Monday, December 15
Shadow
Shuwagabannin tsaron Najeriya na shan suka bayan kìsàn mutane 250 a cikin makonni 2, ana zargin sun gaza

Shuwagabannin tsaron Najeriya na shan suka bayan kìsàn mutane 250 a cikin makonni 2, ana zargin sun gaza

Duk Labarai
Masu sharhi akan al'amuran tsaro na sukar shuwagabannin hukumomin tsaro na Najeriya saboda yawaitar kashe-kashen da ake yi musamman a jihohin Arewa. Ana ganin matsalar tsaron ta sha kan su ko kuma basa daukar matakan da ya kamata dan magance matsalar. Hakan na zuwanw yayin daka yi kashe-kashe a jihohin Filato, Borno, Katsina, da Benue. Hakanan ga kuma wata sabuwar kungiyar masu ikirarin jihadi me suna Mamuda data bayyana a jihar Kwara dake arewa maso tsakiyar Najeriya. Manyan shuwagabannin hukumomin tsaro a Najeriya sune Gen. Christopher Musa; Chief of Army Staff, Lt-Gen. Olufemi Oluyede; Chief of Air Staff, Air Marshal Hassan Abubakar, Chief of Naval Staff, Vice Admiral Emmanuel Ogalla. Sannan akwai babban me baiwa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro, Malam Nuhu Ribadu ...
Ji ainahin abinda ya faru tsakanin Minista Tugga da Mataimakin gwamnan jihar Bauchi(wanda aka ce ya zabgawa Ministan Mari) wanda sai da Mataimakin shugaban kasa ya shiga tsakani

Ji ainahin abinda ya faru tsakanin Minista Tugga da Mataimakin gwamnan jihar Bauchi(wanda aka ce ya zabgawa Ministan Mari) wanda sai da Mataimakin shugaban kasa ya shiga tsakani

Duk Labarai
Rahoton Marin da mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Auwal Jatau yawa Ministan Harkokin kasashen Waje, Yusuf Tuggar na daya daga cikin wadanda suka dauki hankula a yau. Saidai daga baya Mataimakin gwamnan ta bakin me magana da yawunsa, Muslim Lawal ya musanta hakan. Amma a wata majiya da muka samo da kafar Sahara Reporters tace tabbas an yi musayar yawu tsakanin Mataimakin gwamnan da Ministan a cikin motar bas data daukesu zuwa fadar Me martaba Sarkin Bauchi. Rahoton yace ana tsaka da tafiyane sai aka ga fastar Ministan sai gwamna yace zasu yi maganinsa saboda rashin kunyar da yakewa shuwagabannin jam'iyyar jihar. Saidai Tuggar ya mayar da martanin cewa jihar Bauchi ba kayan kowa bace, hakan yasa mataimakin gwamnan yayi kokarin kaiwa gareshi amma sai jami'an tsaron mataimakin shug...
Duk da dakatar dashi da yayi, Gwamna Fubara na jihar Rivers ya gayawa al’ummar jihar su ci gaba da goyon bayan shugaba Tinubu

Duk da dakatar dashi da yayi, Gwamna Fubara na jihar Rivers ya gayawa al’ummar jihar su ci gaba da goyon bayan shugaba Tinubu

Duk Labarai
Dakataccen gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya gayawa al'ummar jiharsa da su ci gaba da goyon bayan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. Fubara ya bayyana hakane a sakon Easter da ya fitar inda yace wannan lokaci ne na hadin kai da yin sulhu. Yace Mutanen jihar su ci gaba da fatan Allah ya kawo ci gaba da warwarewar Al'amura a jihar.
JAMB ta saka sabuwar ranar fara jarrabawar wannan shekara

JAMB ta saka sabuwar ranar fara jarrabawar wannan shekara

Duk Labarai
Hukumar Shirya Jarrabawa Shiga Manyan Makarantu ta Najeriya, JAMB, ta saka ranar Alhamis 24 ga watan Afrilu a matsayin ranar fara jarrabawar wannan shekarar maimakon ranar 25 ga wata da ta fara sakawa. Cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Dr Fabian Benjamin ya fitar ranar Asabar, ya ce an yi hakan ne domin tabbatar da kumar ta ce muhimman matakan da ta ɗauka da kuma dauran hukumomin da za su taimaka mata wajen gudanar da aikin. Dr Fabian Benjamin ya ce a yanzu haka waɗanda za su rubuta jarrabawar za su iya fitar da katin shiga jarrabawar - wadda ke ɗauke da muhimman bayanai dangane da jarrabawar. Ya ƙara da cewa akwai bayanin wuri da lokacin mutum zai zana jarrabawar da sauran muhimman bayanai game da yadda tsarin zaman ɗakin jarrabawar zai kasance duka a jikin katin. Dubban ...
Shettima ga ƴan Kwankwasiyya da Gandujiyya: Ku hakura da rikicin siyasar nan haka domin cigaban Kano

Shettima ga ƴan Kwankwasiyya da Gandujiyya: Ku hakura da rikicin siyasar nan haka domin cigaban Kano

Duk Labarai
Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya roki yan siyasar Jihar Kano da su tuna irin zumuncin da ke tsakaninsu kada su bari banbancin ra'ayin siyasa ya raba kansu. Kashim Shettima yayi wannan roko ne a gaban gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf da Shugaban jam'iyar APC na jihar Kano Alhaji Abdullahi Abbas da sauran jiga jigan yan siyasa daga bangaren Kwankwasiyya da Gandujiyya a lokacin da yake ta'aziyar rasuwar Galadiman Kano marigayi Abbas Sunusi. Kashim Shettima ya ce kuskure ne shiyasa a jiha kamar kano da ake takama da ita a kowanne mataki ta raba kan mutanan Kano ko kawo cikas a a tsakaninsu. "Jihar Kano itace abar koyi a duk Najeriya,dan haka bama murna idan munga ana samun sabanin ra'ayin siyasa kuma ana nuna juna yatsa. Kano itace cibiyar Arewa ,duk abinda ya sha...
Da Duminsa: Ji Abinda mataimakin Gwamnan Bauchi yace bayan da “ya zabgawa Minista mari”

Da Duminsa: Ji Abinda mataimakin Gwamnan Bauchi yace bayan da “ya zabgawa Minista mari”

Duk Labarai
Mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Auwal Muhammad Jatau ya yi magana akan rahoton dake cewa ya zabgawa ministan harkokin kasashen waje, Yusuf Maitama Tuggar mari. Jatau yayi magana ta bakin kakakinsa, Muslim Lawal inda yace rahoton marin ba gaskiya bane Yace su basu ma da labari game da maganar marin a bakin 'yan jarida suke ji. Yace babu ta yadda za'a yi mataimakin gwamnan jihar Bauchi ya mari minista, yace ko gwamna ba zai mari minista ba ballantana mataimakinsa. Kokarin jin ta bakin ministan ya ci tura.
Kalli yanda matashi ya Kàshè kansa bayan kama Budurwarsa na cin amanarsa

Kalli yanda matashi ya Kàshè kansa bayan kama Budurwarsa na cin amanarsa

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Wani matashi dalibin jami'a a kasar Ghana ya kàshè kansa ta hanyar rataya bayan kama budurwarsa na cin amanarsa. Lamarin ya farune a jami'ar University of Education, Winneba dake kasar ta Ghana ranar Laraba, 16 ga watan Afrilu. Saidai ba'a bayyana sunan dalibin ba. Rahotanni sun bayyana cewa, dalibin ya yanke jiki ya fadi bayan kama budurwar tasa inda kuma daga bisani ya shiga daki ya rataye kansa. 'Yansandan garin Winneba sun dauke gawar matashin inda suka tafi da ita suka...