Thursday, December 18
Shadow
Ana Zargin Abokan Dan Tsohon Shugaban Karamar Hukumar Jama’are, Isa Wabi Da Kašhè Shi A Yayin Da Suka Hauro Masa Gida Cikin Darè A Jihar Bauchi

Ana Zargin Abokan Dan Tsohon Shugaban Karamar Hukumar Jama’are, Isa Wabi Da Kašhè Shi A Yayin Da Suka Hauro Masa Gida Cikin Darè A Jihar Bauchi

Duk Labarai
Rundunar 'yansandan Najeriya reshen jihar Bauchi ta ce ta kama mutum ɗaya bisa zargin kashe tsohon shugaban ƙaramar hukumar Jama'are Isa Wabi. A cewar wata sanarwa da rundunar ta fitar a yau Juma'a, waɗanda ake zargin abokan ɗansa ne kuma sun aikata kisan ne da tsakar daren yau a gidansa da ke Fadaman Mada. Nan take aka kai shi asbitin Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa bayan rahoto ya ishe 'yansandan cewa wasu matasa sun caccaka masa wuƙa a wuya. "Binciken farko-farko ya nuna wasu mutum biyu ne suka aikata kisan waɗanda abokan ɗan Wabi ne ɗan shekara 24 mai suna Abdulgafar Isa Mohammed," a cewar sanarwar. Ta ce dakaru sun tarar da ɗaya daga cikin mutanen a sume kuma aka kai shi asibiti, inda daga baya aka tabbatar da mutuwarsa. 'Yansanda sun ce sun kama Abdulgafar domin ci gaba...
Ƙungiyar Kiristoci ta CAN Ta Nemi Haɗin Gwiwar Shiga Ayyukan Hisbah, Don Magance Baɗala

Ƙungiyar Kiristoci ta CAN Ta Nemi Haɗin Gwiwar Shiga Ayyukan Hisbah, Don Magance Baɗala

Duk Labarai
Ƙungiyar CAN Ta Nemi Haɗin Gwiwar Shiga Ayyukan Hisbah, Don Magance Baɗala Daga Mustapha Abubakar Ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN) ta nemi haɗin gwiwa da kuma samun cikakken damar shigar da membobinta cikin ayyukan hukumar Hisbah domin samun kyakkyawar dangantaka da haɗin kai a aiki. Fasto Nuhu Sani, Sakataren CAN na ƙaramar hukumar Sabon Gari a jihar Kaduna, ne ya bayyana hakan a lokacin wani taron bita na kwana ɗaya da hukumar Hisbah ta shirya a sakatariyar ƙaramar hukumar. Fasto Sani ya ce tun da hukumar Hisbah ƙungiya ce ta addini da ke da alhakin kawar da miyagun ayyuka a cikin al’umma, ya zama dole a samu haɗin gwiwa da ƙungiyar Kiristoci domin cika wannan buri. Sakataren ya lurantar da cewa Musulmai da Kiristoci suna zaune tare a wuri ɗaya, a don haka ya zama ...
An Kama wani Ɗan Nijar a Dajin Yankari sanye da kayan sojoji.

An Kama wani Ɗan Nijar a Dajin Yankari sanye da kayan sojoji.

Duk Labarai
An Kama wani Ɗan Nijar a Dajin Yankari sanye da kayan sojoji. Rundunar ‘yan sandan Bauchi ta kama wani mutum mai suna Jibrin Ali, ɗan shekara 28 daga Zandar, Jamhuriyar Nijar, a cikin dajin Yankari da ke ƙaramar hukumar Alkaleri. An kama shi ne yayin sintiri na hadin gwiwa, yana sanye da kayan sojoji, kuma ana zargin yana ciki waɗanda suke tada hankali a yankin wanda ya ke fama da ayyukan ‘yan bindiga, ya kasa bayar da sahihin bayani kan dalilin kasancewarsa a dajin.Kwamishinan ‘yan sanda ya bada umarnin a gudanar da cikakken bincike.
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya alƙawarta samar wa sojojin ƙasar kayan aiki domin fatattakar ayyukan ƴanbindiga a arewacin ƙasar.

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya alƙawarta samar wa sojojin ƙasar kayan aiki domin fatattakar ayyukan ƴanbindiga a arewacin ƙasar.

Duk Labarai
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya alƙawarta samar wa s5ojojin ƙasar kayan aiki domin fatattakar ayyukan ƴanbindiga a arewacin ƙasar. Yayin da yake jawabi ga sojojin ƙasar ranar Juma'a a wata ziyara da ya kai jihar Katsina - ɗaya daga cikin jihohin da ke fama da ayyukan ƴan fashin daji, shugaban ƙasar ya ce matsalar ƴanta'adda da masu garkuwa da mutane da ƴan fashin daji ta jima a ƙasar. "Ƴan Najeriya sun zuba muku ido, suna jiran ku kawo ƙarshen matsalar tsaro tare da ƙwato kowane yanki na ƙasarmu, ku nuna wa maƙiyan Najeriya cewa ƙaryarsu ta ƙare'', in ji Shugaba Tinubu. ''Gwamnati na ɗaukar matakan samar muku isassun kayan aiki, da suka haɗ da sabbin fasahohin zamani da sabbin hanyoyin tattara bayanan sirri da dabarun yaƙi, ba wai don kare ƙasarmu kaɗai ba, sai don samun ƙar...
Facebook da Instagram na barazanar daina aiki a Najeriya saboda Harajin da Gwamnatin Tinubu ke saka mai yayi yawa

Facebook da Instagram na barazanar daina aiki a Najeriya saboda Harajin da Gwamnatin Tinubu ke saka mai yayi yawa

Duk Labarai
Kamfanin Meta iyayen Facebook da Instagram na barazanar ficewa daga Najeriya saboda yawan dokokin da gwamnatin tarayya ke gindaya musu. Hakanan dayan dalilin da yasa kamfanin ke son ficewa daga Najeriya hadda harajin da ake kaka ba musu wanda suka ce yayi yawa. Gwamnatin Najeriya ta maka kamfanin META a kotu akan zarge-zarge daban-daban inda take neman kamfanin ya biyata diyyar Dala Miliyan $290m, META sun shiga kotu amma basu yi nasara ba. Kamfanin na Meta dai shine kuma ke da manhajar WhatsApp amma bai bayyanata cikin wanda zai kulle ba. Kotun dai ta baiwa kamfanin nan da zuwa watan Yuni ya biya harajin da aka kakaba masa.
Bidiyo Kalli Miliyan 10 da kayan Abinci, Shinkafa, Kaza, da Talotalo, lemu da za’a kai a matsayin kudin fansa dan kubutar da wani da aka yi Gàrkùwà dashi

Bidiyo Kalli Miliyan 10 da kayan Abinci, Shinkafa, Kaza, da Talotalo, lemu da za’a kai a matsayin kudin fansa dan kubutar da wani da aka yi Gàrkùwà dashi

Duk Labarai
Bidiyon yanda aka tara Miliyan 10 a matsayin kudin fansa za'a kaiwa 'yan Bindiga ya dauki hankulan mutane sosai a kafafen sada zumunta. Rahoton Bidiyon yace an tara kudinne ta hanyar neman taimako. Sannan 'yan Bindigar sun nemi a kuma kai musu Lemu da kaza da sauran kayan abinci wanda suma sun kai Naira Miliyan 1. https://twitter.com/ChuksEricE/status/1918310544060170580?t=Gi4pQc0qWeFOsOA26eFvzg&s=19 Mutane dai sun yi ta Allah wadai kan lamarin.