Wednesday, May 13
Shadow
Kalli Bidiyo: Sadiya Kabala tace saurayinta yace kibarta ta yi yawa dan haka ta canja kalar abincin da take ci

Kalli Bidiyo: Sadiya Kabala tace saurayinta yace kibarta ta yi yawa dan haka ta canja kalar abincin da take ci

Duk Labarai
Tauraruwar fina-finan Hausa, Sadiya Kabala ta bayyana cewa, Saurayinta ya gaya mata cewa kibarta ta yi yawa. Tace dalili kenan da yasa ta canja kalar abincin da take ci. Ta nuna kalar abincin da ta koma ci da suka hada da kayan marmari da ganyen dan rage kiba. https://www.instagram.com/reel/DGV5MxtM-_k/?igsh=anl5ODg3ODF4bmhr https://www.instagram.com/reel/DGV5MxtM-_k/?igsh=anl5ODg3ODF4bmhr
Tsaka Mai Wuya: Har yanzu Atiku yaƙi karɓar katin zama ɗan Jam’iyyar ADC kan jin Jonathan zai koma PDP

Tsaka Mai Wuya: Har yanzu Atiku yaƙi karɓar katin zama ɗan Jam’iyyar ADC kan jin Jonathan zai koma PDP

Duk Labarai
Tsaka Mai Wuya: Har yanzu Atiku yaƙi karɓar katin zama ɗan Jam'iyyar ADC kan jin Jonathan zai koma PDP Tsohon Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar yaƙi ya karɓi katin zama ɗan Jam'iyyar ADC, a yayinda ake ci gaba da jita-jitar cewa tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan zai yi takara a shekarar 2027. Atiku, wanda a ƴan kwanakin baya ya fita daga jam'iyyar PDP bayan ɗaukar tsawon lokaci ana rigingimu, an tsara zai karɓar katin jam'iyyar ADC. Atiku dai zai karɓi katin jam'iyyar ADC a garin sa na Jada da ke ƙaramar hukumar Jada ta Adamawa, an tsara cewa zai karɓi katin jam'iyyar a ranar Laraba 6 ga watan Agusta, amma aka ɗage karɓar katin ba tare da wani bayani ba. Daga Usman Salisu
Kalli Bidiyo: Na jawa kaina, Tunda nace ina son Sheikh Salihu Zaria, duk masu nema na sun tsere>>Murja Kunya

Kalli Bidiyo: Na jawa kaina, Tunda nace ina son Sheikh Salihu Zaria, duk masu nema na sun tsere>>Murja Kunya

Duk Labarai
Tauraruwar fina-finan Hausa, Murja Kunya ta bayyana cewa, tun da ta fito ta bayyana cewa tana son babban malamin Addinin Islama, Sheikh Salihu Zaria duk zawarawanta suka tsere. Murja ta ce su yi hakuri su dawo da wasa take. https://www.tiktok.com/@murjakunya0/video/7536714068321750277?_t=ZS-8ylIECfsaZc&_r=1 A baya dai, Murja ta bayyana cewa idan Sheikh Salihu Zaria bai aureta ba, zata shiga Duniya, Lamarin da ya dauki hankula sosai.
Kalli Bidiyo: Kuskuren Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf na cewa “Kullu Nafsin Zalikatul Maut” ya jawo cece-kuce sosai

Kalli Bidiyo: Kuskuren Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf na cewa “Kullu Nafsin Zalikatul Maut” ya jawo cece-kuce sosai

Duk Labarai
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf a yayin da yake mika sakon ta'aziyyarsa kan rasuwar daya daga cikin hadimansa yayi kuskuren fadin Kullu Nafsin za'ikatul Maut. Gwamnan yace, Kullu nafsin Zalikatul Maut. Lamarin dai ya jawo cece-kuce sosai inda wasu ke masa uzuri, wasu kuwa raha suka mayar da abin. https://www.tiktok.com/@gentlefarouq/video/7536135680326520069?_t=ZS-8yky8Ge6ByC&_r=1
Allah Sarki, Kalli Bidiyo, Rahama Sadau ta bayyana babban dana saninta, bayan aure

Allah Sarki, Kalli Bidiyo, Rahama Sadau ta bayyana babban dana saninta, bayan aure

Duk Labarai
A jiyane aka daura auren Tauraruwar fina-finan Hausa, Rahama Sadau da angonta Ibrahim. Bayan daura auren, Dan uwanta, Haruna Sadau ya bayyana cewa, tun kamin mahaifinsu ya bar Duniya yake cewa yana da burin ganin 'ya'yansa sun yi aure. Yace dan hakane bayan rasuwarsa duka suka sha Alwashin fito da mazajen aure cikin manemansu. Yace sai aka fara da Rahama. Yace abun kawai dake damun Rahama Sadau shine da mahaifinta bai ga aurenta da ranshi ba. Kallu Bidiyon hirar anan https://www.tiktok.com/@aliyu_haidar_backup/photo/7536735561483144504?_d=secCgYIASAHKAESPgo8uDpifjlBHENJQdMDEpbZZ3UBx7ghuoD3XXn%2B9eHdvFPpS2b%2BMtgFeUrjZ5Nf43vioTCE2W1P67FUnWtKGgA%3D&_r=1&_svg=1&aweme_type=150&checksum=ca96c2a241e5d319e322c30e680149a91979fa89381e849314a91a3c22aee0f4&link_re...
Idan kuka zabeni shugaban kasa, a cikin wata daya zan magance rashawa da cin hanci idan kuma na kasa yin hakan zan sauka>>Inji Rotimi Amaechi

Idan kuka zabeni shugaban kasa, a cikin wata daya zan magance rashawa da cin hanci idan kuma na kasa yin hakan zan sauka>>Inji Rotimi Amaechi

Duk Labarai
Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya bayyana cewa, idan ya zama shugaban kasa, zai magance matsalar rashawa da cin hanci a cikin wata daya. Yace amma ida ya kasa, zai sauka daga shugabancin. Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi a X. Ya kara da cewa, kuma zai canja kundin tsarin mulkin Najeriya. Sannan yace yasan ta inda zai wa Tinubu illa ya ci zabe idan aka zabeshi a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC