatan fatan sauka lafiya da gudanar da aikin Hajji lafiya cikin nasara. Sun kuma buƙaci maniyyatan da su yi amfani da lokacin wajen gudanar da addu’ar zaman lafiya da ci gaba ga Jihar Borno da Najeriya.
A cewar Kadafur, wanda shi ne shugaban kwamitin aikin Hajji na Jihar Borno na shekarar 2025 kana kuma Amirul Hajji, ya ba da tabbaci...








