Saturday, December 13
Shadow
Ban ga Amfanin Zumudin Hadakatar ‘yan Adawar da El-Rufai yake yi ba, kamata yayi a bar Shugaba Tinubu ya nutsu yawa ‘yan Najeriya aiki kar a raba masa hankali>>Inji Buba Galadima

Ban ga Amfanin Zumudin Hadakatar ‘yan Adawar da El-Rufai yake yi ba, kamata yayi a bar Shugaba Tinubu ya nutsu yawa ‘yan Najeriya aiki kar a raba masa hankali>>Inji Buba Galadima

Duk Labarai
Jigo a jam'iyyar NNPP, Injiniya Buba Galadima ya bayyana cewa, yayi wuri ace an fara hadakar 'yan Adawa dan zaben shekarar 2027. Galadima ya bayyana hakane a hirar da Jaridar Punchng suka yi dashi inda yace Zumudin El-Rufai yayi yawa, yace ko da yake ba dan siyasa ban shiyasa amma yasa ba inda zashi. Yace kamata yayi a bari shugaba Tinubu ya nutsu mayar da hankali wajan yiwa 'yan Najeriya aiki. Yace shi a yanzu ba zai ce komai akan mulkin Tinubu ba sai ya cika shekara biyu cif yana mulki kamin su duba suka yayi kokari ko akasin haka.
Duk wanda yace ban yi komai ba tun bayan hawa Mulkin Najeriya Makahone kuma Kurmane>>Shugaba Tinubu

Duk wanda yace ban yi komai ba tun bayan hawa Mulkin Najeriya Makahone kuma Kurmane>>Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, duk wanda ke ikirarin bai aikata komai ba bayan hawa mulki to Makahone kuma kurma ne. Shugaban ya bayyana hakane ta bakin me magana da yawunsa, Daniel Bwala. Ya bayyana hakanne a hirar da aka yi dashi a TVC News inda yace shugaba Tinubu ya kara yawan kudaden da Najeriya ke ajiye dasu a bankin Amurka inda kuma ya biya tarin bashin da tsohuwar gwamnatin da ya gada ta bar masa. Ya kara da cewa kuma Shugaba Tinubu ya kara yawan kudaden da yake aikawa jihohi, yace kamin zuwan Tinubu jihohi 27 sun Talauce basa iya biyan Albashi. Yace amma a yau babu jihar da ta Talauce ko ta kasa biyan Albashi. Yace ba biyan Albashi ba kadai yanzu Jihohi na gudanar da ayyukan ci gaba inda yace kwanannan suka je jihar Katsina, kuma Gwamnan jihar ya ...
Shugaba Tinubu ya amince da cire Naira Biliyan N787.14 da Dala Miliyan $651.7 dan gina Tinuna a jihohi 13, Karanta kaga ko akwai jiharka

Shugaba Tinubu ya amince da cire Naira Biliyan N787.14 da Dala Miliyan $651.7 dan gina Tinuna a jihohi 13, Karanta kaga ko akwai jiharka

Duk Labarai
Majalisar Zartaswa a zamanta na ranar Litinin ta amince da fitar da kudade da ayyukan gina tituna a sassa daban-daban na Najeriya. Bayan kammala zaman, Ministan Ayyuka, Dave Umahi ya bayyanawa manema labarai cewa, akwai sabbin ayyukan titi da wanda ake sabuntawa a jihohi 13. Yace wasu daga cikin titunan da za'a yi sun hada da na garuruwan Akure-Eta-Ogbese-Iju-Ekiti zuwa garuruwan Ikere-Ado-Ekiti wanda suke tsakanin jihohin Ondo da Ekiti. Yace akwa kuma Tagwayen titunan da za'a gina a hanyar Sokoto-Zamfara-Katsina-Kaduna. Sannan kuma akwai titin Maiduguri-Monguno a jihar Borno. Sauran Titunan da za'a gina sune na Aba-Ikot-Ekpene, da titin Ebute-Ero. Akwa kuma Tituna Gombe-Yola. Sannan Akwai Titin Benin-Shagamu-Ore. Akwai kuma titin Enugu-Onitsha. Sannan Akwai ti...
Yan fàshì sun hàrbè mafarauta da fararen hula kimanin 19 har làhìrà a Karamar Hukumar Alƙaleri ta Jihar Bauchi

Yan fàshì sun hàrbè mafarauta da fararen hula kimanin 19 har làhìrà a Karamar Hukumar Alƙaleri ta Jihar Bauchi

Duk Labarai
A yayin ziyarar da ya kai wurin, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Bauchi, Sani-Omolori Aliyu, ya ba da umarnin yin cikakken bincike da kuma tura karin jami’an tsaro yankin. Mazauna kauyen Mansur sun ce an kashe ’yan farauta guda tara da kuma fararen hula guda goma, kuma an yi jana’izar ’yan bangar a kauyen Mansur kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. Amma ’yan sanada da jami’an Ƙaramar Hukumar Alƙaleri ba su ce komai ba kan adadin mamatan ba. Kakakin ’yan sanda na jihar, CSP Ahmed Mohammed Wakil, ya ce kwamishinan ya tattauna da masu ruwa da tsaki a yankin, inda ya buƙaci jama’a su kwantar da hankalinsu, su kuma kasance a cikin shiri, tare da bai wa ’yan sanda goyon baya wajen gudanar da binciken su.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nuna Alhininsa da mika ta’aziyya ga iyalan wanda suka ràsù a hadarin mota a Danbatta

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nuna Alhininsa da mika ta’aziyya ga iyalan wanda suka ràsù a hadarin mota a Danbatta

Duk Labarai
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya bayyana alhininsa tare da ta'aziyya ga al'ummar ƙaramar hukumar Dambatta bisa rasuwar mutum biyar yan yankin sakamakon haɗarin mota ranar Lahadi. Hadarin dai ya faru kilometer bakwai kafin shiga garin Dambatta lokacin da mutanen ke dawowa daga jihar Bauchi bayan sun raka amarya. Daga cikin waɗanda suka rasu akwai yayan Alhaji Surajo guda biyu da kuma yayan kaninsa Alhaji Salisu Dan Raino guda uku. Sanarwar daraktan yaɗa labaran gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ta rawaito Abba Kabir Yusuf na bayyana rashin a matsayin na al'ummar Kano gaba ɗaya tare addu'ar Allah ya ji ƙan su ya bai wa iyalansu hakuri.
An Hango ‘yan bìndìgà 300 a kan babura dauke da muggan makamai suna tafiya daga Zamfara zuwa jihar Naija

An Hango ‘yan bìndìgà 300 a kan babura dauke da muggan makamai suna tafiya daga Zamfara zuwa jihar Naija

Duk Labarai
Akalla mutane 300 da ake zargin ‘yan bindiga ne, dauke da muggan makamai Akan babura, an hango su suna ketare hanyar Kontagora zuwa Minna, tsakanin Kampanin Bobby da Wamba a Karamar Hukumar Mariga ta Jihar Neja. Lamarin ya faru ne da rana tsaka, inda hakan ya sa direbobi da fasinjoji suka tsere domin kare rayukansu. Wani ganau ya bayyana cewa, an yi imanin cewa ‘yan bindigar sun fito ne daga Jihar Zamfara, kuma suna tafiya cikin 'yanci zuwa Karamar Hukumar Mashegu ba tare da gamuwa da jami’an tsaro ba. Wani direba da ya shaida lamarin ya ce babu ko da jami’in tsaro guda daya a lokacin da lamarin ke faruwa. Shugaban Karamar Hukumar Mariga, Abbas Kasuwa Garba, ya tabbatar da faruwar lamarin yayin da aka tuntube shi. Ya bayyana cewa an tura hadin gwiwar jami’an tsaro zuwa yankin d...
Duk Wanda Ya Yi Silar Haduwata Da Adam A. Zango, Na Yi Alkawarin Zan Ba Shi Tukwicin Naira Dubu Dari Biyar, Inji Matashi Sharhabilu Musa Malumfashi

Duk Wanda Ya Yi Silar Haduwata Da Adam A. Zango, Na Yi Alkawarin Zan Ba Shi Tukwicin Naira Dubu Dari Biyar, Inji Matashi Sharhabilu Musa Malumfashi

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Duk Wanda Ya Yi Silar Haduwata Da Adam A. Zango, Na Yi Alkawarin Zan Ba Shi Tukwicin Naira Dubu Dari Biyar, Inji Matashi Sharhabilu Musa Malumfashi
Shugaban APC, Ganduje yayi magana bayan cece-kuce yayi yawa kan Bidiyon da aka ga dansanda na gyara masa takalmi

Shugaban APC, Ganduje yayi magana bayan cece-kuce yayi yawa kan Bidiyon da aka ga dansanda na gyara masa takalmi

Duk Labarai
A jiyane Bidiyo ya bayyana inda aka ga Shugaban jam'iyyar APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje a tsaye, dansandansa ya duka yana daure masa takalmi. Bidiyon ya watsu sosai a kafafen sada zumunta inda akaita bayyana mabanbanta ra'ayoyi akai. Da yake mayar da martani kan lamarin ta bakin kakakinsa, Aminu Dahiru Ahmad, Ganduje yace wasu ne dake son jawo cece-kuce da kawo rudani a tsakanin al'umma suka fitar da Bidiyon. Yace Ganduje an sanshi mutum ne me haba-haba da mutane sannan kuma yana da kyakkyawar alaka tsakaninsa da masu masa aiki shiyasa aka ga abinda dansandan yayi.
Idan Namiji ya miki Ba daidai ba kina son yin maganinshi, kawai ki kalamai sharrin cewa ya miki Fyàdè>>Inji Wannan matar

Idan Namiji ya miki Ba daidai ba kina son yin maganinshi, kawai ki kalamai sharrin cewa ya miki Fyàdè>>Inji Wannan matar

Duk Labarai
Wata mata ta dauki hankula bayan da ta bayyana cewa hanya mafi sauki ta yin maganin maza itace kala musu sharrin fyade. Ta bayyana hakane ta shafinta na sada zumunta inda abin ya baiwa mutane mamaki. A kwanannan ne dai Sanata Natasha Akpoti ta zargi kakakin majalisar Dattijai Godswill Akpabio da nemanta da lalata.