Majalisar Dattawan Najeriya ta kafa kwamiti mai mambobi 18 domin sanya idanu kan yadda gwamnan riƙo na jihar Ribas Vice Admiral Ibok Ete Ibas mai ritaya ke tafi da aikinsa.
Majalisar ta ce ta ɗauki matakin ne a wani yuƙuri na ƙarfafa shugabanci na gari ba tare da rufa-rufa ba a jihar da ke kudu maso kudancin Najeriya.
Shugaban Majalsiar Dattawa Godswill Akpabio ya sanar yayin zaman majalisar na yau Talata cewa kafa kwamitin na da matuƙar mahimmancin wajen sa ido kan abubuwan da ke faruwa a jihar.
Shugaban masu rinjaye Opeyemi Bamidele ne shugaban kwamatin, mambobin kuma sun haɗa da Adamu Aliero, da Osita Izunaso, da Osita Ngwu, da Kaka Shehu, da Aminu Abass, da Tokunbo Abiru, Adeniyi Adebire.
A watan Maris ne Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a Ribas sakamakon a...
Danmajalisar da wakiltar mazaɓar Ɓagwai da Shanono a Majalsar Wakilan Najeriya ya nemi ƙarin jami'an tsaro sakamakon abin da ya kira hare-haren 'yanfashin daji a yankin.
Yusuf Badau ya yi kiran ne yayin wani ƙudiri da ya gabatar a gaban zauren majalisar yau Talata, inda ya lissafa lokutan da aka kai musu wasu hare-haren.
"Yan bindigar sun fara kai hari ne wata kasuwa da ke garin Farin Ruwa a ƙaramar hukumar Shanono ranar 17 ga watan Afrilu, inda suka kashe mutum biyu, da raunata mutum shida kuma suka sace mutum ɗaya," in ji shi.
"Sun sake kai irin wannan hari a garin Shanono ranar 26 ga watan Afrilun, sai dai mutanen garin sun tari ƴanbindigar kuma suka kore su.
"A ranar 2 ga watan Mayu a garin Fafarawa da Sandamu na Shanono da Bagwai, sun yi garkuwa da mutum daya da sace wayoy...
Jadawalin kasashen Duniya da mutanensu suka fi farun ciki guda 40 kenan wanda kafar kungiyar World Happiness Report suka wallafa, saidai babu Najeriya a ciki.
World's happiest countries.
Finland
Denmark
Iceland
Sweden
Netherlands
Costa Rica
Norway
Israel
Luxembourg
Mexico
Australia
New Zealand
Switzerland
Belgium
Ireland
Lithuania
Austria
Canada
Slovenia
Czechia
UAE
Germany
United Kingdom
United States
Belize
Poland
Taiwan
Uruguay
Kosovo
Kuwait
Serbia
Saudi Arabia
France
Singapore
Romania
Brazil
El Salvador
Spain
Estonia
Italy
(World Happiness Report)
Da yiyuwar Tinubu ba zai iya tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027 ba idan Amurka ta saki bayanai kan safarar miyagun kwayoyi da tace yayi.
Ana zargin dai Shugaban kasa Tinubu da wasu mutane 3 a shekarun 90s sun yi safarar kwayoyi a birnin Chicago na Jihar Illinois ta kasar Amurka.
An yi shari'a dan yanke musu hukunci amma ba'a san inda aka kwana ba
Lauyoyi da ma sauran masu fafutuka na ta neman hukumar FBI da DEA su saki bayanai kan lamarin amma sai jan kafa suke inda lamarin ya dauki shekaru.
Wasu dai na zargin akwai wata kullalliya a kasa game da kin fitar da bayanan.
TSADAR RAYUWA: Road Safety Sun Koma Daukan Fasinja A Abuja.
Yadda Tsadar Rayuwa an Abuja ta sa Aka Mayar da Motocin Kiyaye Haddura ta 'Road Safety' Suka koma na daukar Fasinja suna biyan su Kudade zuwa Unguwanninsu a Abuja.
A Daren Jiya ne dai Wakilin Jaridar Rariya Online Ya Hangi Motar Ana Mata Lodi a Tashar AYA dake Birnin Tarayya Abuja
Ba da yawuna aka kafa allon da ke nuna 'Katsina babu ƙorafi' ba a Katsina ~ Dikko Raɗɗa.
Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa yace a matsayinsa na gwamna, bai da masaniya dangane da kafa wani allo da ke nuna cewa Al'ummar Jihar ba su da ƙorafi bisa ga salon Mulkin shugaba Tinubu ba.
Hasalima Gwamnan yace, sun gabatar ma shugaba Tinubu ƙwararan ƙorafe-ƙorafe har guda 3 da ke buƙatar a magance masu, wanda suka haɗa da Matsalar tsaro, kammala wuta mai amfani da hasken Rana, da kuma fadada filin sauka da tashin jirage na Umar Musa Yar'adua da ke Katsina.
Bayan haka ya ja hankalin masu suka da su riƙa tantance labarin da suka gani a kafafen sada zumunta domin tabbatar da asalin labarin, kafin sukar wanda baya da masaniya a kai.
Daga Lukman Aliyu
Tashin Hankali: Wata Amarya ta yiwa Ango yankan rago a Kano kwana 9 da aurensu.
Rahotannin da ke shigo wa Jaridar Arewa yanzu haka sun tabbatar da cewa ana zargin wata amarya da yiwa Angonta yankan rago a daren jiya Litinin, a jihar Kano.
Lamarin ya faru a unguwar Farawa da ke cikin birnin Kano. Bayanai sun tabbatar da cewa Amaryar ta fara shayar da shi guba ne a Lemu, daga bisani ta yi masa yankan rago kamar yadda ta Dala FM ta ruwaito.
Hakazalika wani rahoton ya ce an yi masu auren zumunci ne a ranar 27 ga watan Afrilu, wanda yau kimanin kwana 9 kenan.
Zuwa yanzu jami'an tsaron yan sanda sun samu nasarar kama Amaryar domin bincike.
Jaridar Arewa
Kungiyar ƙananan likitoci a Najeriya reshen Abuja babban birnin ƙasar ta sanar da fara yajin aikin gargadi na kwanaki uku daga yau Talata, bayan korar ma’aikatan lafiya 127 da hukumar kula da ma’aikatan birnin na FCT ta yi.
An yanke shawarar shiga yajin aikin ne bayan wani taron gaggawa da kungiyar likitocin ta gudanar a asibitin Asokoro ranar Litinin, kamar yadda kafar talabijin ta Channels TV ta ruwaito.
Shugaban ƙungiyar likitocin, Dr. George Ebong, ya bayyana korar a matsayin maras tushe da kuma "rashin imani", yana mai buƙatar gaggauta dawo da ma’aikatan bakin aiki tare da biyansu albashin watan Afrilu.
Dr. Ebong ya kuma buƙaci shugaban hukumar kula da ma’aikatan Abuja, Emeka Ezeh, da ya yi murabus daga mukaminsa.
Ya yi gargaɗin cewa idan Ministan Abuja Nyesom Wi...