An kwashe maniyyatan jihohin Najeriya 12 – NAHCON
Ma'aikaar kula da aikin hajji ta Najeriya ta bayyana cewa an kwashe maniyyata aikin hajji daga jahohi 12 na ƙasar, waɗanda yawansu ya kai mutum 25,702.
Jihohin su ne Osun da Oyo da Adamawa da Filato da Ekiti Imo da Legas da Abiya kuma Edo.
Hukumar alhazan ta ce an kwashe wannan adadin ne bayan sawu 63 daga Najeriya zuwa Saudiyya a cikin kwana goma.
Kawo yanzu dai hukumar ta ce babu wata matsala da aka fuskanta tun bayan soma jigilar maniyyatan, inda a wannan shekarar hukumomin suka ce mutum 43,000 ne za su sauke farali a ƙasar ta Saudiyya domin gudanar da babbar ibadar ta Musulmai.
A ckin wata sanarwa da jami'in gudanarwar hukumar na ƙasa, Ibrahim Muhammad ya sanya wa hannu, ya bayyana cewa matakan da hukumar ta ɗauka da ke kan tsari sun taimaka matuƙa inda jigilar maniyyatan d...








