Saturday, December 13
Shadow
Kar a saka min kayan kyale-kyale ko Alatu a kabarina>>Wasiyyar Fafaroma

Kar a saka min kayan kyale-kyale ko Alatu a kabarina>>Wasiyyar Fafaroma

Duk Labarai
Marigayi shugaban cocin katolika da ya mutu, watau Fafaroma Francis ya bar wasiyyar cewa, kada a saka masa kayan Alatu a kabarinsa. Tun a shekarar 2022 ne ya rubuta wannan wasiyyar inda yace kuma yana so a binneshine a Rome wanda rabon da a binne Fafaroma a wannan waje tun shekarar 1669. Fararoma Francis ya mutu yana da shekaru 88 inda ya sha yabo saboda soyayyar da yake nunawa Talakawa, 'yan Luwadi, 'yan Gudun Hijira, Falasdinawa da sauransu.
Da Duminsa: Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya dawo Najeriya bayan kwashe kwanaki 19 a Turai yana hutawa

Da Duminsa: Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya dawo Najeriya bayan kwashe kwanaki 19 a Turai yana hutawa

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya dawo Najeriya a yau, Litinin bayan kwashe kwanaki 19 a Turai yana hutawa. Dama dazu da rana fadar shugaban kasar tace yau zai dawo Najeriya. Da farko dai an bayyana cewa sati biyu shugaban kasar zai yi amma daga baya sai gasho ya wuce hakan, wanda lamarin ya fara saka 'yan Najeriya cikin damuwa.
Ji yanda aka yi daurin auren dan ministan kudi ba tare da kowa ya sani ba saboda yace bai son Almubazzaranci musamman saboda halin da ‘yan Najeriya ke ciki

Ji yanda aka yi daurin auren dan ministan kudi ba tare da kowa ya sani ba saboda yace bai son Almubazzaranci musamman saboda halin da ‘yan Najeriya ke ciki

Duk Labarai
An daura auren dan ministan Kudi Wale Edun, me suna Mr. Tobi Edun a asirce ba tare da kowa ya sani ba. Daurin auren ya samu halartar manyan mutane ma'aikatan gwamnati na 'yan kasuwa amma ba'a yi Sharholiya ba. Ministan kudin ne ya bukaci kada a yi almubazzaranci wajan bikin dan nasa. Inda ake tsammanin ya dauki wannan mataki ne musamman saboda halin matsin da mafi yawan 'yan Najeriya ke ciki, kamar yadda wata majiya a kusa dashi ta gayawa jaridar Vanguard.
Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana abinda za’a yi dan girmama Fafaroma da ya mùtù

Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana abinda za’a yi dan girmama Fafaroma da ya mùtù

Duk Labarai
Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya mika sakon ta'aziyyarsa ga kiristoci kan mutuwar fafaroma. Ya bayyana cewa fafaroma mutum ne da ya nuna tausai ga talakawa da 'yan Cirani da sauransu. Ya bayyana cewa, sakon karshe na Fafaroma shine kiran da yayi a kawo karshen yakin Gaza. Dan hakane ma Buhari a sakon da ya fitar ta hannun kakakinsa, Malam Garba Shehu yayi kira ga kasar Israela da kungiyar Hamas da su kawo karshen yakin a matsayin girmamawa ga Fafaroman.
Kalli Yanda Gunkin Virgin Mary(Watau Mahaifiyar Annabi Isa(AS)) ya fashe da kuda a coci saboda mutuwar Fafaroma

Kalli Yanda Gunkin Virgin Mary(Watau Mahaifiyar Annabi Isa(AS)) ya fashe da kuda a coci saboda mutuwar Fafaroma

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, kwanaki kadan kamin mutuwar shugaban cocin katolika, Fafaroma Francis, Gunkin Virgin Mary( watau Mahaifiyar annabi Isa(AS)) ya zubar da hawaye. Gunkin yayi hawayenne ranar Juma'a, 18 ga watan Afrilun daya gabata. Da yawa dai sun alakanta hakan da mutuwar Fafaroma. Wasu kuma sun ce hakan wata mu'ujizace ta musamman.
Ni ke da Kafacity iya Kafacity dan kuwa sau biyu ina zama Gwamnan Kano, Kai kuwa babu abinda ka taba tsinanawa a siyasa>>Ganduje ya gayawa Buba Galadima

Ni ke da Kafacity iya Kafacity dan kuwa sau biyu ina zama Gwamnan Kano, Kai kuwa babu abinda ka taba tsinanawa a siyasa>>Ganduje ya gayawa Buba Galadima

Duk Labarai
Shugaban jam'iyyar APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya mayarwa da Jigo a jam'iyyar NNPP, Injiniya Buba Galadima martani kan sukar da ya masa. Injiya Buba Galadima ya bayyana Ganduje a matsayin wanda bashi da wani muhimmanci a siyasance. Saidai a martanin Ganduje yace shi kuwa ke da muhimmanci dan sau biyu a jere ya zama Gwamnan Kano. Sannan yace ayyukan da ya gudanar suna nan har yanzu ana ganinsu. Yace kuma APC a karkashinsa sai kara ci gaba take amma jam'iyyar su buba Galadima NNPP sai ci baya take banda rikicin cikin gida babu abinda suke fama dashi. Yace sannan shi kanshi Buba Galadima a siyasance babu wani abu da zai nuna na ci gaba da ya samu dan ko dawwamammen jam'iyya baya da ita.
An dakatar da wasannin gasar Serie A ta Italiya sanadiyyar rasuwar fafaroma

An dakatar da wasannin gasar Serie A ta Italiya sanadiyyar rasuwar fafaroma

Duk Labarai
An dakatar da wasanni guda huɗu na gasar Serie A ta ƙasari Italiya bisa rasuwar Fafaroma Francis. A ranar Litinin fadar Vatican ta sanar da rasuwar fafaroman wanda ya shafe shekara 88 a duniya bayan wata jinya da ya yi har aka kwantar da shi a asibiti. Karawar da aka soke ta haɗa da:Torino v Udinese, Cagliari v Fiorentina, Genoa v Lazio and Parma v Juventus. Hukumar da ke lura da gasar ta Serie A a ƙasar ta ce za ta duba wani lokacin da za a buga wasannin a nan gaba. Ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa da dama sun miƙa ta'aziyyar su bisa rasuwar shugaban cocin katolikan na duniya.
Motar kaya ta hàlalàkà masu bikin Easter biyar a jihar Gombe

Motar kaya ta hàlalàkà masu bikin Easter biyar a jihar Gombe

Duk Labarai
Wani hatsarin mota ya yi sanadiyar mutuwar aƙalla mutum biyar yayin da wasu takwas suka ji raunuka a ƙaramar hukumar Billiri ta jihar Gombe. Lamarin ya faru ne a lokacin da birkin wata mota ɗauke da kayan abinci ya shanye, inda ta kutsa cikin dandazon jama’a da ke gudanar da bukukuwan Easter na mabiya addinin Kirista. Wata da ke halartar bukukuwan kuma ta shaida lamarin ta faɗa wa BBC cewa ɓacin rai ya sa mutane suka ƙona motar nan take. "Ana rawa ana waƙa ana biki, kawai sai mutane muka gani a ƙarƙashin mota, ana cewa ya tsaya ya tsaya amma bai tsaya ba," in ji ta. "An ƙona komai da komai na motar, har sai da jami'an tsaro suka zo suka kori mutane." Rundunar 'yansanda a jihar ta ce cikin waɗanda suka jikkata har da wasu Musulmai da ke sallah a gefen titi. Ismaila Uba Mis...
Charles Oka da ake tsare dashi saboda tayar da bàm ranar ‘yancin Najeriya a gidan yarin Maiduguri ya mùtù

Charles Oka da ake tsare dashi saboda tayar da bàm ranar ‘yancin Najeriya a gidan yarin Maiduguri ya mùtù

Duk Labarai
Rahotanni daga gidan yarin Maiduguri na cewa, Charles Oka da ake tsare dashi a gidan yarin saboda tayar da bam a ranar 'yancin Najeriya ya mutu. Rahoto a daren jiya daga Sahara reporters yace an jefa bam a dakin da Charles Okah ke tsare wanda hakan yasa hayaki ya tashi a dakin wuta ta tashi ta kama gidan sauron da yake ciki da kuma katifar da yake kwanciya akai. A sabon rahoton da aka samu yau yace Charles Okah ya jikkata sanadiyyar wannan lamari. Saidai daga baya an samu rahotanni dake cewa yana mutu amma ba'a hukumance ba. Charles Okah dai ya rubuta budaddiyar wasika zuwa ga Ministan harkokin cikin gida inda yake zargin aikata rashawa da cin hanci a gidan yarin. Tun daga nanne dai aka sakashi a gaba. Hukumar gidan yarin Najeriya tace babu wani bam da ya tashi a gidan ya...