Tuesday, December 16
Shadow
Za mu shiga haɗakar ƴan hamayya ƙarƙashin David mark – Shekarau

Za mu shiga haɗakar ƴan hamayya ƙarƙashin David mark – Shekarau

Duk Labarai
Ƙungiyar siyasa ta Northern Democrats, ƙarƙashin jagorancin Malam Ibrahim Shekarau ta ce za ta shiga sabuwar haɗakar ƴan hamayya ta National Coalition Group ƙarƙashin tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata David Mark domin tunkarar zaɓen 2027. A wata sanarwar bayan taron da ƙungiyar ta yi ranar Alhamis, ND ta ce duk da amincewar da ta yi na shiga haɗaka, amma za su ci gaba da bayar da gudunmawa wajen tattaunawa yiwuwar kafa sabuwar jam'iyya ko kuma shiga wata jam'iyyar domin yin tafiya tare. Harwayau, ƙungiyar ta Northern Democrats ta ƙara da cewa sun amince da matsa wa gwamnati lamba musamman jagorancin majalisar dokoki wajen ganin an tabbatar da bin tsarin mulkin ƙasar sau da ƙafa. Daga ƙarshe ƙungiyar ta ce mambobinta sun amince su tattauna da jihohin arewacin ƙasa...
Ji Yadda aka tsinci Hamdiyya a dajin Zamfara bayan ɓacewarta a Sokoto

Ji Yadda aka tsinci Hamdiyya a dajin Zamfara bayan ɓacewarta a Sokoto

Duk Labarai
Makusantan matashiyar nan da ta yi suna bayan jan hankalin gwamnatin jihar Sokoto kan matsalar tsaro sun tabbatar wa BBC cewa an tsince ta a wani daji na jihar Zamfara bayan batan-dabon da ta yi. Tun ranar Talata ne aka bayar da rahoton ɓatan Hamdiyya Sidi Sharif, bayan ta fita domin zuwa kasuwa, lamarin da ya sanya ta kasa bayyana a zaman kotu kan shari'ar da ake mata a ranar Laraba a Sokoto. A watannin baya ne dai gwamnatin jihar Sokoto ta shigar da matashiyar ƙara a gaban kotu, bisa zargin ta da aikata laifin tunzura tayar da zaune tsaye, shari'ar da har yanzu ake gudanar da ita. A tattaunawarsa da BBC, lauyan da ke kare Hamdiyya, Abba Hikima ya ce yanzu haka tana wani asibiti da ke ƙaramar hukumar Bakura a jihar Zamfara "cikin mummunan yanayi." Ya ce ''wasu mutane ne sanye ...
Mun Gama Ýanke Shawarar Mayar Da Tinubu Jihar Legas A Zaben 2027, Domin Za Mu Dakatar Da Shi Daga Zarcewa A Mulki Karo Na Biyu, Inji El-Rufai

Mun Gama Ýanke Shawarar Mayar Da Tinubu Jihar Legas A Zaben 2027, Domin Za Mu Dakatar Da Shi Daga Zarcewa A Mulki Karo Na Biyu, Inji El-Rufai

Duk Labarai
Mun Gama Ýanke Shawarar Mayar Da Tinubu Jihar Legas A Zaben 2027, Domin Za Mu Dakatar Da Shi Daga Zarcewa A Mulki Karo Na Biyu, Inji El-Rufai. Daga Comr Nura Siniya Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa akwai wani muhimmin yunkuri na kafa hadaka da nufin ganin an dakatar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu daga sake samun mulki a karo na biyu. Malam Nasiru El-Rufai ya bayyana hakan ne a yayin taron baje kolin fasaha da ƙirƙira na “Arewa TechFest da aka gudanar a jihar Katsina ranar Laraba 21 ga watan Mayu 2025. A cewarsa, “Jiya da karfe 8 na dare, mun gudanar da wani muhimmin taro na hadakar da muke kokarin kafa wa domin tabbatar da cewa Shugaba Tinubu ya koma Legas.” Duk da wannan yunkuri, El-Rufai ya jaddada cewa akwai ministocin da suke ganin sun...
Da Duminsa: Matatar man Dangote ta sake rage farashin Man fetur

Da Duminsa: Matatar man Dangote ta sake rage farashin Man fetur

Duk Labarai
Rahotannin da muke samu na cewa, matatar man fetur ta Dangote ta sake rage farashin man fetur dinta. Matatar tace a yanzu a Legas za'a rika sayar da man fetur din akan Naira N875 kan kowace lita sai kuma a kudu maso yamma za'a rika sayar da man nasu akan Naira N885 kowace lita. A Arewa maso yamma da Arewa ta tsakiya kuwa za'a rika sayar da man fetur din ne akan Naira N895 duk lita. Hakanan tace a jihohin Kudu maso gabas da kudu maso kudu kuma za'a rika sayen man fetur din akan Naira N905 kowace lita. Matatar tace za'a samu man fetur din a wannan farashin a gidajen mai abokan hildarsu, wanda suka hada da MRS, AP, Heyden, Optima, TechnOil, da Hyde.
Kalli Bidiyo Gwanin ban Tausai: Yanda Mijina ya hanani zuwa jana’izar babana bayan ya ràsù, inji wannan matar

Kalli Bidiyo Gwanin ban Tausai: Yanda Mijina ya hanani zuwa jana’izar babana bayan ya ràsù, inji wannan matar

Duk Labarai
Wannan matar ta dauki hankula sosai a kafafen sadarwa bayan da ta yi zargin cewa, mijinta ya gallaza mata. Tace abinda ba zata taba mantawa dashi ba shine mahaifinta ya rasu amma ya hanata ta je jana'iza. Kalli Cikakkiyar hirar da aka yi dashi: https://www.tiktok.com/@bcrw.social.spotlight/video/7506277106347822392?_t=ZM-8wYy46Fya0c&_r=1 Labarin nata dai ya zowa mutane kamar Almara inda akai ta mamaki.
Kaso 85 na wadanda muke daukar nauyinsu mu aikasu karatu kasashen Turawa basa dawowa dan su taimaka a gina kasarnan>>Gwamnatin Tarayya ta koka

Kaso 85 na wadanda muke daukar nauyinsu mu aikasu karatu kasashen Turawa basa dawowa dan su taimaka a gina kasarnan>>Gwamnatin Tarayya ta koka

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta koka da cewa, Kaso 85 na daliban Najeriya da take daukar nauyinsu dan zuwa kasashen waje su karo ilimi da zummar su dawo dan ciyar da Najeriya gaba, basa dawowa. Ministan Ilimi, Dr Tunji Alausa ne ya bayyana hakan a wajan wani taro da ya wakana a Legas. Yace dalilin haka yasa suka canja lissafi domin sun gano cewa yawanci karatun da ake daukar nauyin daliban su je su yi a kasashen da suka ci gaba, za'a iya yinsa a Najeriya. Yace dan hakane suka mayar da hankali wajan karfafa harkar ilimin a Najeriya inda yace sun bude cibiyoyin bincike da zurfafa ilimi a jami'o'i daban-daban na kasarnan.
Jimullar masu laifi 2000 ne suka tsere daga gidajen yarin Najeriya kuma ake nema ruwa a jallo

Jimullar masu laifi 2000 ne suka tsere daga gidajen yarin Najeriya kuma ake nema ruwa a jallo

Duk Labarai
Bayan tserewar masu laifi daga gidan yarin Ilesa na jihar Osun su 7 ranar Talata, an gano cewa akwai masu laifi 2000 da suka tsere daga gidajen yari daban-daban na Najeriya da ake nema ruwa a jallo. Haka na zuwane wata daya kacal bayan da masu laifi 12 daga gidan yari me suna Katon Karfe suka tsere daga jihar Kogi. A shekarar 2024 ma dai an samu tserewar masu laifi daga gidan yarin MCC dake Suleja jihar Naija inda masu laifi 118 suka tsere amma guda 23 ne kawai aka samu damar sake kamowa. Hakan na zuwane yayin da laifuka da kashe-kashen da ayyukan ta'addanci suka yi yawa a Najeriya. Rahoton yace zuwa yanzu akwai jimullar masu laifi 2000 da suka tsere daga gidajen yarin Najeriya daban-daban.