Monday, December 15
Shadow
Allah kasa kada in kai matsayin da sai Annabi(Sallallahi Alaihi Wasallam) ya cece ni Ranar tashin Qiyama>>Inji Dr. Hussain Kano

Allah kasa kada in kai matsayin da sai Annabi(Sallallahi Alaihi Wasallam) ya cece ni Ranar tashin Qiyama>>Inji Dr. Hussain Kano

Duk Labarai
Malamin Addinin Islama, Dr. Hussain Kano ya roki Allah cewa Allah sa kada ya kai matsayin da sai Annabi (Subhanallahi Alaihi Wasallam) ya ceceshi ranar Tashin Qiyama. Yayi inkari ga masu neman ceton Annabi a wajan Maulidi inda yace hakan shirka ce me iya kai mutum ga wuta wanda kuma Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ba za iya ceton me yin hakan ba. https://www.tiktok.com/@dr.hussainkano5/video/7583771231518772491?_t=ZS-92Dvt4alenA&_r=1
Naira milo 150 ko takalmi ba zata sai min ba>>Inji Primate Elijah Ayodele

Naira milo 150 ko takalmi ba zata sai min ba>>Inji Primate Elijah Ayodele

Duk Labarai
Malamin Kirista, Primate Elijah Ayodele ya bayyana cewa, Naira Miliyan 150 ko takalmi ba zata sai mai ba. Ya bayyana hakane a cocinsa sannan a matsayin martani ga Ministan wuta, Bayo Adelabu wanda ke son tsayawa takarar gwamnan jihar Oyo. Shi dai Ministan ya zargi malamin da cewa ya nemi ya bashi Naira Miliyan 150 ya masa Addu'ar neman nasara amma ya kiya shine ya koma yana bata masa suna. Saidai Faston yace kawai Bayo Adelabu yaga ba zai yi nasara bane a zaben me zuwa shine yake soki burutsu.
A tarihi wadanda basu da Addini ne masu bautar Gumaka ke binne gàwàrsù a cikin Akwatin gawa na Gwal, ban san inda Kiristoci suka samo hakan a addinin su ba>>Inji Malam Bashir Ahmad

A tarihi wadanda basu da Addini ne masu bautar Gumaka ke binne gàwàrsù a cikin Akwatin gawa na Gwal, ban san inda Kiristoci suka samo hakan a addinin su ba>>Inji Malam Bashir Ahmad

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Tsohon Hadimin Shugaban kasa, Malam Bashir Ahmad ya bayyana cewa a Tarihi, Wanda basu da addini masu bautar Gumaka ne ke binne gawarwakinsu a cikin akwatin gawa na Zinare. Yace a dokokin Addinin Kiristoci babu inda aka ce a binne gawa a cikin akwatin Zinare. Ya bayyana hakane a matsayin Martani ga wani fasto a jihar Bayelsa da ya binne Mahaifiyarsa a cikin akwatin gawa na Naira Miliyan 150 wanda aka ce da gwal aka yishi. https://twitter.com/BashirAhmaad/status/200018623266445...
Sarkin Wakar Daura ne aka baiwa Rarara ba Sarkin wakar kasar Hausa ba>>Inji Babban Yaron Naziru Sarkin Waka, Abba C Sale

Sarkin Wakar Daura ne aka baiwa Rarara ba Sarkin wakar kasar Hausa ba>>Inji Babban Yaron Naziru Sarkin Waka, Abba C Sale

Duk Labarai
Babban yaron Naziru Ahmad Sarkin Waka, Abba C Sale ya bayyana cewa, Sarautar Sarkin Wakar kasar Hausa da aka baiwa Rarara ba ta inganta ba. Yace sarkin Daura ne ya bayar da Sarautar dan haka a Kano su ba zasu kira Rarara da Sarkin Wakar Kasar Hausa ba. Yace Sarkij wakar Daura da Katsina ne Rarara. https://www.tiktok.com/@abbacsale2/video/7582265183674961172?_t=ZS-92DX9Q8IjC4&_r=1 Hakan na zuwane jim kadan bayan da Me Martaba sarkin Daura, Umar Farouk Umar ya nada Rarara a matsayin sarkin Wakar kasar Hausa.
Kalli Bidiyon Abin Mamaki, An zargi cewa an saka Fitilun bikin Kirsimeti a wani Masallaci dake kudancin Najeriya

Kalli Bidiyon Abin Mamaki, An zargi cewa an saka Fitilun bikin Kirsimeti a wani Masallaci dake kudancin Najeriya

Duk Labarai
Wani daga kudancin Najeriya yayi zargin cewa, an saka fitilun bikin Kirsimeti a masallaci. Yayi Bidiyon masallacin inda ya wallafa a shafinsa. Saidai da yawa sun ce basu yadda inda wasu ke cewa dama saidai a kudancin Najeriyar ne hakan zai iya faruwa. https://www.tiktok.com/@lucent0019/video/7583271209534622984?_t=ZS-92DVwAuKVrF&_r=1
Kalli Bidiyon: Sojan Najeriya yace duk dan Najeriyar dake goyon bayan Burkina Faso bai san abinda yake ba

Kalli Bidiyon: Sojan Najeriya yace duk dan Najeriyar dake goyon bayan Burkina Faso bai san abinda yake ba

Duk Labarai
Sojan Najeriya yace duk dan Najeriyar dake goyon bayan kasar Burkina Faso kan abinda ke faruwa a tsakaninta da Najeriya bai san abinda yake ba. Sojan ya bayyana hakane yayin da kasar Burkina Faso ke ci gaba da rike sojojin Najeriya 11 data kama bisa zargin sun shiga sararin samaniyar ta ba bisa ka'isa ba. Sojan yace ta ko ina Najeriya tafi kasar Burkina Faso dan haka mu ba sa'anninta bane. https://twitter.com/General_Somto/status/2000092438313009508?t=jO5vE27mTP4E3u78tn22qg&s=19