Friday, December 5
Shadow
Kalli Bidiyon: Inda wata matar aure ke bada labarin cewa abokin aikinda a ofis da suke aikata alfasha tare yafi mijinta iya sarrafa mace

Kalli Bidiyon: Inda wata matar aure ke bada labarin cewa abokin aikinda a ofis da suke aikata alfasha tare yafi mijinta iya sarrafa mace

Duk Labarai
Wata mata dake aikata Alfasha da wani Farfesa a wajan aikinta ta bayyana cewa yafi mijinta iya romance watau sarafa jikin mace. Ta gayawa malam hakane a yayin da take neman shawara saboda tana son tuba saboda abin ya isheta. Malam da kansa ne yake bayar da labarin. Saidai yace bayan wata daya, ya sake tambayar ta ko sun sake aikaya alfashar da Farfesan? Tace masa eh sun yi sau daya. https://www.tiktok.com/@abdulyellow11/video/7572481112505683208?_t=ZS-91RhHMdPpq5&_r=1
Kai Duniya Kalli Bidiyon manyan mutane da aka kama sanye da malunmalun suna shatar waya a masallaci>>

Kai Duniya Kalli Bidiyon manyan mutane da aka kama sanye da malunmalun suna shatar waya a masallaci>>

Duk Labarai
Wannan wasu mutanene da rahotanni suka ce an kamasu a masallaci da yunkurin satar waya. Abin takaici shine gasu ba yara ba kuma su rasa inda zasu yi satar sai a Masallaci. Bidiyonsu ya yadu sosai inda ake ta Allah wadai wasu kuma na musu Addu'ar shiriya. https://twitter.com/Aboki_Nagari/status/1989768372352176248?t=YfqG03zi_xPwpdOgccwMow&s=19
APC kamar Jirgin Annabi Nuhu(AS) ne duk Wanda bai shigo ba ba zai tsira ba>>Inji Gwamnan Nasarawa

APC kamar Jirgin Annabi Nuhu(AS) ne duk Wanda bai shigo ba ba zai tsira ba>>Inji Gwamnan Nasarawa

Duk Labarai
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya bayyana cewa, jam'iyyar APC kamar Jirgin Annabi Nuhu(AS)take. Ya bayyana hakane a ranar Asabar wajan karbar wasu sabbin 'yan siyasa da suka shiga jam'iyyar ta APC. Yace Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya basu kudade masu yawa su yiwa mutane aiki shiyasa ma bai ga dalilin da zai hana a sake zaben Shugaba Tinubu a karo na biyu ba. Yace APC itace jirgin Annabi Nuhu kuma duk wanda bai shiga ba za'a barshi a baya.
Kalli Yanda aka gano wani Kirista da yayi amfani da hoton makabartar Musulmai da cewa Kiristane da aka Shyekye dan ya jawo hankalin kasar Amurka

Kalli Yanda aka gano wani Kirista da yayi amfani da hoton makabartar Musulmai da cewa Kiristane da aka Shyekye dan ya jawo hankalin kasar Amurka

Duk Labarai
Wannan hoton wata makabartar musulmai ce da wani Kirista yayi amfani da shi da nuna irin yanda a cewarsa aka kashe mutane da yawa a jihar Benue. Saidai musulmai da yawa sun ce wannan makabartar Musulmi ce. https://twitter.com/iambabangida_/status/1989723500848771543?t=rZWFLzzhU87whLXjREFbgA&s=19
Nima ban amince da kirar da akawa Wike daga PDP ba>>inji Gwamnan jihar Flato>>Caleb Mutfwang

Nima ban amince da kirar da akawa Wike daga PDP ba>>inji Gwamnan jihar Flato>>Caleb Mutfwang

Duk Labarai
Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang ya bayyana cewa, bai goyi bayan korar da akawa ministan Abuja, Nyesom Wike daga jam'iyyar PDP ba. Ya bayyana hakane a sanarwar da ya fitar ta bakin me magana da yawunsa, Gyang Bere. Hakan na zuwane bayan da PDP ta sanar da korar Wike da wasu jiga-jigan jam'iyyar daga cikin jam'iyyar. Gwamna Mutfwang ya bayyana cewa ba a tattauna wannan masala a taron gwamnonin jam'iyyar ba hakanan ba'a san da ita ba dan haka shi baya goyon bayan korar Wike.
Kasar Angola ta karrama Tsohon Shugaban kasa, Janar Murtala Ramat Muhammad saboda taimakon da ya bayar wajan ci gaban Nahiyar Afrika

Kasar Angola ta karrama Tsohon Shugaban kasa, Janar Murtala Ramat Muhammad saboda taimakon da ya bayar wajan ci gaban Nahiyar Afrika

Duk Labarai
Rahotanni daga kasar Angola na cewa kasar ta karrama tsohon shugaba Mulkin soja na Najeriya, Janar Murtala Ramat Muhammad saboda taimakon da ya bayar wajan ci gaban Nahiyar Afrika Hakanan cikin wadanda aka karamma akwai tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo da Farfesa Ibrahim Gambari. An yi bikin karramawar ne a babban birnin kasar me suna Luanda.
Kalli Bidiyo: Wani mutum ya kai Sheikh Dr. Ahmad Gumi Kotu inda yace ya rike masa matarsa tun watan Satumba ta zauna a gidan Sheikh Gumi taki komawa gidansa

Kalli Bidiyo: Wani mutum ya kai Sheikh Dr. Ahmad Gumi Kotu inda yace ya rike masa matarsa tun watan Satumba ta zauna a gidan Sheikh Gumi taki komawa gidansa

Duk Labarai
Wani mutum me suna Alhaji Nasir Musa Idris a jihar Kaduna ya kai karar Babban malamin dadi Islama, Sheikh Dr. Ahmad Gumi kotu inda yake zargin malamin da rike masa mata tun watan Satumba. Mutumin wanda yake auren balarabiya yace matar tasa ta yi yaji ta koma gidan malan Gumi da zama kuma ya hadu fa malam din yace yana son matarsa ta koma gida amma abu yaci tura. Ga cikakken bayaninsa anan: https://www.tiktok.com/@faruq_abuja/video/7572863094666415378?_t=ZS-91QoCDzJl7B&_r=1