Sunday, December 21
Shadow
Laftanar Buba Hamza Kènan Da Aka Ķàšhè A Fagen Dàga A Jihar Borno Bayan Kwanaki Kadan Da Kara Masa Girma A Gidan Sojà

Laftanar Buba Hamza Kènan Da Aka Ķàšhè A Fagen Dàga A Jihar Borno Bayan Kwanaki Kadan Da Kara Masa Girma A Gidan Sojà

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Laftanar Buba Hamza Kènan Da Aka Ķàšhè A Fagen Dàga A Jihar Borno Bayan Kwanaki Kadan Da Kara Masa Girma A Gidan Sojà Allah Ya gafarta masa.
Gwamnatin Kano ta kama awaki da su ke cinye bishiyoyin da aka dasa a sabbin titunan da ake ginawa

Gwamnatin Kano ta kama awaki da su ke cinye bishiyoyin da aka dasa a sabbin titunan da ake ginawa

Duk Labarai
Gwamnatin Kano ta kama awaki da su ke cinye bishiyoyin da aka dasa a sabbin titunan da ake ginawa. Ma'aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi ta Jihar Kano ce ta kama wasu awaki da su ke cinye bishiyoyin da aka dasa don ƙawata sabbin titunan da ake yi a cikin birnin jihar. Kwamishinan ma'aikatar, Dr. Dahir M. Hashim ne ya baiyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Kano, inda ya ce tuni aka kama wajin aka daure su a ofishin Ƴansanda na Zone 1. Ya zargi al'umma da sakin wani sakaka, inda ya ce gwamnati ba za ta lamunci hakan ba. "Mun samu rahotanni cewa wasu suna barin awaki suna yawo suna cin sababbin bishiyoyin da muka dasa. "Ina so jama'a su sani cewa wannan abu ne da ba za mu lamunta ba. A halin yanzu, mun kama wasu awaki suna cin bishiyoyin da aka dasa kuma mun ɗauresu a Zon...
Haziƙin Ɗalibin Jami’ar Umaru Musa Yar’adua Da Ke Katsina Ya Rasu

Haziƙin Ɗalibin Jami’ar Umaru Musa Yar’adua Da Ke Katsina Ya Rasu

Duk Labarai
INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN. Haziƙin Ɗalibin Jami'ar Umaru Musa Yar'adua Da Ke Katsina Ya Rasu Allah Ya Yi Wa Haziƙin Matashin Ɗalibin Jami'ar Umaru Musa Yar'adua Dake Katsina, Dake Nazarin Dubarun Mulki, Surajo Muhammad Masari Rasuwa, Yau Juma'a. An Yi Jana'izarsa Kamar Yadda Addinin Musulunci Ya Tanada A Tsaunin Tinya Dake Karamar Hukumar Kafur A Jihar Katsina. Allah Ya Jikansa Da Rahama! Daga Jamilu Dabawa, Katsina
Budurwa ta mùtù a dakin Saurayinta bayan da ta kai masa ziyara

Budurwa ta mùtù a dakin Saurayinta bayan da ta kai masa ziyara

Duk Labarai
Wata Budurwa a jihar Delta me suna Brenda ta mutu bayan da ta kaiwa Saurayinta Ziyara. Budurwar ta hadu da saurayin me suna Emmypounds ne a kafar Tiktok inda kuma ya gayyaceta zuwa dakinsa kuma ta amince. Saidai tun bayan data ziyarceshi ba'a kara jin duriyarta ba, dan hakane wata kawarta dake da bayanan shiga shafinta na Tiktok ta shiga ta duba taga inda tace. Ko da aka tambayi saurayin, yace ta kwanta rashin Lafiyane aka kaita Asibiti, saidai an gano ashe karyane mutuwa ta yi.
Kuma Dai: Shugaban Kungiyar dalibai ya maka dan shugaban kasa, Seyi Tinubu da Shugaban DSS da shugaban NTA a kotu inda yake neman a biyashi diyyar Naira Biliyan 38.3

Kuma Dai: Shugaban Kungiyar dalibai ya maka dan shugaban kasa, Seyi Tinubu da Shugaban DSS da shugaban NTA a kotu inda yake neman a biyashi diyyar Naira Biliyan 38.3

Duk Labarai
Shugaban kungiyar daliban Najeriya, Comrade Atiku Abubakar Isah, ya maka dan shugaban kasa, Seyi Tinubu da shugaban gidan talabijin na kasa, NTA, da shugaban hukumar tsaron farin kaya, DSS a kotu inda yake neman a biyashi diyyar Naira Biliyan 38.3. Ya kuma nemi a sakeshi daga tsaron da ake masa na tsawon kwanaki 14 wanda ya bayyana da cewa garkuwa ce aka yi dashi. Hakanan ya kuma bayyana cewa yana neman kotu ta dakatar da bata masa sunan da ake yi, inda yace kuma tsaron da akw masa an take hakkinsa na walwala kamar yanda Kudin tsarin mulkin Najeriya ya baiwa kowane dan kasa damar yi. Dan haka yake neman kotun tarayya dake Abuja ta bi mai hakkinsa, ya shigar da karar ne ta hannun lauyansa, Ugwueze I. Oduegbu da R.O. Ifebhor. An dai kama Kwamared Isa ne bayan da ya zargi Dan shug...
Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya soki kasashen Larabawa saboda karrama Shugaban kasar Amurka Donald Trump yayin da akewa Falasdiynawa Kìsàn Kiyashi

Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya soki kasashen Larabawa saboda karrama Shugaban kasar Amurka Donald Trump yayin da akewa Falasdiynawa Kìsàn Kiyashi

Duk Labarai
Babban malamin Addinin Islama, Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya soki kasashen Larabawa inda ya kirasu da munafukai saboda yanda suka tarbi shugaban kasar Amurka, Donald Trump suka bashi kudade na fitar hankali dan ya je ya zuba jari a kasarsa. Kasashen da Trump ya je sune Saudiyya, Qatar, da UAE. https://twitter.com/el_uthmaan/status/1923238869039726928?t=RVrz9PM8VPKMldyHE70bXA&s=19 Sheikh Gumi yace wannan kudade da suka baiwa Amurka, kamar sun baiwa Israela ne yace dan ba zaka raba Israela da Amurka ba. Yace malaman kuma da suka yi shiru to suna da raunin Imanine.
An kama dan wasan Real Madrid da yiwa karamar yarinya fyàdè

An kama dan wasan Real Madrid da yiwa karamar yarinya fyàdè

Duk Labarai
'Yan wasan Real Madrid 4 ciki hadda Raul Asencio zasu iya fuskantar hukunci bayan yada Bidiyon badala da wasu mata biyu ciki hadda wata karamar yarinya wadda shekarunta basu kai 18 ba. Alkalin dake shari'ar yace ya kammala nazarin Bidiyon wanda aka dauka wani wajan shakatawa. Alkalin yace matan dake cikin Bidiyon daya shekarunta 18 dayar kuma shekarunta 16. Alkalin yace laifukan da ake zargin 'yan wasan dasu sune yada Bidiyon da aka dauka a sirce ba tare da izinin wadandake cikin Bidiyon ba da kuma amfani da karamar yarinya
Gwamnatin jihar Bauchi ta tallafawa tubabbun mata 100 Karuwai da koyon sana’a

Gwamnatin jihar Bauchi ta tallafawa tubabbun mata 100 Karuwai da koyon sana’a

Duk Labarai
Gwamnatin jihar Bauchi ta tallafawa tubabbun mata karuwai da masu shaye-shaye da suka daina da kayan sana'a dan dogaro da kai. An tattaro matanne daga karamar hukumar Misau ta jihar ta Bauchi wanda ke karuwanci da shaye-shaye inda aka tallafa musu a karkashin tsarin Better Life Restoration Initiative (BERI). Daya daga cikin matan da suka amfana da wannan lamari ta bayyana cewa ta samu canjin rayuwa a yanzu an bata sana'a amma tace matsalar daya ce shine har yanzu ana hantararsu.
YANZU-YANZU: Shugaba Tinubu Ya Ƙaddamar Da Sabbin Jiragen Yaƙi Masu Saukar Angulu Samfurin Agusta A-109Power Attack

YANZU-YANZU: Shugaba Tinubu Ya Ƙaddamar Da Sabbin Jiragen Yaƙi Masu Saukar Angulu Samfurin Agusta A-109Power Attack

Duk Labarai
Shugaba Tinubu Ya Ƙaddamar Da Sabbin Jiragen Yaƙi Masu Saukar Angulu Samfurin Agusta A-109Power Attack A wani ɓangare na kokarin sabunta tsarin tsaron ƙasa. Shugaba Tinubu ya wakilta mataimakinsa Kashim Shettima wajen kaddamar da Sabbin jiragen yaƙin Shettima ya jaddada kudirin gwamnatin Najeriya na shiga dumu-dumu hannun cikin harkar inganta sabbin fasahohin aiyukan tsaron ƙasa domin wadata sojojin Najeriya da abubuwan da suka dace don tunkarar kalubalen tsaro. Gwamnatin ta kuma tabbatar wa da hukumar sojojin saman Najeriya ta NAF da cewa za ta sami ƙarin jiragen yaƙi sama 49 a cikin shekaru biyu masu zuwa. Shugaban ya kuma bukaci sojojin saman da su kiyaye ɗa'a da bin ƙa'idojin aiki don cin gajiyar manufofin aiki
Mummunan hàrì yayi sanadiyyar salwantar rayuka 10 a jihar Filato

Mummunan hàrì yayi sanadiyyar salwantar rayuka 10 a jihar Filato

Duk Labarai
Aƙalla mutum 10 ne aka kashe tare da sace shanu a wani sabon rikici da ya ɓarke a yankin ƙaramar hukumar Riyom a jihar Plateau. Sabon rikicin ya samo asali ne daga lalata amfanin gona da sace shanu da kashe wasu dabbobin, kamar yadda Gidan Talbijin na Channels a ƙasar ya ruwaito. Cikin wata sanarwa da rundunar soji ta 'Operation Safe Haven' ta fitar ta ce rikicin ya fara ne tun a ranar Litinin 12 ga watan Mayun da muke ciki, a lokacin da aka zargi wasu fusatattun matasa da kashe wasu shanu da suka yi zargin sun shiga gonakinsu a ƙauyen Dayan da ke ƙaramar hukumar ta Riyom. A ranar 13 ga watan ne kuma aka zargi wasu makiyaya da kai hari ƙauyen Danchindo domin ramuwar gayya, tare da kashe mutum huɗu kafin su tsare bayan zuwan jami'an tsaro. Haka kuma a ranar 14 aka zargi wasu mah...