Saturday, December 13
Shadow
Masu ikirarin Jìhàdì sun kàshè  manoma da masunta 40 a jihar Borno

Masu ikirarin Jìhàdì sun kàshè manoma da masunta 40 a jihar Borno

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar mayaƙan ÌŚWÀP ta kashe wasu manoma 23 da kuma masunta a wani hari da ta kai ƙauyen Malam Karanti kusa da Baga a karamar hukumar Kukawa na jihar Borno. Majiyoyi sun ce mayaƙan sun tara manoman da kuma masunta ne wuri ɗaya, inda suka kashe manoman wake 23. An hana mazauna garin ɗaukar gawawwakin ƴan uwansu da aka kashe, kamar yadda gidan talabijin na Channels a Najeriya ya ruwaito. "Mun yi ƙoƙarin zuwa don ɗaukar gawawwakin waɗanda aka kashe tare da jami'an tsaro, sai dai mayaƙan sun hana mu yin haka. Iyalai da dama na jiran gawawwakin ƴan uwansu," in ji wani ɗan garin. Ƙauyen Malam Karanti matattara ne na mayaƙan ISWAP, wuri kuma da fararen hula ke noma da kamun kifi duk da irin barazanar da suke fuskanta.
Hukumar tace fina-finai ta haramta bikin ‘ƙauyawa’ a jihar Kano

Hukumar tace fina-finai ta haramta bikin ‘ƙauyawa’ a jihar Kano

Duk Labarai
Hukumar tace fina-finai a jihar Kano ta sanar da haramta bukukuwan Kauyawa da ake yi a faɗin jihar, a wani mataki na ƙarfafa kyawawan ɗabi'u tsakanin al'umma da kuma bin doka. Shugaban hukumar, Abba El-Mustapha ne ya sanar da matakin yayin wani taron manema labarai a yau Asabar, inda ya ce an kuma dakatar da dukkan wuraren gudanar da bukukuwan wato 'event centers' har sai abin da hali ya yi. El-Mustapha ya ce wannan mataki da suka ɗauka wani ɓangare ne da hukumar ke yi na ƙarfafa ɗabi'u masu kyau tsakanin al'umma. "Wannan mataki da muka ɗauka yana cikin tsarin dokar hukumar mu wanda majalisar jiha ta yi wa garambawul da kuma gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanya wa hannu," in ji El-Mustapha. Ya ƙara da cewa dokokin sun bai wa hukumar tace finai-finai ta jihar Kano damar kula da kuma...
Laftanar Buba Hamza Kènan Da Aka Ķàšhè A Fagen Dàga A Jihar Borno Bayan Kwanaki Kadan Da Kara Masa Girma A Gidan Sojà

Laftanar Buba Hamza Kènan Da Aka Ķàšhè A Fagen Dàga A Jihar Borno Bayan Kwanaki Kadan Da Kara Masa Girma A Gidan Sojà

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Laftanar Buba Hamza Kènan Da Aka Ķàšhè A Fagen Dàga A Jihar Borno Bayan Kwanaki Kadan Da Kara Masa Girma A Gidan Sojà Allah Ya gafarta masa.
Gwamnatin Kano ta kama awaki da su ke cinye bishiyoyin da aka dasa a sabbin titunan da ake ginawa

Gwamnatin Kano ta kama awaki da su ke cinye bishiyoyin da aka dasa a sabbin titunan da ake ginawa

Duk Labarai
Gwamnatin Kano ta kama awaki da su ke cinye bishiyoyin da aka dasa a sabbin titunan da ake ginawa. Ma'aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi ta Jihar Kano ce ta kama wasu awaki da su ke cinye bishiyoyin da aka dasa don ƙawata sabbin titunan da ake yi a cikin birnin jihar. Kwamishinan ma'aikatar, Dr. Dahir M. Hashim ne ya baiyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Kano, inda ya ce tuni aka kama wajin aka daure su a ofishin Ƴansanda na Zone 1. Ya zargi al'umma da sakin wani sakaka, inda ya ce gwamnati ba za ta lamunci hakan ba. "Mun samu rahotanni cewa wasu suna barin awaki suna yawo suna cin sababbin bishiyoyin da muka dasa. "Ina so jama'a su sani cewa wannan abu ne da ba za mu lamunta ba. A halin yanzu, mun kama wasu awaki suna cin bishiyoyin da aka dasa kuma mun ɗauresu a Zon...
Haziƙin Ɗalibin Jami’ar Umaru Musa Yar’adua Da Ke Katsina Ya Rasu

Haziƙin Ɗalibin Jami’ar Umaru Musa Yar’adua Da Ke Katsina Ya Rasu

Duk Labarai
INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN. Haziƙin Ɗalibin Jami'ar Umaru Musa Yar'adua Da Ke Katsina Ya Rasu Allah Ya Yi Wa Haziƙin Matashin Ɗalibin Jami'ar Umaru Musa Yar'adua Dake Katsina, Dake Nazarin Dubarun Mulki, Surajo Muhammad Masari Rasuwa, Yau Juma'a. An Yi Jana'izarsa Kamar Yadda Addinin Musulunci Ya Tanada A Tsaunin Tinya Dake Karamar Hukumar Kafur A Jihar Katsina. Allah Ya Jikansa Da Rahama! Daga Jamilu Dabawa, Katsina
Budurwa ta mùtù a dakin Saurayinta bayan da ta kai masa ziyara

Budurwa ta mùtù a dakin Saurayinta bayan da ta kai masa ziyara

Duk Labarai
Wata Budurwa a jihar Delta me suna Brenda ta mutu bayan da ta kaiwa Saurayinta Ziyara. Budurwar ta hadu da saurayin me suna Emmypounds ne a kafar Tiktok inda kuma ya gayyaceta zuwa dakinsa kuma ta amince. Saidai tun bayan data ziyarceshi ba'a kara jin duriyarta ba, dan hakane wata kawarta dake da bayanan shiga shafinta na Tiktok ta shiga ta duba taga inda tace. Ko da aka tambayi saurayin, yace ta kwanta rashin Lafiyane aka kaita Asibiti, saidai an gano ashe karyane mutuwa ta yi.
Kuma Dai: Shugaban Kungiyar dalibai ya maka dan shugaban kasa, Seyi Tinubu da Shugaban DSS da shugaban NTA a kotu inda yake neman a biyashi diyyar Naira Biliyan 38.3

Kuma Dai: Shugaban Kungiyar dalibai ya maka dan shugaban kasa, Seyi Tinubu da Shugaban DSS da shugaban NTA a kotu inda yake neman a biyashi diyyar Naira Biliyan 38.3

Duk Labarai
Shugaban kungiyar daliban Najeriya, Comrade Atiku Abubakar Isah, ya maka dan shugaban kasa, Seyi Tinubu da shugaban gidan talabijin na kasa, NTA, da shugaban hukumar tsaron farin kaya, DSS a kotu inda yake neman a biyashi diyyar Naira Biliyan 38.3. Ya kuma nemi a sakeshi daga tsaron da ake masa na tsawon kwanaki 14 wanda ya bayyana da cewa garkuwa ce aka yi dashi. Hakanan ya kuma bayyana cewa yana neman kotu ta dakatar da bata masa sunan da ake yi, inda yace kuma tsaron da akw masa an take hakkinsa na walwala kamar yanda Kudin tsarin mulkin Najeriya ya baiwa kowane dan kasa damar yi. Dan haka yake neman kotun tarayya dake Abuja ta bi mai hakkinsa, ya shigar da karar ne ta hannun lauyansa, Ugwueze I. Oduegbu da R.O. Ifebhor. An dai kama Kwamared Isa ne bayan da ya zargi Dan shug...
Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya soki kasashen Larabawa saboda karrama Shugaban kasar Amurka Donald Trump yayin da akewa Falasdiynawa Kìsàn Kiyashi

Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya soki kasashen Larabawa saboda karrama Shugaban kasar Amurka Donald Trump yayin da akewa Falasdiynawa Kìsàn Kiyashi

Duk Labarai
Babban malamin Addinin Islama, Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya soki kasashen Larabawa inda ya kirasu da munafukai saboda yanda suka tarbi shugaban kasar Amurka, Donald Trump suka bashi kudade na fitar hankali dan ya je ya zuba jari a kasarsa. Kasashen da Trump ya je sune Saudiyya, Qatar, da UAE. https://twitter.com/el_uthmaan/status/1923238869039726928?t=RVrz9PM8VPKMldyHE70bXA&s=19 Sheikh Gumi yace wannan kudade da suka baiwa Amurka, kamar sun baiwa Israela ne yace dan ba zaka raba Israela da Amurka ba. Yace malaman kuma da suka yi shiru to suna da raunin Imanine.
An kama dan wasan Real Madrid da yiwa karamar yarinya fyàdè

An kama dan wasan Real Madrid da yiwa karamar yarinya fyàdè

Duk Labarai
'Yan wasan Real Madrid 4 ciki hadda Raul Asencio zasu iya fuskantar hukunci bayan yada Bidiyon badala da wasu mata biyu ciki hadda wata karamar yarinya wadda shekarunta basu kai 18 ba. Alkalin dake shari'ar yace ya kammala nazarin Bidiyon wanda aka dauka wani wajan shakatawa. Alkalin yace matan dake cikin Bidiyon daya shekarunta 18 dayar kuma shekarunta 16. Alkalin yace laifukan da ake zargin 'yan wasan dasu sune yada Bidiyon da aka dauka a sirce ba tare da izinin wadandake cikin Bidiyon ba da kuma amfani da karamar yarinya
Gwamnatin jihar Bauchi ta tallafawa tubabbun mata 100 Karuwai da koyon sana’a

Gwamnatin jihar Bauchi ta tallafawa tubabbun mata 100 Karuwai da koyon sana’a

Duk Labarai
Gwamnatin jihar Bauchi ta tallafawa tubabbun mata karuwai da masu shaye-shaye da suka daina da kayan sana'a dan dogaro da kai. An tattaro matanne daga karamar hukumar Misau ta jihar ta Bauchi wanda ke karuwanci da shaye-shaye inda aka tallafa musu a karkashin tsarin Better Life Restoration Initiative (BERI). Daya daga cikin matan da suka amfana da wannan lamari ta bayyana cewa ta samu canjin rayuwa a yanzu an bata sana'a amma tace matsalar daya ce shine har yanzu ana hantararsu.