Saturday, December 13
Shadow
Goodluck Jonathan, da Bukola Saraki sun yiwa Tsohon Shugaban kasa, Marigayi Umar Musa ‘Yaradua addu’a

Goodluck Jonathan, da Bukola Saraki sun yiwa Tsohon Shugaban kasa, Marigayi Umar Musa ‘Yaradua addu’a

Duk Labarai
A yayin da tsohon shugaban kasa, Marigayi, Umar Musa 'Yaradua ya cika shekaru 15 da rasuwa, Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya masa addu'a. Yace 'yaradua ya sashi ya kara fahimtar aikin gwamnati da kyau. Yace bai cika yawan magana ba, kuma idan yayi magana babu siyasa a ciki zaka ji ta me ma'ana ce. Yace bashi da girman kai, yana da kankan da kai. Inda a karshe yayi mai fatan Allah ya ci gaba da sakashi ciki mutane na gari a Aljannah Firdausi. Shima Bukola Saraki a nasa sakon cewa yayi, Muna girmama tsohon shugaban mu da bashi da girman kai ga hangen nesa . Yace manyan abubuwan da ake tuna tsohon shugaban kasar dasu sune, hadin Kan Najeriya, Sulhu da 'yan Naija Delta, zaman lafiya da gyaran Zabe. Yayi fatan Allah ya ci gaba da yi masa Rahama.
Tsohon Gwamnan jihar Sokoto, Dr. Dalhatu Bafarawa ya koka da rashin kishin kasa na ‘yan siyasa

Tsohon Gwamnan jihar Sokoto, Dr. Dalhatu Bafarawa ya koka da rashin kishin kasa na ‘yan siyasa

Duk Labarai
Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Dr. Dalhatu Bafarawa yace 'yan siyasar yanzu basu da kishin kasa wanda yace hakan barazanane ga ci gaban Najeriya. Yace yanda ake shirin mayar da mulkin Najeriya babu 'yan adawa abin damuwa ne musamman yanda 'yan adawar ke komawa jam'iyya me mulki saboda abinda zasu samu ba dan kishin masa ba. Yace hakan baranane ga Dimokradiyyar Najeriya. Yace idan aka bar abubuwa suka ci gaba da lalace wa hakan ba karamar illanzai wa Najeriya da al'ummarta ba. Ya bayyana hakane a ganawar da aka yi dashi a kafar BBCHausa.
EFCC ta kama matashi bayan da yayi Bidiyo yana wulakanta Naira a Kaduna

EFCC ta kama matashi bayan da yayi Bidiyo yana wulakanta Naira a Kaduna

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Hukumar yaki da rashawa da ci hanci EFCC ta kama matashin da yayi Bidiyo yana wulakanta Naira yana talata inda kuma ya nemi ida EFCC din sun isa su kamashi. Matashin me amnfani da sunan @youngcee0066 a Tiktok tuni ya shiga hannu. Hukumar tace ta kama matashin me suna Muhamad Kabir Sa'a a unguwar Tudun Wada dake Kaduna. Tace nan gaba zata gurfanar dashi a gaban kotu dan a yanke masa hukunci.
JIYA BA YAU BA: Farashin Kaya A Lokacin Mulkin Marigayi ‘Yar’Adua

JIYA BA YAU BA: Farashin Kaya A Lokacin Mulkin Marigayi ‘Yar’Adua

Duk Labarai
JIYA BA YAU BA: Farashin Kaya A Lokacin Mulkin Marigayi 'Yar'Adua Litar Fetur = Naira 65Gas = Naira 112Shinkafa = Naira 3,500Siminti = Naira 750Taki = Naira 2500Buhun Siga= Naira 7,000.Buhun Fulawa = Naira 6,050 Da sauran farashin kaya, duk babu tsada a lokacin sa, kuma ya dauko hanyoyin gyara kasa, Allah Ya dauki ransa. A yau ne dai marigayi tsohon shugaban kasan ke cika shekaru 15 da rasuwa. Gaskiya Nijeria mun yi rashin Adalin Shugaban Kasa, Ya Allah Ka haskaka kabarin Umar Musa Yar'Adua, Ka sa shi a aljannar Firdausi, Don Alfarmar Sayyidina Rasulillah. Daga Rashida Bala Suleja
Hukumar raba arziƙin ƙasa ta nemi sake duba ƴancin kashe kuɗin ƙananan hukumomi a Najeriya

Hukumar raba arziƙin ƙasa ta nemi sake duba ƴancin kashe kuɗin ƙananan hukumomi a Najeriya

Duk Labarai
Hukumar rarraba arziƙin ƙasa (RMAFC) ta bukaci gwamnatin tarayya da ta sake duba ƴancin kashe kuɗin ƙananan hukumomi 774 da yadda ake aiwatar da sabuwar dokar man fetur (PIA). Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ɗauke da sa hannun shugaban hukumar, Dr. Muhammed Shehu, da Sakatarenta, Injiniya Joseph Okechukwu Nwazeb. hukumar ta fitar da sanarwar ne bayan taron horarwar kwana uku da aka gudanar a Uyo, Jihar Akwa Ibom inda taron ya mayar da hankali kan inganta tsarin kuɗi da rarraba albarkatu a Najeriya. Sanarwar ta ce "Ya zama dole a riƙa biyan kuɗaɗen kananan hukumomi kai tsaye daga asusun tarayya ba tare da tsoma bakin gwamnatocin jihohi ba." Haka kuma, hukumar ta buƙaci a sauya Sashe na 162(2) na kundin tsarin mulki domin sanya lokaci na musamman da s...
DA DUMIDUMINSA: An Gwangwaje Mawaki Rarara Da Matarsa Aisha Humaira Da Kyautar Motoci Biyu A Katsina

DA DUMIDUMINSA: An Gwangwaje Mawaki Rarara Da Matarsa Aisha Humaira Da Kyautar Motoci Biyu A Katsina

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} DA DUMIDUMINSA: An Gwangwaje Mawaki Rarara Da Matarsa Aisha Humaira Da Kyautar Motoci Biyu A Katsina Daga Comr Nura Siniya Uwar marayun kasar Kaita Dr. Amina Musa Kaita ta baiwa Mawakin siyasa Dauda Adamu Rarara da kyautar babbar mota Coaster mai ɗaukar mutum 35, yayin da yake wake Ɗan nata Dr. Haruna Maiwada a wajen taron walimar taya murnar nadinsa a Katsina Kazalika Dr. Amina ta gwangwaje amaryarsa Aisha Humaira da mota ƙirar RAV 4 New model domin tasha amarci. A cewar D...
Gwamnonin Zamfara da Benue sun ƙalubalanci gayyatar kwamitin majalisar wakilai

Gwamnonin Zamfara da Benue sun ƙalubalanci gayyatar kwamitin majalisar wakilai

Duk Labarai
Gwamnonin jihohin Zamfara da Benue, Dauda Lawal da Hyacinth Alia, sun ƙi amincewa da gayyatar da Kwamitin Karɓar Ƙorafe-ƙorafe na Majalisar Wakilai ta Tarayya ya aike musu, inda suka bayyana shakku kan halaccin gayyatar. An gayyaci gwamnonin da majalisun dokokin jihohinsu ne domin su bayyana a gaban kwamitin bisa zargin karya ƙundin tsarin mulki da kuma gazawa wajen gudanar da mulki. Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban sashen yaɗa labarai na kwamitin, Chooks Oko, ya fitar Sanarwar ta bayyana cewa an tsara zaman sauraron bayanansu ne a ranar 8 ga watan Maris, inda ake sa ran za su bayar da ƙarin haske kan wasu muhimman al’amura. Daga cikin matsalolin da ake son jin bayani a kansu har da dakatar da wasu 'yan majalisar jiha da kuma taɓarɓarewar tsaro a jihohin biy...
Manyan Malaman Cocin Katolika 2 da ake tsammanin zasu gaji Fafaroma Francis an samesu da zargin yin rufa-rufa game da cin zàràfìn yara ta hanyar yin làlàtà dasu

Manyan Malaman Cocin Katolika 2 da ake tsammanin zasu gaji Fafaroma Francis an samesu da zargin yin rufa-rufa game da cin zàràfìn yara ta hanyar yin làlàtà dasu

Duk Labarai
Manyan Malaman cocin Katolika 2 da ake tsammanin na daga cikin wanda zasu gaji Fafaroma Francis ana zarginsu da yin rufa-rufa game da binciken cin zarafin kananan yara. Malam sune Cardinal Pietro Parolin dan kasar Italiya, sai Cardinal Luis Antonio dan kasar Philippines. Wata kungiya dake saka ido kan irin wannan lamari ta kasar Amurka, The American watchdog Bishop Accountability ce ta bayyana hakan inda tace duka malaman biyu ana zarginsu da yin rufa-rufa wajan binciken malaman cocin da aka kama da lalata da kananan yara. Daya daga cikin shuwagabannin wannan kungiya me suna Anne Barrett Doyle ta bayyana cewa, an kaiwa Cardinal Pietro Parolin korafe-korafen cin zarafin yara ta hanyar lalata dasu da suka faru a kasashen Duniya daban-daban amma sai yayi rufa-rufa yaki bin diddigin ...
BA RABO DA GWANI BA: Yau Shekara 15 Da Rasuwar Tsohon Shugaban Ƙasa Ummaru Musa Yar’adua

BA RABO DA GWANI BA: Yau Shekara 15 Da Rasuwar Tsohon Shugaban Ƙasa Ummaru Musa Yar’adua

Duk Labarai
Daga Comr Nura Siniya Shugaba ƙasa na farko mafi kwazo a mulkin farar hula da akayi a tarihin Najeriya mai tausayi mai ƙishin talaka mai tsantsini da dukiyar talaka da son ganin al'umma taci gaba. Abinda ya ƙara bani sha'awa da marigayi Yar'adua shi ne lokacin da yake neman a zabe shi bai fito yayi ma ƴan Nijeriya alƙawuran ƙarya ba wanda yasan bazai iya cikawa ba. sai dai ya fito da tsarin 7-point Agenda ta yadda ya ƙudurci sauya fasalin Najeriya don ganin talaka ya samu sauƙin rayuwa da bunƙasa tattalin arziƙin ƙasa 'Yar'adua ya zo da manufofi masu kyawan gaske inda ya fara inganta albashin ma'aikatan gwamnati da albashin jami'an tsaro da ƙara inganta alawus na matasa masu ɓautar ƙasa NYSC da suka kammala karatun jami'a tare da kawo ƙarshen rikicin tsagerun yankin Naija Delta ta...
Ku shirya karin kudin wutar Lantarki dan ba zamu iya ci gaba da biyan Tallafin wutar labtarkin ba saboda ba kudi>>Gwamnatin Tarayya

Ku shirya karin kudin wutar Lantarki dan ba zamu iya ci gaba da biyan Tallafin wutar labtarkin ba saboda ba kudi>>Gwamnatin Tarayya

Duk Labarai
Ministan wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, ya bayyana cewa, yanayin tattalin arziki yasa gwamnati ba zata iya ci gaba da biyawa 'yan Najeriya tallafin wutar Lantarki ba. Yace dan haka 'yan Najeriyar su shirya fara biyan ainahin kudin wutar lantarkin da suke sha ba tare da tallafin gwamnati ba. Yace akwai 'yan Najeriya masu rauni da zasu ci gaba da samun tallafin gwamnati amma maganar gaskiya ba zasu iya ci gaba da biyan tallafin wutar ba nan gaba. Yace a yanzu haka kamfanonin wutar lantarkin na bin Gwanatin bashin Naira Tiriliyan 4. Ya bayyana hakane yayin ganawa da kamfanonin wutar lantarkin kan biyan bashin sa suke bin gwamnati.