Shugaban Jam'iyyar APC Na Kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje Ya Karɓi Bakuncin Shahararren Mawaƙin Siyasa, Dauda Kahutu Rarara A Gidansa Dake Abuja Da Yammacin Jiya Lahadi.
Daga Jamilu Dabawa
Rahotanni sun bayyana cewa Jimullar Naira Tiriliyan 7 ne gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta samu bayan cire tallafin Man fetur.
Saidai duk da haka, talakan Najeriya bai shaida ba inda ake ci gaba da fama da tsadar rayuwa da Talauci da matsalar tsaro.
Wadannan karin kudade da aka samu an karawa gwamnatoci a kowane mataki watau Tarayya, jiha da kananan hukumomi yawan kudaden da suke samu.
Sannan an sayo motoci masu amfani da Gas me Arha sannan an rabawa talakawa kudaden Tallafi sannan an kashe makudan kudade wajan gyaran matatun man fetur din da muke dasu amma duk da haka babu Alamar shaida hakan ga Talaka.
Yawanci kasuwanci da kamfanoni musamman kanana da matsakaita sun rage ma'aikata wasu ma sun kulle inda Bankin Duniya, da IMF ke kara tabbatar da cewa akwai mutane ...
Rahotanni sun bayyana cewa rashin jituwa da rikici ya barke tsakanin Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde da Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike.
Rahoton yace An kafa kwamiti dan yin sulhu tsakanin su amma Wike ya fice daga sulhun da ake yi inda ya ke zargin Gwamna Seyi Makinde da Gwamnan Jihar Enugu da hannu a rikicin da ya mamaye jam'iyyar.
Hakan na zuwane a yayin da jam'iyyar ke shirin yin babban taronta na masu ruwa da tsaki ranar 27 ga watan Mayu da muke ciki.
Tuni Kwamitin Amintattu na jam'iyyar suka kira taron gaggawa a yau, Litinin dan shawo kan matsalar.
A zaben shekarar 2023 dai Gwamna Seyi Makinde da Nyesom Wike na daga cikin gwamnoni 5 da suka hadewa Atiku ka sukace ba zasu goyi bayansa ba.
Wani abin ban mamaki da ya faru shine yanda aka gano wasu bata gari dakewa kananan yara maza wayau suna aika musu hotunansu tsirara.
Yaran dai nantsakanin shekaru 14 zuwa 21 ne.
Wasu daga cikinsu da saninsu ake aikata hakan saboda ana basu kudi, wasu kuma ba da saninsu ba saboda an musu wayau ne.
Jaridar Punchng ta yi bincike akan lamarin kuma ta gano cewa ana amfani da kafafen sada zumunta ne irin su X ne wajan aikata wannan masha'a.
Saidai ana ta kulle irin wadannan shafuka amma masu aikata wannan masha'a sai su kara bude wasu.
Wasu yaran da a yanzu sun girma amma ana da Bidiyonsu suna cikin fargaba saboda a yanzu ana ta yada Bidiyon a kakafen sada zumunta wanda hakan yana zamar musu Abin Kunya.
An yi kira ga gwamnati, da ta dauki matakai kan lamarin dan tsafta kafafen...
Tsohuwar tauraruwar fina-finan Hausa, Mansurah Isah ta bayyana dalilin da yasa Tsohon Mijinta, Sani Danja ya aureta.
Mansurah ta bayyana hakanne a wata hira da BBChausa ta yi da ita inda take cewa ita ba 'yar Iska bace.
Tace da ita 'yar iska ce da Sani Danja bai Aureta ba.
Kalli Bidiyon hirar:
https://www.tiktok.com/@musaddeeqq_haysam/video/7508388274101046534?_t=ZM-8wfWYscDyDt&_r=1
Mansurah dai ta tabbatar da cewa Aurenta na biyu ya mutu ne a hirar da BBC inda tace mijin nata yaudararta yayi.
Rahotanni daga Kano sun ce fada da ya barke tsakanin matasan kauyukan Faruruwa dana Tarandai dake karamar hukumar Takai ta jihar yasa an yi asarar rai.
Lamarin ya farune a kasuwar garin Faruruwa ranar 23 ga watan Mayu da misalin karfe 7:45 p.m.
An yi fadanne ranar Kasuwar garin inda aka kona runfunan Kasuwa da dama.
Rahoton yace wani me suna Sani Yunusa, 28 daga kauyen Toho Diribo dake karamar hukumar Takai ya je wajan budurwarsa dake kauyen Tarandai.
Saidai matasa sun afka masa da duka da itace.
Tuni aka aika da jami'an tsaro yankin dan su kwantar da tarzomar.
Rahoton yace ana kokarin kama wadanda suka fara tada tarzomar dan yi musu hukunci.
TURKASHI: An Baiwa Hammàtà Iska A Dakin Taron Hadakar Jam'iyyun Adawa Da Su Atiku Da Peter Obi Suke Gudanarwa.
https://twitter.com/abdullahayofel/status/1926682793477640481?t=jnOygvF_fT_QW8DOci488A&s=19
Rahoton yace wakilai daga Jihar Jigawa ne suka tayar da fitinar.
Bidiyon matar aure ya bayyana a kafafen safa zumunta inda aka ganta tana lalata da wani mutum.
Matar dai ta fito ne daga jihar Anambra.
Lamarin yasa matan yankin da take suka fito zanga-zanga inda suke cewa tana kokarin kwace musu maza.
Matar dai da aka yi hira da ita tace taĺauci ne yasa ta ta aikata hakan.
Tace kuma cin zarafin da mijinta yake mata ya taimaka sosai wajan halin data samu kanta.
Rundunar ƴansandan Najeriya ta samu nasarar hada matashiyar ƴar gwagwarmayan nan, Hamdiyya Shareef da mahaifan ta a Sakkwato bayan batan da ta yi a ranar Laraba.
Hamdiyya, wadda ta shahara wajen fafutukar ilimin ‘yan mata da kare hakkin matasa, ta bace a wani hali da ba a san ainihin dalilinsa ba, lamarin da ya tayar da hankulan mahaifan ta da dangin ta da masu goyon bayanta.
A cewar Rundunar ‘Yansanda ta Jihar Sokoto, hadin gwiwa da hanzarin tattara bayanan sirri ne suka taimaka wajen gano inda take cikin koshin lafiya. Kakakin rundunar ya yaba wa ‘yan kasa bisa hadin kan da suka bayar tare da jaddada kudirin rundunar na kare duk wani dan Najeriya, musamman matasa masu rauni.
‘Yan uwanta, cike da hawaye da farin ciki, sun bayyana godiya ga ‘yan sanda da duk wanda ya tsaya musu a ...
Mawallafin jaridar Sahara reporters, Omoyele Sowore kuma dan siyasa ya bayyana cewa an riga an rubuta sakamakon zaben shekarar 2027.
Ya bayyana hakane a wata hira da kafar Vanguard ta yi dashi.
Inda yace abu daya kawai da 'yan Najeriya zasu yi shine su yi zanga-zanga dan samun zabe me kyau amma tsarin zaben da ake dashi bai da kyau
Kuma ya bayyana cewa, ba zai hada kai da Peter Obi ba a zaben shekarar 2027 ba.