Saturday, December 13
Shadow
Bayan da majalisa ta kwace mata motarta ta aiki, Kalli Motar Alfarma da Sanata Natasha Akpoti ta siya take tuka abinta

Bayan da majalisa ta kwace mata motarta ta aiki, Kalli Motar Alfarma da Sanata Natasha Akpoti ta siya take tuka abinta

Duk Labarai
Bayan dakatar da Sanata Natasha Akpoti daga majalisar tarayya, An kuma kwace kayan aikinta wanda suka hada da motar da akw baiwa kowane dan majalisa da sauransu. Saidai duk da korafin da ta yi na a dawo mata da kayan aikinta hakan ya faskara, dan hakane ma ta koma ta sayo mota ta kece raini. Motar ta dauki hankula sosai bayan da aka ga Sanata Natasha Akpoti a ciki.
Ni Musulmi ne kuma nasa Allah a raina sanda nake aiki, Na yiwa Najeriya aiki tukuru ta yanda ko hutu bana samu, kuma a shirye nake na amsa tambayoyin EFCC, amma dai yanzu basu kamani ba ina nan ina hutawa tukuna>>Tsohon Shugaban NNPCL, Mele Kolo Kyari

Ni Musulmi ne kuma nasa Allah a raina sanda nake aiki, Na yiwa Najeriya aiki tukuru ta yanda ko hutu bana samu, kuma a shirye nake na amsa tambayoyin EFCC, amma dai yanzu basu kamani ba ina nan ina hutawa tukuna>>Tsohon Shugaban NNPCL, Mele Kolo Kyari

Duk Labarai
Tsohon shugaban kamfanin mai na kasa, NNPCL, Mele Kolo Kyari ya fito ya karyata rade-radin da ake yadawa cewa wai yana hannun hukumar EFCC inda ake bincikensa. Kyari ya fitar da sanarwa ta shafinsa na X inda yace a yanzu yana hutawa ne bayan kammala yiwa Najeriya aiki na tsawon shekaru 34. Yace a lokacin da yake aiki ko hutun sati biyu baya samu dan haka yanzu yana hutun da ya kamata ace yayi a baya. Yace 'yan uwa da abokan arziki suna ta kiranshi suna sanar dashi game da wani labari dake cewa an kamashi yana hannun EFCC. Yace wannan labari karyane, yace a sanda yake aiki ya sa Allah a ransa saboda yasan zai tsaya a gaban Allah ya amsa tambayoyi. Dan haka yace a yanzu ma a shirye yake ya amsa tambayoyin EFCC ka yanda ya gudanar da ayyukansa. Yace ya kamata a daina yada ir...
‘Yan tà’àddà sun kàshè sojojin Najeriya 4 a jihar Yobe

‘Yan tà’àddà sun kàshè sojojin Najeriya 4 a jihar Yobe

Duk Labarai
Rahotanni daga jihar Yobe na cewa mahara wanda ake tsammanin mayakan kungiyar Bòkò Hàràm ne sun kai hari sansanin sojoji na 27 dake Gujba karamar hukumar Buni Yadi ta jihar Yobe inda suka kashe sojoji 4. Hakanan maharan sun lalata motocin yakin sojojin. Hakan na zuwane kasa da awanni 24 bayan da Gwamnonin yankin Arewa maso gabas suka yi taro a Damaturu dan samar da tsaro a yankinsu. Daya daga cikin sojojin wanda ya tsira daga harin yace 'yan Bindigar sun afka musu ne da misalin karfe 2 na dare ranar Asabar. Yace mamayarsu maharan suka yi amma an yi musayar wuta inda sojoji 4 suka mutu kuma suma sun kashewa 'yan ta'addar mutane sosai. Hedikwatar tsaro ta tabbatar da harin amma bata bayar da cikakken bayani ko an samu wadanda suka mutu ba ko a'a
2027: Kuri’un Buhari miliyan 12 har yanzu na APC ne, inji Gwamna Sule

2027: Kuri’un Buhari miliyan 12 har yanzu na APC ne, inji Gwamna Sule

Duk Labarai
Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bayyana cewa tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari har yanzu yana da matukar muhimmanci ga jam’iyya mai mulki, wato APC, gabanin zaben 2027. Gwamna Sule ya ce kuri’un Buhari da yake samu guda miliyan 12, za su ba jam’iyyar mai mulki rinjaye a zaben mai zuwa. Gwamnan ya bayyana hakan ne a wani babban taron girmamawa da aka gudanar domin Sakataren Gwamnatin Jihar, Barr. Labaran Magaji, a fadar gwamnati da ke Lafia, babban birnin jihar. Sule ya soki wadanda ke ganin cewa Buhari da magoya bayansa za su bar hadin gwiwar da ta haifar da jam’iyyar APC, yana mai cewa Buhari har yanzu yana daga cikin manyan shugabannin jam’iyyar kuma yana da tasiri wajen samun nasara a zaben da ke tafe. Ya kara da cewa duka Buhari da Shugaba Bola Tinubu sun dad...
Ana rade-radin Sanata Binani ta sayi ginin da sakatariyar jam’iyyar APC take a jihar Adamawa ta basu sati daya su tashi su bata guri

Ana rade-radin Sanata Binani ta sayi ginin da sakatariyar jam’iyyar APC take a jihar Adamawa ta basu sati daya su tashi su bata guri

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Ana yada rade-radin cewa, Sanata A'ishatu Binani ta sayi ginin da Sakatariyar APC dake Adamawa inda ta baiwa jam'iyyar sati daya a tashi a bata gininta. Saidai Sanata Binani bata tabbatar ko musanta wannan rahoto ba zuwa yanzu
Kalli Bidiyo: Wata ‘yar Fulani taji sanyin AC tace Motar naku akwai akwai aljanna sanyiiiiiiii

Kalli Bidiyo: Wata ‘yar Fulani taji sanyin AC tace Motar naku akwai akwai aljanna sanyiiiiiiii

Duk Labarai
Wasu 'yan Fulani da me mota ya tsaya a gefen titi dan sayen Mangwaro daga hannunsu sun bayar da nishadi. Daa daga cikinsu tace akwai Aljanna a motar bayan da ta ji sanyin AC. https://twitter.com/Deejamarh/status/1918565033149145305?t=equ8lvutilSkk-K2rN6lSw&s=19 Da yawa dai sun ce ashe ba sharri akewa Fulani ba wani abin idan an ce sun yi.
Da Duminsa: A karshe dai EFCC ta yi nasarar cafke Tsohon shugaban kamfanin mai na kasa, NNPCL

Da Duminsa: A karshe dai EFCC ta yi nasarar cafke Tsohon shugaban kamfanin mai na kasa, NNPCL

Duk Labarai
Rahotanni da hutudole ke sami na cewa yanzu haka tsohon shugaban kamfanin mai na kasa, NNPCL, Mele Kolo Kyari ya shiga hannun EFCC. Tun ranar Juma'a ne dai EFCC ta yi nasarar cafkeshi inda aka fara masa tambayoyi shi da wasu tsaffin ma'aikatan da aka kamasu tare. Rahotannin sun ce zai kwashe karshen makonnan a hannun EFCC inda za'a ci gaba da tuhumarsa.
Ji yanda aka kama Sojoji 2 na taimakawa ‘yan tà’àddà a jihar Borno

Ji yanda aka kama Sojoji 2 na taimakawa ‘yan tà’àddà a jihar Borno

Duk Labarai
Hukumar sojojin Najeriya ta sanar da kama wasu mutane 4 dake kaiwa 'yan ta'adda kayan masarufi, biyu daga cikin wadanda aka kama din sojoji ne. Sanarwar tace an yi bincikenne a tsakanin ranar 26 ga watan Afrilu zuwa 29 ga watan kuma an yi bincikenne a kananan hukumomin Bama, Kukawa, da Madagali na jihar Borno. Kakakin sojin, Major General Markus Kangye ya tabbatar da hakan inda yace abin takaici ne irin wannan cin amana. Ya jawo hankalin kwamandojin yaki dasu saka ido dan lura da sojoji masu irin wannan hali inda ya gargadi sojojin da kai kansu ga irin wannan hanya ta halaka.
Za mu ƙwato duka dazukan Najeriya daga hannun ɓata-gari -Tinubu

Za mu ƙwato duka dazukan Najeriya daga hannun ɓata-gari -Tinubu

Duk Labarai
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya tabbatar da cewa gwamnatinsa na ƙoƙarin ƙwato duka wurare da dazukan ƙasar da ƴanbindiga ke ɓuya, ta hanyar girke sabbin dabaru na zamani domin yaƙi da ta'addaci da ƴan fashin daji. Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga jagororin jihar Katsina a lokacin liyafar cin abincin dare da aka shirya masa a gidan gwamnatin jihar ranar Juma'a. ''Dangane da matsalar tsaro, matsala ce da ta addabi ƙasarmu', kuma na yi magana da sojoji, na tabbatar musu cewa za mu yi duk mai yiwuwa don kawo ƙarshen matsalar ƴanbindiga'', in Tinubu. "Za mu samar da kayan aiki na zamani domin ƙwace duka dazukan ƙasarmu daga hannun miyagu, matsalar tsaro ta shafi duka Najeriya ne ba wani yanki ba, kuma mun sani cewa indai muna so ƙasarmu ta ci gaba to dole mu kawa...