Gwamnan jihar Enugu ya baiwa Dan Arewa mukamin me bashi shawara
Gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah ya baiwa dan Arewa,Alhaji Abubakar Yusuf Sambo mukamin me bashi shawara akan ayyuka na musamman.
Alhaji Abubakar Yusuf Sambo dai kuma shine sarkin Hausawan Enugu.
A Enugu aka haifeshi kuma yana jin Inyamuranci sosai.
Hakanan Gwamnan jihar Enugu ya bashi mukamin mem ba na kwamitin tsaro na jihar.








