Saturday, December 13
Shadow
‘Yan Najeriya na fama da wahala da Talauci sai mun tashi tsaye>>Akpabio ya gayawa Sauran Abokan aikinsa Sanatoci

‘Yan Najeriya na fama da wahala da Talauci sai mun tashi tsaye>>Akpabio ya gayawa Sauran Abokan aikinsa Sanatoci

Duk Labarai
Kakakin majalisar Dattijai, Godswill Akpabio ya jawo hankalin abokan aikinsa Sanatoci kan cewa 'yan Najeriya na cikin Wahala. Ya bayyana hakane a cikin jawabinsa na farko bayan komawar majalisar hutun da ta yi. Yace abinda ya kamata su mayar da hankali akai shine baiwa maganar tsaro, Inganta rayuwar mutane, da bangaren Makamashi. Yace ya kamata su taimakawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu wajan kawar da matsalar da wahalar da 'yan Najeriya suke ciki. r
2027 : Allah ya fada Mani cewa nine shugaban kasa mai zuwa>>Fasto Tunde

2027 : Allah ya fada Mani cewa nine shugaban kasa mai zuwa>>Fasto Tunde

Duk Labarai
2027 : Allah ne ya fad@ Mani cewa nine shugaban kasa mai zuwa__Fasto Tunde Daga Barista Nuraddeen Isma'eel "Babban malamin addinin kirista a Nijeriya Fasto Tunde, ya shaidawa mabiyan shi a cikin coci cewa, Allah ya fada mashi kuma yaji da kyau! Akan cewa shine shugaban kasar Nijeriya mai zuwa a zaben kakan bana mai zuwa ta 2027 . "Biyo bayan sanar da shi da Allah yayi, yasa baiyi kasa a gwiwaba na wurin zuge miliyan 100 a domin sayen fam din Takarar shugaban kasar Nijeriya."
Idan da gaske kake game da daina Shigo da abubuwa daga kasashen waje a rika Amfani da wanda aka yi a Najeriya, ka ajiye motocin Alfarma da kake hawa ka koma Amfani da motocin Innoson da ake kerawa a jihar Anambra>>Atiku ya gayawa Tinubu

Idan da gaske kake game da daina Shigo da abubuwa daga kasashen waje a rika Amfani da wanda aka yi a Najeriya, ka ajiye motocin Alfarma da kake hawa ka koma Amfani da motocin Innoson da ake kerawa a jihar Anambra>>Atiku ya gayawa Tinubu

Duk Labarai
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya cewa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu idan da gaske yake maganar daina amfani da abubuwan da aka kera a kasashen waje to ya daina amfani da motocin Alfarmar da yake hawa ya koma Amfani da motar Innoson da ake kerawa a jihar Anambra. Ya bayyana hakanne bayan da shugaba Tinubu ya baiwa ma'aikatun gwamnati umarnin su daina shigo da kayan da ake yin irin su a Najeriya. Saidai Atiku yace wannan duk yaudara ce wadda 'yan Najeriya sun saba ji, yace idan Gwamnatin da gaske take, ta fara daga kan kanta. Yace kamata yayi shugaba Tinubu ya fara da kanshi, ya daina amfani da motocin Alfarma da yake amfani dasu ya koma amfani da motocin Innoson ko makamantansu da ake kerawa a Najeriya. Yace ministocin Buharin ma haka ya kamata su ...
Wata Kungiyar masu ikirarin Jìhàdì ta je kusa da Abuja ta kafa sansani

Wata Kungiyar masu ikirarin Jìhàdì ta je kusa da Abuja ta kafa sansani

Duk Labarai
Kungiyar dake ikirarin jìhàdì ta Ansaru ta je kusa da babban birnin tarayya Abuja ta kafa sansani. Rahoton yace kungiyar wadda ta balle daga Bòkò Hàràm ta kuma kafa sansanoni 8 a cikin jihar Kogi. Wasu daga cikin sansanonin kungiyar na tsakanin Obajana da Kabba wanda hakan yasa manyan mutane dake wucewa ta wajan biyan kudi masu yawa dan samarwa kansu tsaro yayin wucewa ta wajan. Rahoton yace babban wajan horas da 'yan kungiyar na kilomita 93 ne tsakaninsa da babban birnin tarayya, Abuja. Kokarin jinn ta bakin hukumomin tsaro kan lamarin ya ci tura.
Ba zamu kara yadda da wani uzuri ba na rashin samar da ingantacciyar wutar Lantarki>>Ministan Wuta ya gayawa ma’aikatar wutar Lantarkin

Ba zamu kara yadda da wani uzuri ba na rashin samar da ingantacciyar wutar Lantarki>>Ministan Wuta ya gayawa ma’aikatar wutar Lantarkin

Duk Labarai
Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu ya bayyanawa ma'aikatun wutar Lantarki na kasa cewa Gwamnati ba zata sake amincewa da rashin samar da wutar lantarkin ba. Ya bayyana hakane bayan amincewa da sabon daftarin gyaran wutar. Yace kuma an samar da wani sabon tsari na baiwa ma'aikatan wutar Lantarkin horaswa ta musamman. Inda yace nan da shekaru 10 za'a magance matsalar karancin ma'aikata a hukumar wutar lantarkin.
Dattawan APC sun ce basu son Kwankwaso ya koma jam’iyyar

Dattawan APC sun ce basu son Kwankwaso ya koma jam’iyyar

Duk Labarai
Raɗe-raɗin dawowar Kwankwaso jam'iyyar APC mai mulki, na cigaba da fitowa fili. An samu rudani a sakateriyar jam’iyyar APC, a ranar Talata, bayan da Shugaban jam’iyyar na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, da Ministan Jiha na Harkokin Gidaje da Ci gaban Birane, Yusuf Ata, suka yi sabani kan daowawar Kwankwaso jam'iyyar APC. Yayin da Minista Ata ke cewa Kwankwaso – wanda kuma tsohon Ministan Tsaro ne – ya rasa karbuwa a Kano kuma siyasar sa na dab da mutuwa, Ganduje ya ce APC ba lallai ta ki karbansa ba, yana mai cewa “aboki a lokacin bukata, aboki ne na gaskiya.” Ata, yayin da yake zantawa da manema labarai bayan ganawa da Ganduje a sakateriyar jam’iyyar da ke Abuja, ya bayyana cewa matsin lambar siyasar da Kwankwaso ke ciki ne ke sa shi kokarin dawowa APC, yana mai cewa har Kw...