Saturday, December 20
Shadow
Ban san ta yaya suke iya bacci ba yayin da ‘yan tà’àddà ke kàshè mutane>>Atiku ya koka kan matsalar tsaro, yace shuwagabannin da suka zo bayan mulkinsu shi da Obasanjo ne suka kawo matsalar tsaro

Ban san ta yaya suke iya bacci ba yayin da ‘yan tà’àddà ke kàshè mutane>>Atiku ya koka kan matsalar tsaro, yace shuwagabannin da suka zo bayan mulkinsu shi da Obasanjo ne suka kawo matsalar tsaro

Duk Labarai
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana cewa, shuwagabannin Najeriya da suka zo bayan Obasanjo ne ke da Alhakin dawowar Kungiyar Bòkò Hàràm. Ya bayyana hakane a Abuja a yayin ziyarar da wasu 'yan siyasa daga jihar Kogi suka kai masa. Yace kungiyar ta fara bayyanane a shekarar 2002 a jihar Yobe Yace suna sumun labari, Obasanjo ya aika aka kirashi yace mai ya yake ganin za'a bullowa wannan lamari? Sai yace masa a kira shuwagabannin tsaro a basu lokaci su gama da kungiyar, idan suka kasa sai a sauke su a nada wasu. Yace haka kuwa aka yi kuma aka murkushe kungiyar. Yace bayan sun sauka Mulki ne wanda suka hau suka yi sakaci kungiyar ta dawo.
Gwamnati ta bayyana jihohin da suka fi fama da tsadar kayan Abinci a Najeriya, Duba kaga jiharka na ciki?

Gwamnati ta bayyana jihohin da suka fi fama da tsadar kayan Abinci a Najeriya, Duba kaga jiharka na ciki?

Duk Labarai
Hukumar NBS dake kula da kididdigar alkaluma a Najeriya ta fitar da bayanan Alkaluma kasuwanci da kayan Masarufi na watan maris. Hukumar tace alkaluma sun nuna makin farashin kayan masarufi ya tsaya a mataki na kaso 23.71 cikin 100. Hakan na nufin farashin kaya masarufi sun yo kasa idan aka hada da alkaluma baya da aka samu. Saidai Jihohin Enugu, Kebbi, Niger, Benue, Ekiti, Nassarawa, Zamfara, Delta, Gombe, Sokoto, da babban birnin tarayya Abuja, nasu Alkaluman sama suka yi. Rahoton yace wadannan jihohi alkaluansu sun nuna suna da maki 30 cikin 100 na hauhawar farashin kayan masarufi.
Bidiyo: Ya kamata a bar mutanen Najeriya su rike màkàmài dan baiwa kansu kariya>>Ado Doguwa

Bidiyo: Ya kamata a bar mutanen Najeriya su rike màkàmài dan baiwa kansu kariya>>Ado Doguwa

Duk Labarai
Dan majalisar Wakilai daga jihar Kano, Alhassan Ado Doguwa ya nemi a baiwa 'yan Najeriya dama su rike makamai dan baiwa Kansu Kariya. Ya bayyana hakane a farfajiyar majalisar Wakilai inda yace idan jami'an tsaro sun kasa, kamata yayi a baiwa 'yan Najeriya damar kare kansu. https://twitter.com/General_Somto/status/1922760426145620359?t=W744pEzgJuQRYfcSdcw8pg&s=19 A baya dai Tsohon Ministan matasa da wasanni, Solomon Dalung da Lauya dan fafutuka, Deji Adeyanju, da Janar T.Y Danjuma duk sun nemi a baiwa 'yan Najeriya damar daukar Makamai dan kare kansu
Yaduwar Gurbatacciyar Shinakafa me kisa a Najeriya ta saka fargaba

Yaduwar Gurbatacciyar Shinakafa me kisa a Najeriya ta saka fargaba

Duk Labarai
Hankula sun tashi a jihohin Ogun da Legas saboda farfagandar yaduwar shinkafa me guba dake kisa. 'Yan uwa da dangi sun rika aikawa jina sakonni musamman ta WhatsApp inda ake gargadinsu da cin shinkafa, ana yada cewa, wata mata ce 'yar kasuwa aka kwacewa Shinkafar aka shigo da ita Najeriya inda ita kuma ta yi tsafi kan duk wanda ya ci ya mutu. Rahoton yace masu yada wannan labari sunce har wasu sojoji da jami'an Kwastam sun rasu sanadiyyar wannan shinakafa, kamar yanda Punchng ta ruwaito. Hakanan rahoton yayi ikirarin cewa, Mutane 70 sun mutu sanadiyyar shinkafar. Iyaye har makaranta sun rika bin 'ya'yansu suna gargadin masu abinci kada su sayarwa da 'ya'yansu Abinci. Saidai Tunu hukumomin Kwastam na jihohin Ogun da Legas suka musanta wannan zargi. Sun ce babu wata shinka...
Majalisar tarayya za ta yi bincike kan matsalolin da aka samu a JAMB ta bana

Majalisar tarayya za ta yi bincike kan matsalolin da aka samu a JAMB ta bana

Duk Labarai
Majalisar tarayya za ta yi bincike kan matsalolin da aka samu a JAMB ta bana Majalisar Wakilai ta yanke shawarar gudanar da bincike kan kuskuren fasaha da ya shafi sakamakon Jarrabawar UTME na shekarar 2025. Majalisar ta amince da wannan kuduri ne a zaman ta na ranar Alhamis, bayan ta amince da kudurin gaggawa mai muhimmancin jama’a da dan majalisa daga jihar Osun, Adewale Adebayo, ya gabatar.
Muzanta Naira: Kotu ta yanke wa wani dan Tiktok hukunci a Kaduna

Muzanta Naira: Kotu ta yanke wa wani dan Tiktok hukunci a Kaduna

Duk Labarai
Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC reshen Kaduna ta samu nasara bayan da kotu ta yanke hukunci ga wani a mai amfani da shafukan Tiktok da Instagram, Muhammad Kabir. An gurfanar da wanda ake zargin ne a gaban Mai Shari’a R.M. Aikawa na Babban Kotun Tarayya dake zamanta a Kaduna, bisa laifin wulakanta kudin Naira. Shugaban sashen hulda da jama’a na EFCC, Dele Oyewale, ya bayyana cewa an kama Kabir ne a ranar Talata, 29 ga Afrilu, 2025 a Tudun Wada, jihar Kaduna, bayan ya wallafa wani bidiyo a shafukansa na Tiktok da Instagram (@youngcee0066), yana watsar da takardun kudi na Naira a ƙasa, yana taka su da kafa, tare da furta wasu kalmomi cikin harshen Hausa yana kalubalantar EFCC da ta zo ta kama shi a inda aka san yana zaune. An kama shi bisa karya dokar Babban Bankin Najer...
Majalisar wakilai na son a maida yin zaɓe ya zama wajibi ga ƴan Nijeriya

Majalisar wakilai na son a maida yin zaɓe ya zama wajibi ga ƴan Nijeriya

Duk Labarai
Majalisar wakilai na son a maida yin zaɓe ya zama wajibi ga ƴan Nijeriya Wani ƙudiri da ke neman maida yin zaɓe ya zama wajibi ga ƴan Nijeriya ya tsallake karatu na biyu a majalisar wakilai. Ƙudurin, wanda shugaban majalisar, Tajuddeen Abbas ya ɗauki nauyi, ya tsallake karatu na biyu bayan an yi wata zazzafar muhawara a zauren majalisar a yau Alhamis.