Kalli Bidiyon yanda Mutum 19 suka ràsì bayan tawagar ƴanwasan Kano sun yi hatsari
Motar da ke ɗauke da ƴanwasan Kano da masu horar da su a gasar wasanni ta ƙasa wato National Sport Festival ta Najeriya ta yi hatsarin a hanyar komawa gida, inda rahotanni suka ce mutum 19 daga cikinsu sun rasu, sannan wasu sun jikkata.
Lamarin ya faru kimanin kilomita 50 zuwa Kano a yau Asabar bayan motar ta taso daga jihar Ogun da ke kudu maso yammacin ƙasar bayan an kammala wasannin a ranar Juma'a.
https://twitter.com/SaharaReporters/status/1928797578813984970?t=-7LG2F0J5GMJapK0JxPhMg&s=19
Ibrahim Umar Fage shugaban riƙo na hukumar wasanni ta jihar Kano ya tabbatar wa BBC da aukuwar lamarin, inda ya ce, "ƴanwasanmu sun kwana a Abuja ne da safe sai suka kama hanyar komawa gida. A kusa da Dakatsalle suka yi hatsari. Motar ta faɗa wata gada da ke kusa da Ciromawa. Aƙalla mut...







