“Wallahi yanzu haka in da zan bayar da duk abin da na mallaka don in koma gida zan yi hakan, idan na koma gida sai na zuba ruwa a ƙasa na sha, na yi sujada don gode wa Ubangiji.” Inji Matashin Najeriya dake shan Wahala A Kasar Libya
"Wallahi yanzu haka in da zan bayar da duk abin da na mallaka don in koma gida zan yi hakan, idan na koma gida sai na zuba ruwa a ƙasa na sha, na yi sujada don gode wa Ubangiji."
Wannan ne kalami na ƙarshe da Mukhtar ya faɗa min a tattaunawar da na yi da shi game da tafiyarsa da kuma zaman da yake yi yanzu haka a Libya.
Yana daga cikin dubban matasan da ke ficewa daga ƙasashen Yammacin Afirka domin zuwa neman rayuwa mai kyau a ƙasashen Turai ta ɓarauniyar hanya, waɗanda akasarinsu kan faɗa tarkon ƙungiyoyin masu riƙe da makamai a ƙasashen yankin arewacin Afirka.
Da dama daga cikinsu kan gamu da ajalinsu, ko dai a kan hanyarsu ta tafiya ko kuma a lokacin da suka tsinci kansu a ƙasashe irin Libya inda ƙungiyoyin ƴanbindiga ke yaƙi da juna sanadiyyar raunin hukumomi.
Su kuma waɗan...








