Tuesday, December 16
Shadow
Ali Nuhu yayi Tsokaci kan wannan hoton na Ango da Amarya, Rarara da A’isha Humaira

Ali Nuhu yayi Tsokaci kan wannan hoton na Ango da Amarya, Rarara da A’isha Humaira

Duk Labarai
A jiyane bayan Aure, Dauda Kahutu Rarara ya saki sabbin hotuna tare da Amaryarsa, A'ishatulhumaira. Hotunan sun kayatar sosai ta inda mutane suka yaba musu musamman ma ganin cewa, Sai bayan aure ne Rarara da Amaryarsa suka saki hotunan, abinda ba kasafai aka cika gani ba. Ali Nuhu ma ba'a barshi a baya ba, ya saka hoton inda yace yana kara taya ma'auratan murna.
Muguntar da El-Rufai yayi a baya ce take binsa saboda Alhaki kwikwiyo ne, Kuma ba zai yi nasara ba, saboda mutane da yawa basu yadda dashi ba saboda mayaudari ne kuma maciyin amanane>>Buba Galadima

Injiniya Buba Galadima ya bayyana cewa, Tsohon gwamnan Kaduna, Malan Nasiru Ahmad El-Rufai ba zai yi nasara ba a kokarin da yake na hada kan 'yan jam'iyyar Adawa da kuma kalubalantar Gwamnatin Tinubu a zaben shekarar 2027. Buba Galadima ya bayyana hakane a wata hira da jaridar Punchng ta yi dashi wadda shafin hutudole ya bibiya. Yace El-Rufai ya saba ya shiga jam'iyya wadda me karfi ce tana kan hanyar Nasara shima ya samu Nasara. Yace amma yanzu da yake kokarin farowa daga farko a yanzu ne zai gane wahalar da ake sha wajan gina jam'iyya da siyasa. Yace amma matsalar El-Rufai itace bashi da alaka me kyau da mutane, ya taka mutane da yawa kuma mayaudari ne maci yin amanane dan haka babu wanda ya yadda dashi kuma dalili kenan da yasa ba zai yi nasara ba. Yace El-Rufai yayi maga...
Za’a samu gagarumin faduwar farashin man fetur a Najeriya

Za’a samu gagarumin faduwar farashin man fetur a Najeriya

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa ana tsammanin gagarumin faduwar farashin Man fetur da gas a Najeriya. Hakan ya biyo bayan faduwar farashi danyen man fetur a kasuwar Duniya. 'Yan kasuwar man fetur na Najeriya sun tabbatarwa da kafar Punchng hakan saidai sun ce ba za'a ga faduwar farashin da sauri ba har sai idan farashin danyen man fetur din ya ci gaba da faduwa. A ranar Litinin, Hutudole ya samu cewa, farashin Danyen Man fetur na Brent ya kai dala $59.80 akan kowace ganga
Duk da Hukumar Hisbah ta Kano tace ta je gidan yarin Goron Dutse ta ga ba gaskiya a zargin Luwadi da ake da yara, Saidai da yawa sun ce basu yadda da binciken na Hisbah ba, ciki kuwa hadda tsohon hadimin shugaban kasa, Malam Bashir Ahmad

A jiyane Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta sanar da cewa ta je gidan gyara hali dake Goron Dutse inda aka yi zargin cewa ana luwadi da matasa da ake tsare dasu dan ta yi bincike. Hukumar tace ta kammala binciken ta kuma ta gano cewa babu kanshin Gasol a zargin. Saidai duk da haka wasu sun ce basu gamsu da binciken Hisbah ba, kamata yayi a samu dan jarida wanda bashi da alaka da gwamnati watau me zaman kansa yayi wannan bincike. Wasu sun ce shin a yayin binciken da Hisbah ta yi an cire wandon yaran an ga yanayin lafiyar duburarsu, kuma an kaiwa likita ya dubasu? https://twitter.com/BashirAhmaad/status/1919121269301084633?t=8MOoE2qcVtxNLhZAh56gOQ&s=19 Cikin masu irin wannan ra'ayi hadda Malam Bashir Ahmad wanda tsohon hadimin shugaban kasa ne. https://twitter.com/Realo...
Kalli Bidiyo yanda fadawan sarkin Katsina suka fasa kofar taro suka shigar da sarkin bayan da aka kulle kofar dakin Taron da aka yiwa Tinubu Maraba a jihar

Kalli Bidiyo yanda fadawan sarkin Katsina suka fasa kofar taro suka shigar da sarkin bayan da aka kulle kofar dakin Taron da aka yiwa Tinubu Maraba a jihar

Duk Labarai
Wasu rahotanni sun ce bayan da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya shiga dakin taron da aka mai tanadi dan yi masa maraba a jihar Katsina, An kulle dakin taron. Saidai daga baya Me martaba sarkin Katsina ya isa wajen inda fadawa suka iske kofar a kulle. Saidai sun fasa gilashij kofar inda suka shigar da Sarki wajan Taron. Kalli Bidiyon: https://twitter.com/northern_blog/status/1919398029473284233?t=eIgHj3fbuZ8VxrkeyPlTSw&s=19 Da yawa dai sun jinjinawa Fadawan.
Kasar Israyla ta amince da kwace gaba dayan yankin Gaza ya koma karkashin kulawa da ikonta, dan haka ta kirawo tsaffin sojojinta dan yin wannan aiki

Kasar Israyla ta amince da kwace gaba dayan yankin Gaza ya koma karkashin kulawa da ikonta, dan haka ta kirawo tsaffin sojojinta dan yin wannan aiki

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa kasar Israela ta amince da matakin kwace gaba dayan yankin Gaza ya koma karkashin mulkinta. Dan hakane ta kirawo duka sojojinta da suka yi ritaya dana karta kwana dan gudanar da wannan gagarumin aikin. Israela dai bata bayyana zuwa yaushene zata rike zirin na gaza ba watau saidai abinda Allah yayi. Kasar ta Israela tace a wannan sabon mataki zata bari a shiga da kayan agaji cikin Gaza amma zata saka ido ta tabbatar basu fada hannun kungiyar Hamas ba.
Kadan ya hana in daina karanta Jarida da kallon labarai, Saboda Wahalar da nake ganin ‘yan Najeriya a ciki>>Shugaba Tinubu

Kadan ya hana in daina karanta Jarida da kallon labarai, Saboda Wahalar da nake ganin ‘yan Najeriya a ciki>>Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, saura kiris ya daina jin labarai da karanta jaridu saboda yanda yake ganin 'yan Najeriya a cikin wahala. Ya bayyana hakane a ziyarar da ya kai jihar Katsina. Yace amma duk da haka ya dage ya tsaya tsayin daka dan tabbatar da ganin ya dora Najeriya a turbar gaskiya. Shugaba Tinubu yace kuma zuwa yanzu an fara ganin sakamakon matakan da ya dauka. Inda yace lamura sun fara dawowa daidai